Talakawa ke yin juyin juya-hali a ko’ina

Abubuwan da suke faruwa na canje-canjen jam’iyyu da canja sheka sun isa su sa talakawa su gane rauninsu su tashi tsaye su nema wa kansu kyakkyawar makoma. Duk wata masifa a kan talakawa take karewa. Babu lafiya, babu zaman lafiya. Sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro duk fushinsu a kan talakawa yake karewa, […]

Talakawa ke yin juyin juya-hali a ko’ina
Talakawa ke yin juyin juya-hali a ko’ina

Abubuwan da suke faruwa na canje-canjen jam’iyyu da canja sheka sun isa su sa talakawa su gane rauninsu su tashi tsaye su nema wa kansu kyakkyawar makoma. Duk wata masifa a kan talakawa take karewa. Babu lafiya, babu zaman lafiya. Sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro duk fushinsu a kan talakawa yake karewa, ba sa iya zanga-zanga ko da ta lumana ce a kan hakkinsu: kamar albashi da alawus da fansho da sauransu. Sai dai su kashe talakawa. 

Alhamdulillahi tunda har ta kai ga gwamnoni da sanatoci da wakilai da sauransu sun fara kokawa da zaluncin Gwamnatin Tarayya, ya kamata talakawa su farka saboda babu wanda ake zalunta kamar talaka. Wannan ita ce dama mafi dacewa da talakawa za su hada kai su kwaci hakki da ’yancinsu. Idan ba haka ba azzaluman masu mulki za su yi ta juya mulkin a junansu, zalunci ya yi ta ci gaba babu ranar dainawa.
Idan aka dubi masu fafutukar neman mulki daga masu mulki ne a yanzu sai wadanda suka taba yin mulkin. Kowannensu ya mallaki gidan kwana na kasaita ban da wadanda yake da su a wurare daban-daban, ya mallaki biliyoyin Naira ko Dalar Amurka, akalla daruruwan miliyoyi da hannayen jari a banki ko masana’antu ko kamfanoni da sauransu. Yayin da talakawa suke karewa da sabulu da ashana da taliya da Naira 50 a ranar zabe.
Ba za mu manta da kudinmu na tallafin man fetur Naira tiriliyan 2 da biliyan bakwai ba, adadin da ya wuce rabin kasafin kudin bana, ga matsalar James Ibori da Alameghsia da sauransu, ana jiran zabe ya zo a yi amfani da kudin a yi ka-ci-ba-ka-ci ba; ba-ka-ci-ba-ka-ci. Ga jami’an tsaro: soja da ’yan sanda da hukumar zabe da barayin mai duk sun hada kai. kungiyoyin kwadago duk sun zama karnukan farauta, shi ya sa na ce talakawa su ne kadai za su magance duk wata matsala da ta shafe su, idan suka hada kai ba tare da munafunci ko yaudara ba.
Ni dai na yi imani zalunci ba zai dore ba, komai ya yi tsanani maganinsa ya kusa zuwa. “Fa’inna ma’al usri yusra, inna ma’al’usri yusra.”
Idan muka juya kan masu rijiyar mai da barayin gurbataccen mai masu da’awa da cewa mansu ne saboda a jihohinsu ake hako shi, wannan yana nuna rashin sanin doka da oda ko kin yin aiki da su. Saboda duk wanda ya mallaki rijiyar mai ya mallaka ne karkashin wata doka da ta halatta masa mallakar, amma sata sata ce, babu halacci a yin sata ko wanen e barawon.
Shawarata ga masu rijiyoyin mai su kula da talakawansu, su magance musu yunwa da cututtuka ta hanyar shigo da abinci da magunguna masu yawa su rika tallafa wa masu tsananin bukata a duk fadin Najeriya tsawon shekara daya su ma su san suna da masu kaunarsu.
A bangaren gwamnati a yi aiki da Tsarin Mulkin Najeriya da ya tabbatar duk inda wani arziki ya bayyana na ’yan kasa ne baki daya. Idan akwai wadanda abin ya shafi muhallinsu sai a tashe su a ba su diyya ta kudi ko wani wuri ko duka biyun kamar yadda aka tashi mazauna Abuja aka mayar da wuraren nasu ya zama Birnin Tarayya. Ana iya gina wa duk mutanen Neja-Delta gidaje a ko’ina kamar 1004 irin na Legas komai yawansu. A mai da wuraren hako man (Gobernment Oil Producing Zone).
Suna satar danyen mai ganga dubu 100 a kullum, bugu da kari ana ba su kashi 13 na adadin kudin man da aka sayar, an yi musu Ma’aikatar kula da yankin Neja-Delta, an yi hukuma raya Neja-Delta, sannan a raba 87 da su. Haba!
TSARIN MULKIN NAJERIYA: Ya fayyace karara, duk arzikin kasa mallakar duk ’yan kasa ne. Kowane irin ma’adanai akwai doka da ake amfani da ita wajen wakilta masu kamfanonin da suke harka da ma’adanan na ’yan kasa da baki karkashin hadin gwiwa. Kasancewar dan kasa ya mallaki rijiyar mai ba wata alfarma ta musamman ba ce, ka’ida ce tunda ba tsarin gurguzu ake yi a Najeriya ba, balle a ce komai na gwamnati ne ita kadai. Ko a kasar da ake bin tsarin gurguzu ba a taba mallaka wa mai mulki ko bangaren da ake hakar ma’adanan arzikin bangaren ba. Abin bakin ciki da takaici sai ga shi a Najeriya wadanda suka mallaki rijiyoyin mai da makamantansu sun zama wulakantattu bayin mai mulki da bangaren da ake hako man ko ma’adanan. Saboda rashin tsoron Allah da kin fitar da Zakka sun zama bayin mai mulki sai yadda ya yi da su, ya karbi kudi a wurinsu ya yake su, ya yaki addininsu da kabilarsu da bangarensu, tun ana kashe ’yan uwansu har a zo kansu. Sun kasa farkawa, wasu daga cikinsu ana kwace abin da suka mallaka amma sun yi shiru ba sa so a san sun mallaki kazamar dukiya irin wannan, yayin da talakawa suke fama da kazamin talauci da yunwa da cututtuka.
A rika hukunta masu satar mai daidai da kowane irin barawo babu sassauci. Duk kasashen da suke sayen gurbataccen mai na sata a kai su Kotunan kasa da kasa domin bin kadin hakkinmu. Idan ta kama mu daina kowace ma’amala da kasashen. Haka su ma kasashen da suke ajiye wa barayin shugabannin Najeriya da abokan ma’amalarsu kucin da suka sace mana. Wannan aikin talakawa ne da suka fi cutuwa. Kamar yadda talakawa suka kori Turawa daga Najeriya aka samu mulkin kai a 1960. Sarakuna suka koma karkashin talakawa. Yanzu babu wani dan Bature ko Sarki da yake mulki tun daga sama har kasa. Tarihi zai iya maimaita kansa, yadda ta faru da, ta sake faruwa yanzu. Juyin juya-halin talakawa ne kurum zai iya tsarkake aikin jami’an tsaro a daina samun sojan gona da baragurbi a cikinsu wadanda ake zargi dama masu neman mafakar da za su aikata miyagun laifuffuka ne suke shiga aikin sabanin yadda abin yake a wasu kasashe irin su Birtaniya da ta raine mu. Haka bangaren shari’a da masu yin dokoki da masu zartarwa da duk jami’an gwamnati tun daga sama har kasa. Kowa ya dawo da abin da ya sata a sake rabo, talakawa su samu hakkinsu daidai da kowa. A samu cikakken tsaro na rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini a ko’ina a Najeriya.
Allah Ya ba mu ikon yi ta hanyar lumana!
Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN)
08023106666, 08060116666

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50