Takarar shugaban kasa sai dan Kudu –Gwamnonin APC na Arewa

Gwamnonin APC a Arewa sun ce in don Allah ake yi a bar wa ‘yan Kudu takara

Takarar shugaban kasa sai dan Kudu –Gwamnonin APC na Arewa

Gwamnonin APC bayan taron da suka yi

Gwamnonin APC a Arewa da kuma daya daga cikin jagororin siyasa na yankin sun bukaci a bar wa Kudu takarar shugabancin kasa a jam’iyyar a zaben badi.

Gwamnonin sun bukaci hakan ne a wata sanarwa da suka fitar bayan wata ganawa da suka yi ranar Asabar da nufin sake nazari a kan halin da jam’iyyar ke ciki.

“Bayan mun yi tattaunawa ta tsanaki, muna so mu bayyana amannarmu cewa bayan shekara takwas na mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, kamata ya yi daya daga cikin mambobinmu na jihohin kudancin kasar nan ya zama dan takarar shugaban kasa na APC a zabukan 2023.

“Wannan girmanmu ne kuma wajibinmu ne wanda ba shi da wata alaka da shawarar wata jam’iyyar siyasa.

“Muna tabbatar da cewa dabbaka wannan kuduri ne abin da ya fi dacewa don karfafa kasar nan da hada kanta da kuma ciyar da ita gaba”, inji sanarwar mai dauke da sa-hannun gwamnonin Arewa 10 da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Tun bayan da PDP ta zabi tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi mata takara ne dai  jam’iyyar ta APC ta shiga rudani.

Rikita-rikita

Wasu daga cikin mabobin jam’iyyar na ganin tun da galibin kuri’u a Arewa suke to dan Arewa ne kadai zai iya kayar da Atiku.

A daya bangaren kuma, wasu na ganin babu wanda zai iya ja da dan takarar na PDP ta kowanne bangare sai Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wanda ya fito daga yankin Kudu maso Yamma.

Shugabannin siyasar na APC sun ce sun dauki wannan matsaya ne bayan da suka amsa kiran Shugaba Buhari ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar su bayar da gudunmawa wajen fitar da dan takara mai tasiri.

Ko da yake ba su fito karara sun bayyana sunan wanda suke mara wa baya ba, gwamnonin jam’iyyar na arewacin Najeriya sun goyi bayan mulki ya koma Kudu bayan saukar Shugaba Buhari.

‘Kowa ya janye’

Don haka ne gwamnonin suka yi kira ga ’yan Arewa masu sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasa a jam’iyyar su janye su bar ’yan Kudu su fafata a zaben fid-da-gwanin da za a yi ranar Litinin.

“Don haka, da babbar murya, muke bayar da shawara ga Shugaba Muhammadu Buhari cewa neman wanda zai yi takara a APC don zama magajinsa ya takaita ga ’yan uwanmu da suka fito daga Kudu.

“Muna kuma kira ga dukkan masu neman takara daga Arewa su nuna kishin kasa su janye, su kyale ’yan Kudu kadai a fagen fid-da-gwani”, inji sanarwar.

Gwamnonin da suka sa hannu a sanarwar sun hada da Aminu Bello Masari na Katsina, da Abubakar Sani Bello na Neja, da Abdullahi Sule na Nasarawa, da Babagana Umara Zulum na Borno.

Gwamnonin APC a Arewa

Sauran su ne Muhammad Inuwa Yahaya na Gombe, da Nasir Ahmed El-Rufai na Kaduna, da Bello Matawalle na Zamfara.

Sai kuma Simon Bako Lalong na Filato, da Abdullahi Umar Ganduje na Kano, da Abubakar Atiku Bagudu.

Shugabannin siyasar sun kuma ce alhaki ne da ya rataya a wuyan APC ta tabbatar cewa zabukan 2023 sun samar da wata kafa ta gina kasa da jaddada cewa akwai dama ga kowa ta darewa mulki ta hanyar dimokuradiyya.

“A wannan lokaci ana bukatar nutsuwa da hada hannu domin fitar da dan takarar jam’iyyarmu.

“Muna kuma kira ga dukkan shugabannin APC su sauke wannan nauyi da ya rataya a wuyansu”, inji sanarwar.

Har yanzu dai babu wata alama dake nuna cewa rikita-rikitar da ta dabaibaye jam’iyyar ta APC na daf da zuwa karshe, sa’o’i kadan kafin gudanar da Babban Taron Kasa don fitar da wanda zai tsaya takarar Shugaban Kasa.

Abin jira a gani dai shi ne ko wannan kira da wadannan jagorori na APC a Arewa suka yi zai yi tasiri.