Takarar Kano ta Tsakiya: Rufa’i Hanga ya maye gurbin Shekarau a NNPP
Bayan ficewar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyar NNPP, Malam Ibrahim Shekarau, jam’iyar ta maye guirbinsa da Sanata Rufa’i Sani Hanga
Bayan ficewar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyar NNPP, Malam Ibrahim Shekarau, jam’iyar ta maye guirbinsa da Sanata Rufa’i Sani Hanga.
Shekarau dai ya bar jam’iyar ta NNPP ne zuwa PDP, a kwanakin baya, wanda hakan ya tilasta wa jam’iyar neman wanda zai yi mata zawarcin kujerar a zaben 2023.
- Ana zargin shugaban makaranta da yin lalata da dalibansa 7 a Kwara
- Boko Haram ta kashe rabin malaman makarantun Arewa maso Gabas —NEDC
An dai tabbatar da takarar Sani Hangan ne a filin taro na Sani Abacha Youth Center da ke Kano ranar Alhamis, karkashin jagorancin shugaban jam’iyar na mazabar ta Kano ta Tsakiya, Abdullahi Zubair, kuma daruruwan magoya bayan jam’iyar daga kanana hukumomi 15 na mazabar sun halarta.
Tun bayan ficewar Shekarau daga NNPP din magoya bayanta ke ta bayyana ra’ayoyinsu kan wadanda suke ganin sun fi cancanta da zawarcin kujerar daga ciki da wajen jam’iyar.