Takardun bogi: Atiku ya nemi Kotun Koli ta yi watsi da bukatar Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci Kotun Koli ta yi watsi da bukatar Shugaba Tinubu na kin karbar sabbin hujjojin Atikun kan zargin Tinubun da amfani da takardun bogi.
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci Kotun Koli ta yi watsi da bukatar Shugaba Tinubu na kin karbar sabbin hujjojin Atikun kan zargin Tinubun da amfani da takardun bogi.
Atiku ya gabatar da sabbin hujjoji ga Kotun Kolin kan zargin amfani da takardun bogi da yake cewa Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu da Tinubun ya lashe.
- Yadda mazauna iyakar Najeriya da Nijar suka shiga ha’ula’i bayan rufe boda
- Ni ban ce zan rushe babban masallacin Abuja ba —Wike
Ya ce amfani da takardun bogin da Tinubu ya yi domin rike matsayi mafi girma a Najeriya na da matukar hatsari bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya kamata a taka masa burki.
A kan haka ne ya nemi Kotun Kolin da ta yi watsi da bukatar Tinubu na kin karbar sabbin hujjojin bisa hujjar sarkakinar da za su haifar a shari’ar.
Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun (SAN) ya shaida wa kotun cewa maganar takardun shaidar karatu batu ne da ya danganci abubuwan kafin zabe, don kotun ba ta da hurumin karbar sabbin hujjoji a kansu.