Takardar makaranta: Buhari ya kunyata magabta

Ga dukkan alamu an kawo karshen cece-kucen da aka rika yi game da takardar kammala makarantar sakandare na dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammdu Buhari, bayan da Kwalejin Gwamnati (tsohuwar Makarantar Sakandaren Lardi) ta Katsina ta sako sakamakon jarrabawar kammala makaranta ta Janar din. Jaridar Premium Times, ta ce sakamakon jarrabawar […]

Takardar makaranta: Buhari ya kunyata magabta
Takardar makaranta: Buhari ya kunyata magabta

Ga dukkan alamu an kawo karshen cece-kucen da aka rika yi game da takardar kammala makarantar sakandare na dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammdu Buhari, bayan da Kwalejin Gwamnati (tsohuwar Makarantar Sakandaren Lardi) ta Katsina ta sako sakamakon jarrabawar kammala makaranta ta Janar din.

Jaridar Premium Times, ta ce sakamakon jarrabawar ya tabbatar da da’awar da Janar Buhari ya yi cewa ya dauki jarrabawar takardar shaidar kammala makaranta ta kasashen Afirka ta Yamma (WASC) da Jami’ar Cambridge take shiryawa inda ya samu yabo a darussa biyar da suka hada da Ingilishi da Labarin kasa da Hausa da Tarihi da Kimiyyar Lafiya a makarantar a 1961.
Jaridar ta ce, ta samu kwafen sakamakon na na’urar kwamfuta daga Jami’ar Cambridge da kuma sakamakon da kuma bayanin sakamakon dauke da sanya hannun shugaban Kwalejin Katsina na yanzu mai kwanan wata 21 ga Janirun bana.
Sakamakon jarrabawar ya nuna Buhari ya fadi a darasin Lissafi da Kafinta, kuma ya ci jarrabawar Adabin Ingilishi.
Lambar cibiyar jarrabawar ita ce 8280, yayin da lambar Buhari ta kasance 002. Kuma bayanai sun ce an buga sakamakon jarrabawar a takardar Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Katsina, kuma ta nuna an yi jarrabawar ce a 1961.
Takardar da ta fito daga Cambridge ta kuma nuna sakamakon sauran dalibai 17 a cibiyar ciki har da Shehu ’Yar’aduwa, tsohon Hafsan Hafsoshin Majalisar koli ta Najeriya.
Wakilinmu wanda ya ziyarci kwalejin da ke kofar Sauri a Katsina ya ce wani jami’in kwalejin da ya nemi a saka sunansa ya nuna masa fayil din Janar Buhari da ke dauke da dukkan bayanan da suka shafi zamansa a kwalejin.
Ya ce Buhari ya samu takardar shaidar WASC a 1961 tare da sakamako kamar haka: Turanci-5 da Hausa -5 da Adabin Ingilishi -7 da Tarihi-3 da Labarin kasa (Jogurafi)- 6 da Lissafi-9 da Kimiyyar Lafiya -6 da Kafinta -9.
Ya ce Farfesa Haruna Kaita ne ya rubuta wa makarantar yana bukatar sakamakon jarrabawar a madadin Buhari kuma an mika masa. Sai dai ya ki ba wakilinmu kwafen, inda ya ce sai an samu bukatar haka a ga hukumar makarantar a rubuce.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi Farfesa Kaita ya tabbatar da hakan, inda ya ce tuni ya mika wa hukumomin da suka kamata da kuma kafafen watsa labarai don nuna wa duniya.
Idan za a iya tunawa an samu cece-kuce kan takardar kammala sakandare ta Janar Buhari ne bayan da rundunar sojan Najeriya, ta lashe aman da ta yi cewa takardar suna hannunta, inda daga baya ta ce ba ta da takardar a hannunta.
Kakakin Sojan Najeriya Manjo Janar Olajide Laleye ya fadi wa taron manema labarai cewa ba su da takardar ainihi ko kwafenta na sakamakon kammala makaranta ta Janar Buhari. Ya ce wata hukumar daukar sojoji kan bukaci ganin takardun ainihi na duk mai son shiga soja, amma babu wani bayani da zai nuna ko an bi haka a wajejen 1960.
Bayanin na hukumomin soja y azo ne bayan da Janar Buhari ya ce takardun suna tare da hukumomin soja, kuma matakin da sojojin suka dauka ya tilasta Buhari kiran taron manema labarai a shekaranjiya Laraba, inda ya ce: “Na dauka daukacin takarduna suna tare da rundunar sojan Najeriya. Amma abin mamaki, yanzu an gaya mana duka cewa akwai bayanan sakamakon jarrabawar, amma babu kwafensu a cikin fayil dina. Don haka na rubuta wa tsohuwar makaranta ta wato Sakandaren Lardi ta Katsina da ake kira Kwalejin Gwamnati yanzu ta sake ba ni kwafen sakamakon jarrabawar da take da shi. Kuma za a ba ’yan jarida nan da wani wani lokaci.”
Kafin fito da takardar makarantar Janar Buhari, Jam’iyyar PDP dai ta yi barazana ga Janar Buhari kan ya fito da takardar makarantarsa ko kuma ya mika kansa ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da shi don a bincike shi tare da hukunta shi.
Daraktar Labarai na Kwamitin Yakin Zaben Shugaba Jonathan Femi Fani-Kayode ya fadi wa taron manema labarai haka a Abuja, inda ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta duba yiwuwar kwace mukamin Janar din tunda “bai cancanci” shiga soja ba.
Fani-Kayode ya ce a ce Buhari ya ce “Duk da cewa akwai bayanin sakamakon jarrabawar, amma babu kwafen takardar jarrabawar a fayil dinsa ba wani abu ba ne face ‘yin jabun takarda’ kuma wani ‘babban laifi ne’ a karkashin doka.”