Takardun Pandora: Peter Obi ya musanta sammacin EFCC

Obi ya musanta sammacin, amma ya ce inda aka gayyace shi zai amsa kira.

Takardun Pandora: Peter Obi ya musanta sammacin EFCC

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya musanta rahoton da ake yadawa cewae EFCC ta gayyace shi.

Obi ya ce har yanzu bai samu sammaci daga EFCC ko wata hukumar yaki da rashawa ba.

Sai dai ya bayyana cewa kamar yadda kowa ya gani a intanet cewar hukumar na neman shi, shi ma haka ya gani.

Obi, cikin wata sanarwa da hadimarsa kan kafafen watsa labarai, Valentine Obienyem, ta fitar ta musanta labarin da ke yawo a intanet.

Ta ce, “Obi har yanzu bai samu shaidar takardar sammaci daga EFCC ba, kamar yadda ya karanta a intanet.

“Daga abin da ake yadawa shi ne an tura takardar sammacin zuwa ofishin da ya bari ne, kuma yanzu ba ya ofishin kuma babu wata takarda da aka turo masa.”

Kazalika, sanarwar ta bayyana Obi a matsayin dan kasa na gari mai bin doka, kuma zai martaba duk wata gayyata da za a yi masa daga kowace hukuma.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno