Talakawa na ba da gudunmawa wajen magudin zabe – Ajiyan Dass
Alhaji Alhassan Abubakar Sadik Ajiyan Dass na daya daga cikin ’ya’yan kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), tsohon ma’aikaci ne da ya rike mukamai daban-daban a ciki da wajen Jihar Bauchi ciki har da shugabancin Hukumar Zabe ta Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci kan siyasa da kuma halin da Arewa take ciki: […]
Alhaji Alhassan Abubakar Sadik Ajiyan Dass na daya daga cikin ’ya’yan kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), tsohon ma’aikaci ne da ya rike mukamai daban-daban a ciki da wajen Jihar Bauchi ciki har da shugabancin Hukumar Zabe ta Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci kan siyasa da kuma halin da Arewa take ciki:
A matsayinka na tsohon shugaban hukumar zabe wasu hanyoyi za a bi don magance magudin zabe a Najeriya?
A matsayina na tsohon shugaban hukumar zabe ta Jihar Bauchi ina tabbatar maka cewa talakawan Najeriya suna ba da gagarumar gudunmawa wajen magudin zabe. Misali akwai masu karbar taliya da indomi a lokacin zabe saboda haka matukar za mu ci gaba da yin haka ba za a taba magance magudin zabe ba. Kowa ya ga sakamakon karbar taliya a lokacin zabe, da yawa daga cikin ’yan siyasa suna alkkawura daban-daban ga al’umma a lokacin da suke yawon kamfen amma da zarar hakarsu ta cimma ruwa sai su yi watsi da alkawuran da suka dauka a baya. Bayan haka akwai wasu daga cikin ’yan siyasa wadanda da zarar ka shiga ofis babu abin da suke bukata kamar ka rika ba su makuden kudi da motoci da babura da kujerun aikin Hajji da makamantansu. Kudin da za a yi aiki ga al’umma shi za a dauka a rika ba wasu mutane ’yan tsirari a tsakanin al’umma. Mutanen kudancin kasar nan sun bambanta da ’yan siyasar Arewa, domin kafin mutum ya fito takara sai ya fada wa al’umma yara nawa ya dauki nauyinsu zuwa jami’o’i? Wace gudunmawa ya kawo ga mutanen unguwarsu. Idan mutum ya tsaya takara a Arewa abin da al’umma suke bukata a wajensa shi ne ya rika raba musu kudi dare da rana, daga nan sai a rika manna hotunansa a bakin hanya ana zagin uban kowa. Saboda haka kaga babu wadanda suka fi talauci da jahilci da rashin sanin ya kamata, kamar wasu daga cikin talakawan Arewa ga yawa amma yawan ba ya da amfani.
Yaya kake kagin makomar Najeriya nan da shekara ta 2015?
Makomar Najeriya Allah ne kawai Ya san abin da zai faru nan da zaben shekara ta 2015, amma tabbas za a murza gashin baki daga bisani za a daidaita. Domin da dan Arewa da dan Kudu babu wanda zai iya zama shi kadai, saboda haka sai kowa ya kai zuciya nesa kafin abubuwa su daidaita. Da kudin Arewa ne aka fara hako man fetur da ake yi mana gori a halin yanzu, kuma muna da ma’adanai a karkashin kasa a sassa daban-daban na Arewa. Babbar matsalarmu ita ce ba mu da shugabanni nagari masu zurfin tunani.
Akwai masu cewa ya kamata a raba Najeriya kowa ya kama gabansa?
Magana ta gaskiya ita ce ba na goyon bayan masu cewa a raba Najeriya kowa ya kama gabansa, za mu ci gaba da zama haka har zuwa lokacin da Allah zai magance mana abubuwan da suke damunmu. Kuma ya kamata Shugaba Jonathan ya fahimci cewa babu wani Shugaban kasa da ya taba kammala ayyukan da ya fara a lokacin mulkinsa don haka ya yi hakuri ya nemi ra’ayoyin ’yan Najeriya, domin su ne alkalai.
Kwanakin baya Farfesa Ango Abdullahi sun kira taron manema labarai game da halin da Arewa take ciki da batun ’yan matan Chibok da aka sace sama da wata uku. Saboda haka Shugaba Jonathan ya kamata ya nemo inda aka boye wadannan yara ya kuma mika su hannu iyayensu lafiya. Shugaba Jonathan ne yake nada shugaban rundunar ’yan sanda na kasa, shi yake nada shugaban hukumar leken asiri ta kasa wato (SSS) da sauran masu ruwa da tsari a fannonin tsaro da sauransu. An kashe mutane da dama a jihohin Arewa maso Gabas kamar Borno da Yobe da Adamawa da Taraba da sauran manyan jihohi, saboda haka ya kamata Gwamnatin Tarayya ta sake salo game da yadda take tafiyar da harkokin tsaro.
Mene ne sakonka ga matasan da suke zaman kashe wando?
Shekara sittin da suka gabata lokacin ina aikin malanta da wahala ka ga matashi yana zaman kashe wando, amma yanzu idan ka duba wadanda suka kammmla karatunsu a jami’oi daban-daban na Najeriya ba su da aikin yi. Bayan haka babu masana’antun da za su samar wa matasa hanyoyin samun kudin shiga. Idan matasa suka zauna ba su da aiki dole barayi su yi yawa a tsakanin al’umma. Don Allah matasa ku kama sana’a koda yankan farce ne zai magance mutuwar zuciya, ya kamata matasa ku fahimci haka.
Daga karshe mene ne sakonka ga ’yan Najeriya?
Babban sakona ga mutanen Najeriya shi ne don Allah mu ci gaba da hada kanmu waje daya domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba sai da zaman lafiya. Don haka kowa ya ga abubuwan da ke faruwa a kasar nan, talauci ya yi kamun kazar kuku ga mutanen kasar nan.