Talakawa na bukatar taimakon gaggawa
Halin da ake ciki a kasar nan akwai bukatar gwamnatoci a matakai daban-daban su samar da wata katafariyar gidauniya da za ta rika kula da talakawa marasa karfi domin ceto rayuwar mutanen da suke cikin tsananin bukata a daukacin kananan hukumomin kasar 774, musamman a wuraren da suka fi fama da annoba. Baya ga Gwamnatin […]
Halin da ake ciki a kasar nan akwai bukatar gwamnatoci a matakai daban-daban su samar da wata katafariyar gidauniya da za ta rika kula da talakawa marasa karfi domin ceto rayuwar mutanen da suke cikin tsananin bukata a daukacin kananan hukumomin kasar 774, musamman a wuraren da suka fi fama da annoba.
Baya ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, hukumomi da manyan kamfanoni da masana’antun da ake da su a Najeriya tun daga kan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kamfanin Mai na kasa (NNPC) da kamfanonin sadarwa da na gine-ginen hanyoyi da gadoji da bankuna da sauran masana’antu a sanya kowanne ya rika bayar da akalla kashi daya da rabi cikin 100 na dukiyar da ya mallaka ko kashi 5 cikin 100 na ribar da ya samu a shekara a zuba a cikin gidauniyar.
Sannan masu hakar mai da harkar sufurinsa na shiga da fitarsa da daidaikun masu dukiya su kuma su bayar da akalla kashi daya cikin 40 na adadin abin da suka mallaka.
Idan haka ya samu sai gwamnati ta yi amfani da wannan kudi wajen sayen kayan amfani gona a kara ya wadaci masu tsananin bukata na tsawon wata shida zuwa shekara daya.
A shigo da magunguna masu inganci a wadace, a zuba su a asibitoci su ishi marasa lafiya marasa karfi na tsawon shekara a rika raba su kyauta, shekara ta gaba kuma a fara sayarwa a kan rabin kudinsu, har sai komai ya daidaita, kowa ya dawo cikin hayyacinsa.
Ina kira ga gwamnati ta gaggauta kaddamar da wannan gidauniya ta musamman domin ceto al’ummar kasar nan daga hallaka. Koda za a kashe kashi 99 cikin 100 na duk dukiyar da gwamnati ta mallaka ne wajen ceto al’umma riba ce ga kasar nan, domin rashin ceto al’umma muguwar asarar ce a duniya da Lahira. Domin hakan zai haifar da karuwar miyagu a cikin jama’a, zai sanya masu raunin imani su rasa imanin, marasa imanin kuma zuciyarsu ta dada kekashewa su yi ta aikata barna da fasadi a bayan kasa, ta yadda kowa zai hadu da illarsu.
Tabbas damina ta yi kyau, kuma an yi noma a kasar nan, alhamdulillahi Allah Ya albarkace mu da damina mai kyau, an samu abinci. To amma, kada a manta ba kowa ne manomi ba. Kuma ko a manoman akwai kanana marasa karfi, sannan ga ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati ko na kamfanoni da sauran raunanan cikin jama’a da a yanzu suke cikin mugun kuncin rayuwa da suke cikin tsananin bukatar a ceto rayuwarsu.
Lallai akwai bukatar a dubi wannan batu da idon basira domin a yi wa tufkar hanci, talakan Najeriya ya sadaukar da rayuwa da jin dadinsa wajen zaben wannan gwamnati, kuma ya sadaukar da kansa wajen ba ta goyon baya duk da irin kunci da wahalar da ya shiga, don haka lokaci ya yi da gwamnatin za ta saka masa. Zai fi kyau a dakatar da kowane aiki a yanzu domin kyautata rayuwa da jin dadin jama’a, domin duk aikin da za a yi, saboda mutanen da suke cikin wahalar ake yi. Idan talaka yana cikin kunci ba zai ga amfanin kwaltar da aka yi a unguwarsu ba, idan talaka yana fama da jinya ba zai damu da ruwan famfo ko na burtsatsen da aka yi a unguwarsu ba.
Yayin da a gefe guda kuma za a ci gaba da kwato dukiyar da barayin shugabanni suka sace, wanda hakan ya tagayyara kasar nan. Ina ganin lokaci ya yi da za a fara a kashe na kashewa da daure na daurewa daurin rai da rai, na irin wadannan miyagun shugabanni da suka ruguza kasar nan saboda kasa ta zauna lafiya.
Bai kamata a ci gaba da zama ana zuba ido ga irin wadannan miyagu kuma barayin shugabanni suna yawo da gudanar da rayuwarsu a fili kamar babu abin da suka yi wa kasar nan ba. Abin takaici ne a kyale irin wadannan miyagun shugabanni masu yin jan ido wajen neman mulki da suka kashe kasa su rika ci gaba da rayuwa a cikin jama’a ba tare da an hukunta su ba, kuma babban abin takaici har ma ana ganinsu suna kashe daruruwan miliyoyin Naira duk wata wajen lalata tarbiyyar matasa maza da mata da marayu da zawarawa da matan aure, ta hanyar ba su dan abin sanyawa a bakin salati daga abin da suka sace a jihohi da tarayya. Sannan a gefe guda suna lalata rayuwarsu, ta hanyar ba su abubuwan da suke sanya maye a dabararsu ta tsallake siradin barnar da suka yi tare da bacewa a cikin rububi, ta yadda za a dauke su a matsayin mutanen kirki. Ina kirki ga wanda ya sace dukiyar jiharsa, ya fi jihar dukiya saboda kawai ya zama Gwamna? Ina kirki ga mutumin da ya fi ma’aikatarsa dukiya, saboda ya zama Minista ko Kwamishina? Ina kirki ga mutumin da ya fi karamar hukumarsa dukiyam saboda kawai ya zama ciyaman?
kasar nan ba za ta gyara ta dawo kan turbar kwarai ba, sai mun yarda cewa duk wanda ya yi shugabancin jama’ar da muka gani da maka-makan gidajen kasaita da manya-manyan motocin hawa da jiragen ruwa da na sama da jari a kamfanoni, ba fa halalinsa ba ne na sata ne. Tilas mu tabbatar an hukunta irin wadannan miyagun shugabanni domin ba sai an je Lahira ba, kowa ya san dukiyar nan ta haram ce, kuma sace ta ya jefa kasar nan a cikin bala’i da kuncin a yanzu.
Siyasa dai ba hauka ba ce, mulki kuma ba kasuwanci ba ne, yi wa jama’a da kasa hidima ne. Duk wanda ba haka zai yi ba, bai kamata ya zama koda shugaban jama’ar gidansa ba, balle ya shugabanci jama’a a unguwa ko gunduma ko karamar hukuma ko jiha, balle a kai ga kasa.
Duk wanda ya san rayuwar su Sa Abubakar Tafawa balewa da Sa Ahmadu Bello Sardauna da Malam Aminu Kano da Maitama Sule da Janar Murtala Mohammed da Janar Muhammadu Buhari a nan Arewa da su Nnamdi Azikiwe da Obafemi Awolowo da sauransu a Kudu, ya san siyasa da mulki ba na kazaman mutane ba ne, ba na barayi ba ne, ba na fajirai ’yan kungiyar asiri masu rudar da matasa ’yan shekara 25 da ba su da goguwar aiki ko sana’a, sai shaye-shaye da fajirci ba ne.
Alhaji Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN),
Tsohon Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, (KACCIMA)
08060116666, 08023106666