Takunkumin Amurka ba zai ba mu tsoro ba – Iran
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya tabbatar wa al’ummar kasarsa cewa takunkumin da Shugaban Amurka Donald Trump ke ta kurarin zai kakaba wa kasar ba zai ba su tsoro ba, domin za su iya rike kansu. Shugaba Hassan Rouhani ya yi wannan jawabin ne a daidai lokacin da masu zanga-zanga suka taru a Majalisar Dokokin kasar, […]

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya tabbatar wa al’ummar kasarsa cewa takunkumin da Shugaban Amurka Donald Trump ke ta kurarin zai kakaba wa kasar ba zai ba su tsoro ba, domin za su iya rike kansu.
Shugaba Hassan Rouhani ya yi wannan jawabin ne a daidai lokacin da masu zanga-zanga suka taru a Majalisar Dokokin kasar, inda suke bayyana koke-kokensu a kan yadda darajar kudin kasar ke tabarbarewa.
An samu bayanan cewa zanga-zangar ta fadada zuwa wasu birane, inda aka samu labarin an yi gumurzu a tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zangar.
Da yake kare tsare-tsarensa na tattalin arziki, Shugaba Hassan Rouhani ya ce kudin shigar da gwamnatin ke samu bai ragu ba a ’yan watanni da suka gabata, kawai dai yadda darajar Riyal ta fadi a kasuwar canji ne ya sanya ake ta farfaganda a kafofin watsa labarai.
“Ina tabbatar muku da cewa komai wahala, za mu tabbatar mun samar da ababen bukatun mutanen Iran. Muna da isasshen sukari da man girki da sauransu. Muna da isassun kudaden kasar waje da za mu zuba a cikin kasuwa,” kamar yadda Rouhani ya fadi.
Amurka na shirin dawo da manyan takunkumin karya tattalin arziki ga kasar Iran a ’yan watanni masu zuwa, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar Nukiliya da Iran, wadda a lokacin da aiki da yarjejeniyar, an dauke mata wasu nau’ukan takunkumin.
Wannan lamarin zai iya shafar tattalin arzkin kasar, musamman kudin da take samu wajen sayar da man fetur.