Talakawa suka zabi Buhari amma masu kudi ke cin gajiyar mulkinsa – Alhaji Nura Idris

Alhaji Nura Idris dan kasuwa ne a Jihohin Kurmi sannan jigo ne a tafiyar akidar Kwankwasiyya a Jihohin Kurmi.   Ya bayyana cewa talakan da ya yi ruwa da tsaki ya kasa, ya tsare har Allah Ya bai wa shugaba Buhari mulkin kasar nan ba ya cin gajiyar mulkin sai wasu tsirarun masu hannu da shuni […]

Talakawa suka zabi Buhari amma masu kudi ke cin gajiyar mulkinsa – Alhaji Nura Idris

Alhaji Nura Idris dan kasuwa ne a Jihohin Kurmi sannan jigo ne a tafiyar akidar Kwankwasiyya a Jihohin Kurmi.   Ya bayyana cewa talakan da ya yi ruwa da tsaki ya kasa, ya tsare har Allah Ya bai wa shugaba Buhari mulkin kasar nan ba ya cin gajiyar mulkin sai wasu tsirarun masu hannu da shuni wadanda ke amfana da matsin rayuwar da aka jefa talakan a cikin. 

“Wannan abu a zahiri yake,  za ka ga tun lokaci da shugaba Buhari ya kama madafun iko a shekarar 2015 kayayakin masarufi ke neman fin karfin talakan kasar nan,  a wannan lokacin ne farashin shinkafa ya yi tashin guwaron zabi, hakazalika duk kayayyakin masarufi sun hauhawa tun bayan karin farashin man fetur da wannan gwamnati ta yi, yanzu haka matsakaitan ‘yan kasuwa da talakawa da kananan ma’aikata na cikin halin ha’ula’i,” in ji shi.

Alhaji Nura Idris ya bayyana haka ne a taron da magoya bayan kungiyar Kwankwasiyya suka gudanar na daukacin Jihohin Kudu maso Yamma taron da ya gudana a karshen makon da ya gabata a garin Ile-Ife a Jihar Osun, inda ya samu halartar shugabanin Yarbawan yankin masu akidar Kwankwasiyya da ’yan Arewa mazauna yankin.

A zantawar da Aminiya ta yi da Alhaji Nura Idris wanda ya jagoranci taron y’a shaida cewa a shirye suke su mara wa gwaninsu baya wato tsohon Gwmanan Kano, Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, “a shirye muke mu goya wa jagoranmu Kwankwaso baya a ko wacce jam’iyya ya tsaya takarar shugaban kasa za mu bi shi,  fatan mu gwaninmu ya yi takarar shugabancin kasar nan domin shi ke da tsarin sauyin da talakawa suka dade suna muradi,” inji shi. 

daya daga cikin shugabanin Yarbawan da suka halarci taron wanda shi ne jagoran tsare-tsare na tafiyar Kwankwasiya a Jihohin Kudu maso Yamma Honurabul Awotidefumi Akwatoke ya shaida wa Aminiya cewa kyawawan ayyukan da tsohon gwmanan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya aiwatar a lokacin da yake Gwamnan Kano ne ya ba shi sha’awar ya fito domin a yi tafiyar da shi.

“Fatan mu Allah Ya bai wa Kwankwaso jagorancin kasar nan domin ya yi an gani a Kano, ’ya’yan talakawa sun amfana da shirye-shiryen bunkasa ilimi baya ga tarin manyan ayyukan da ya gudanar.   Shawarata a wannan tafiya ta Kwankwasiyya a ba mata da matasa mahinmmanci domin suna da gagarumar rawar da za su taka, a kuma hada kai a yi aiki tukuru domin mu cinmma gaci,” inji shi.

Sarkin Samarin Ile-Ife Alhaji Shehu Ahmad, kira ya yi ga matasan kasar nan su fito su mara wa Kwankwaso baya domin Kwankwaso ne ke kishin talakawanmu da matasan mu,  mu mutanen Ile-Ife shaidu ne,  lokacin da Allah Ya jarrabe mu da ibti’la’i a kwanakin baya shi ne ya fara kawo mana tallafi ya kuma jagoranci sasanta rikicin,” in ji shi. 

Jagoran matan Arewa a tafiyar siyasar ta Kwankwasiyya Hajiya Asabe Sahabi ta shaida wa Aminiya cewa a baya sun yi aiki tukuru wajen tallata shugaba Buhari har ya dafe madafun iko amma gwamnatinsa ta yi watsi da mata da matasa don haka suka sauya sheka don mara wa kwankwaso baya kuma suna da tabbacin da yardar Allah zai samu nasara ya kuma kawo sauyin da ’yan Nigeriya ke fata.