Takardun Tinubu: Babu ruwan Kwankwaso da karar da Atiku ya shigar —NNPP
NNPP ta ce Atiku ya yi ta kansa, babu abin da ya hada Kwankwaso da karar da ya shigar kan nasarar Tinubu a zaben 2023
Jam’iyyar NNPP ta yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar martani da cewa ya daina neman janyo dan takararta Sanata Rabiu Kwankwaso cikin shari’arsa ta kalubalantar zaben nasara Shugaba Tinubu a zabe.
A ranar Alhamis Atiku ya yi taron ’yan jarida inda ya bukaci dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, da kuma Kwankwaso wanda shi ne dan takarar NNPP, su hada kai da shi, wajen fallasa abin da ya kira asirin Tinubu.
- Kotu ta dawo wa dan majalisar NNPP kujerarsa a Kano
- Gwamnatin Tinubu za ta binciki yadda Buhari ya tafiyar da shirin N-Power
Amma a martanin NNPP a wani taron ’yan jarida a Abuja, Sakaraten jam’iyyar na kasa kuma mukaddashin mataimakin shugaban jam’iyyar, Prince Nwaeze Onu, ya bayyana cewa NNPP ba ta je kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu, don haka ba za ta yi shisshigi ba.
Don haka Atiku da PDP su san inda dare su yi ta kansu, su bar neman janyo NNPP cikin abin da bai shafe ta ba.
A cewarsa, NNPP ta yanke shawarar rashin kalubalantar nasarar Tinubu sabo da kaunar da take wa Najeriya.