Takkadama: Shin jini amaryar Onni ta taka ko akasin haka?

A   makon jiya ne Babban Basaraken Lardin Yarbawa, Ooni na Ife ya yi sabuwar Amarya, lamarin da ya dauki hankalin al’ummar yankin, duba da girman daular mulkin wannan basarake kuma attajirin dan kasuwa. Wani abu da ya fi ja hankalin dinbin jama’a game da wannan biki na Ooni na Ife da sabuwar Amaryarsa, Olori Ogba […]

Takkadama: Shin jini amaryar Onni ta taka ko akasin haka?

Ooni na Ife tare da sabuwar amaryarsa

A   makon jiya ne Babban Basaraken Lardin Yarbawa, Ooni na Ife ya yi sabuwar Amarya, lamarin da ya dauki hankalin al’ummar yankin, duba da girman daular mulkin wannan basarake kuma attajirin dan kasuwa.

Wani abu da ya fi ja hankalin dinbin jama’a game da wannan biki na Ooni na Ife da sabuwar Amaryarsa, Olori Ogba Magret Ogunwusi shi ne yadda wani hoto da aka dauka wanda yake nuni da yadda amaryar ta taka wani jan abu mai kama da jini kafin ta shiga gidan sarautar, lamarin da ya janyo cece-kuce, inda wasu ke cewa jini ta taka wasu kuma na cewa ba jini ba ne, wani garin itaciya ne mai suna Oosu wanda ja ne jajur aka zuba ruwa a cikinsa ta bi ta kai ta wuce.

Aminiya ta yi tattaki zuwa garin Ile-ife a Jihar Osun domin bin diddigin wannan lamari, inda ta yi katarin zantawa da wani jami’in gidan tarihi na gwamnatin tarayya dake Ile-ife wanda ke daura da gidan sarautar Ooni na ife, mai suna Sanusi Mahmuda Madagali wanda masani ne na al’adun yarbawa kana haifaffan garin Ile-ife ne ya.

Masanin ya warware wa Aminiya zare da abawa akan wannan lamari, inda ya ce tabbas al’ummar yarbawa al’umma ce da suke da dinbin tarihi da al’adu kuma suna baiwa wadannan al’adu nasu fifiko da gaskiya. Ya ce tun da fari a sha’anin neman aure a al’adun yarbawa abu ne da ke kama da biko, inda Ango da abokansa kanje gidan amarya su yi nema suna yin durkuso suna kwanciya a kasa duk da sunan girmamawa ga iyalin amarya, “to haka ne yasa idan auren sarki ne shi ba ya zuwa neman auren sai dai ya tura wakilai a danginsa su je su nema masa domin shi sarki baya yi wa wani durkuso ko ya kwanta a kasa da sunan neman a ba shi mace.

“Don haka ka gani iyalin sarkin ne suka halarci bikin a can jihar Ondo domin amayar ‘yar asalin jihar Ondo ce, anan aka yi bikin wanda dangin Onnin suka halarta, to a bisa al’ada ta wannan gida kamar yadda binciken da na gudanar ya tabbatar min, domin na ji daga bakin wasu masana tarihin wannan gida na sarautar Ooni na Ife wadanda wasunsu bayi ne na wannan gida wanda suke gudanar da mafi yawan lamurran wannan gida sune irin masu aske kai suna biye da sarkin a duk inda yake. Sun tabbatar min cewa a da can a zamanin da idan sarki ya yi sabuwar amarya jinin mutum ne ake zubdawa a zubar a kofar gidan sarauta sai amaryar ta bi ta kai ta wuce, hakan wata al’ada ce da suka yi imani da ita, cewa wannan zai wanke ta daga wani sharri kuma idan ma an yi mata wani mugun shiri to anan shirin zai lalace sai ta shiga gidan sarautar salun alun.”

Ya kara da cewa, “amma a yanzu da zamani ya sauya ba jinin mutum ake amfani da shi ba, ya ce jinin dabba ne da aka yanka ake amfani da shi. An tabbatar min cewa raguna biyu aka yanka, jininsu ne aka zuba a kofar gidan shi ne sabuwar amaryar ta bi ta kai ta wuce, daman a al’adance yadda ake yi shi ne idan ta bi ta kai ta wuce, bayan ta shiga gidan sai dangin mijin wato Ooni su tare ta da ruwa a hannun su sai su wanke mata kafar ta, wannan yana nufin ta shiga gidan tsaf abinta, an wanke mata duk wani gilli da take tafe da shi kenan, wannan dadaddar al’ada ce,” Inji shi.

Sabuwar Amaryar ta Ooni Oba Ogunwusi mai shekara 25, babbar jami’ar majami’a ce da ta kware ta kuma yi fice ta fuskar yin da’awa a majami’ar da take aiki. Hasalima tarihi ya nuna cewa ta yanke karatun da take yi a Jami’ar Jihar Ondo domin ba da himma ga ayyukanta na majami’a tun tana da shekara 18, hakan ya sa ta kai ga cin ma babban matsayi a majami’ar.