Talakan Najeriya ne matsalar kasar

DA ZA MU IYA: A fahimtata, duk matsalar da talakan Najeriya ke ciki shi ya jawo ma kansa. Wannan lamarin ba a boye yake ba, domin kuwa hakan ya bayyana a fili, sai dai wanda ya fahimta ya fahimta kuma wanda bai fahimta ba, sai in ce Allah (SWT) ya ganar da shi. Mu talakawa […]

Talakan Najeriya ne matsalar kasar
Talakan Najeriya ne matsalar kasar

DA ZA MU IYA: A fahimtata, duk matsalar da talakan Najeriya ke ciki shi ya jawo ma kansa. Wannan lamarin ba a boye yake ba, domin kuwa hakan ya bayyana a fili, sai dai wanda ya fahimta ya fahimta kuma wanda bai fahimta ba, sai in ce Allah (SWT) ya ganar da shi. Mu talakawa mun kasa fahimtar ko mu su waye. Mun bari wasu na yi mana wasa da hankula, kai har ma da kwakwale.
DA ZA MU IYA: Allah sarki, a duk lokacin da na dubi halin da talakan Najeriya ke ciki na kuncin rayuwa, nakan sami kaina cikin damuwa, bakin ciki da tashin-hankali. Idan kuma na yi tunanin samun mafita, sai in fahimtar cewa kamar dai talakan ya saduda kuma ya debe tsammani daga kubuta ga sharrin ’YAN GURGUZU, wadanda su ne sababin ga halin da muke ciki. Babu tsaro a Najeriya. Babu ingantaccen ilmi a makarantu. Babu aikin yi ga ‘ya’yan talakawa. Babu tanadi ga lafiyar talakawa. Babu hanyoyi isassu domin sufuri da zirga-zirgan al’umma. Babu kulawa ga harkan tattalin arziki, a kullun sai ci baya da sukurkucewa yake yi. Babu tanadin da aka yi don rayuwar ‘ya’yanmu nan da shekara biyu masu zuwa, ballantana shekaru 50. Babu wutan lantarki. Babu kulawa ga harkan noma. Babu komai a Najeriya face cuta, danniya, wariya, kabilanci da rikicin addini da rashin hankali da rashin lissafi da rashin tunani da kidahumanci da yayi katutu a zukatan mu. To ina mafita?
DA ZA MU IYA: A fannin noma, ya kamata talaka ya koma gona. Ya mance da duk wasu burace-burace da yaudara na rayuwar birni. Matsalar Taki da ingantaccen Irin kuwa, tabbas idan duk mun koma gona, ko shakka babu, ‘yan kasuwa za su koma safarar taki da iri mai kyau. Kuma hakan zai sa mu koma amfani da abincin da muka noma, sa’annan ya rage ko dakatar da shigowa da matacciyar shinkafar da ake yi muna karya da ita daga kasashen ketare. Wallahi ko mu yarda ko kar mu yarda, noma shi ne kashin bayan tattalin arzikin kowace kasa. Mu koma gona haikan, noman rani da na damina. Ni dalibi ne na tattalin arziki (Economics) a jami’ar Usmanu danfodiyo, Sokoto kuma digiri na biyu (Master), amma na kudiri aniyar komawa gona kuma tuni na sami gona cikin gonakin babana, a tsakanin Kaduna da Zariya, don in yi noma koda kuma abincin da zan ciyar da iyalaina ne kawai. Idan kuma na noma fiye da abin da zan ci, sai in ajiye sauran ba zan sayar da gaggawa ba, har sai na fahimci inda aka dosa. Idan gwamnati ta kara kudin mai, nima sai in kara kudin amfanin gona don in maye kudin sufuri da zirga-zirga, domin na san masu mota za su kara kudin sufuri.
Abu na biyu kuma shi ne, idan da talaka ba ya sayen kayan abincin da ake shigowa da su, wallahi da tuni an daina shigowa da su. Mu sani wadannan ‘Yan gurguzun da ba za mu suke rawa. Mu dage mu noma abin da za mu ci, in ya so in sun sayo na kasashen ketare su ci su da ‘ya’yansu. Ko shakka na sani wannan maganar ba za ta yi wa KAWU ALIKO da ire-irensa dadi ba, amma ita ce gaskiya.
DA ZA MU IYA: A bangaren wutar lantarki kuwa, sai in ce shekaru 200 da suka wuce kakanninmu sun rayu ba wuta, to mu me zai hana mu iya rayuwa ba wutar? Wallahi, rashin amfani da wutar ba zai sa mu mutu ba. Kai, in takaice maka zance, kuma ko ka yarda, ko kada ka yarda, babu wuta a Najeriya. Kame-kame kawai da dabaru ake yi wa talaka. Allah sarki shi kuma sai biyan kudin wutar da bai sha ba yake yi. Wata rana aka samu sama da wata uku a anguwarmu a birnin Kaduna ba a ba mu wuta sai 12 na dare, kuma in biyar ta Asuba ta yi sai a dauke. Na garzaya ofishin NEPA, na ce su zo su yanke wutarsu ba na so. Na zauna sama da shekara daya da wata tara ban da wuta. Amma daga baya da aka fara amfani da MITAR more kudinka (pre-paid metre) sai na saya, don na san zan biya abin da na sha ne kawai. Wallahi, da duk ‘yan Najeriya za su yi haka da Gwamnati da ‘yan kasuwar wutar lantarki sun gyara matsalar wutar. Mun dai zama wawaye da gangan. Su kuma sai tatsar mu suke yi kulli yaumin. Kai yanzu ma an ce sun daina sayar da mitar more kudinka don za ta tona musu asiri.
DA ZA MU IYA: A harkar man-fetur sai in ce da ku, a ranar Laraba, 5/3/2014 na fito daga Jami’a, a birnin Sakkwato, da niyyar shiga gari in sha mai a mota, amma sai ga shi na ziyarci gidajen mai sama da goma ban samu ba. Sai na tambayi wani, ‘don Allah Malam ko ina zan samu mai, sai ya ce da ni sai na kama hanyar barin gari, zan samu kuma farashin famfo shi ne N185. Da jin haka sai na koma gidan wani abokina na ajiye motar, saboda da ma man da ke ciki ya kusa karewa. Duk wanda ya hadu da ni ya tambaye ni mota, sai in ce da shi, NA AJIYE TA SABODA WAHALA DA TSADAR MAI. Wallahi summa tallahi, da za mu daure, daga masu motocin haya da masu motocin da shiga, mu ajiye su, to komai zai tsaya chak kuma wallahi ba za su bari a yi wata guda ba, za su gyara. Amma kash, kullum nuna wa muke yi ba za mu iya rayuwa ba, sai da fetur.
DA ZA MU IYA: A gefen waya da kasuwanci da makarantu da asibiti da hanyoyi da sauransu, duk haka ya kamata mu yi. Ba sai mun yi zanga-zanga ko fito-na-fitoba da hukuma. Ba sai mun yi fada ba. Ba sai mun tada hankalin wani ba. Babu duka, babu zagi. “Ko ba magana, a zura ido ya isa mai hankali” inji Sani Sabulu.
Na sadaukar da wannan rubutun ga Dattijo, Farfesa Ango Abdullahi Zariya, wanda ya tabbatar wa duniya cewa zai iya rike Arewacin Najeriya da noman ridi. Lokacin da yake maida martani ga tsirarun mutanen da ke neman a raba Najeriya.
Ina rokon duk wanda ya karanta wannan tsokacin nawa, don Allah kar ya kuskura ya baiwa Kwamared Shehu Sani a Kaduna, labarin ababen da na fadi ko na rubuta.
Na gode.
Abdullahi Yusuf (0803-508-1948/0802-741-1571)

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya