Take hakkin kananan yara na karuwa a duniya — MDD

Nijar da Haiti sun yi kaurin suna wajen musguna wa kananan yara a bana.

Take hakkin kananan yara na karuwa a duniya — MDD

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres

Wani rahoton shekara-shekara na Majalisar Dikin Duniya ya bayyana cewa, an samu karuwar take hakkin kananan yara a wasu kasashen duniya a bana.

A ranar Laraba ne aka yi wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya takaitaccen bayani game da sakamakon rahoton musamman bangaren da ke nuna yadda take hakkin yara ya tsananta a bana.

Rahotan ya bayyana cewa, a bana kadai, an ci zarafin kananan yara da aka tabbatar har sau dubu 27, adadin da shi ne mafi girma da Majalisar Dinkin Duniya ta tattara a tarihi.

Kazalika akwai kuma wani adadi na dubu 26 da ke nuna yadda kananan yara suka shiga mawuyacin hali na bukatar daukin gaggawa.

Yanzu haka Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce, ta shiga damuwa saboda wadannan alkaluma masu tayar da hankali.

A rahoton na bana, an samu kasashen Haiti da Nijar da sunayensu suka fito cikin jerin kasashen da suka yi kaurin-suna wajen musguna wa kananan yaran, yayin da a bara, kasashen Habasha da Mozambique da Ukraine suka shiga cikin rahoton.

Rahoton na shekara-shekara na mayar da hankali ne kan yadda aka ci zarafin kananan yara tsakanin watan Janairu zuwa Disamba na kowacce shekara.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan