Talakawa ke yin zanga-zanga — Portable
Mawaƙin ya ce masu kuɗi irin su Dangote da sauransu ba sa shiga zanga-zanga.
Fitaccen mawaƙin Kudancin Najeriya, Habeeb Okikiola wanda aka fi sani da Portable, ya ce talakawa ne ke yin zanga-zanga, saboda haka shi ba zai shiga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta ba.
Portable wanda ya bayyana cewar da shi aka gudanar da zanga-zangar da aka yi a 2020 lokacin yana talaka, ya ce yanzu likkafa ta ci gaba.
- Zanga-zanga: Gwamnati ta tsaurara tsaro a iyakokin Najeriya
- An sanya ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Jigawa
Saboda haka zai mayar da hankali a kan harkokinsa maimakon shiga cikin zanga-zangar da matalauta ne za su yi.
A saƙon bidiyon da ya wallafa, ya yi tamabayar cewar, ko mutane sun ga attajirai irin su Femi Otedola da Aliko Dangote da Dele Momodu na shiga zanga-zanga?
Mawaƙin, ya ce duk mai cewa ya je wajen zanga-zangar domin yin waƙa, ba zai gama da duniya lafiya ba, yayin da ya buƙace su da su, su je su yi waƙa a wajen.
Portable, ya ƙara da kira ga jama’a da su yi wa kan su yaƙi wajen inganta rayuwarsu maimakon yi wa Najeriya yaƙi, inda ya bayyana cewar babu matsalar da ta addabi Najeriya.
Mawaƙin ya kuma buƙaci masu sha’awar waƙoƙinsa da su ƙauracewa shiga zanga-zangar da ake shirin yi wajen fuskantar harkokinsu na yau da kullum.