Talakawa za su yi maganin ‘yan majalisar xa ke kafar ungulu ga vuhari – Xanlaxi Pasali
Alhaji Xanlaxi Garva Pasali shi ne Sakataren kungiyar xillalan Mai ta kasa kuma Koxinaten kungiyar yakin neman zaven shugavan kasa Muhamma vuhari (vCO). A wannan tattaunawa xa ya yi xa wakilinmu, ya vayyana vatutuwa xa xama ciki har yin nuni xa cewa talakawan Nijeriya za su yi maganin ‘yan majalisun tarayya xa suke yi wa […]
Alhaji Xanlaxi Garva Pasali shi ne Sakataren kungiyar xillalan Mai ta kasa kuma Koxinaten kungiyar yakin neman zaven shugavan kasa Muhamma vuhari (vCO). A wannan tattaunawa xa ya yi xa wakilinmu, ya vayyana vatutuwa xa xama ciki har yin nuni xa cewa talakawan Nijeriya za su yi maganin ‘yan majalisun tarayya xa suke yi wa gwamnatin Shugava vuhari kafar ungulu, ta hanyar kin sake zavensu a zaven 2019 mai zuwa. Ga yaxxa tattaunawar ta kasance:
Aminiya; Ya ya ka kalli xagewar xa Majalisar xattawa ta yi game xa sai an cire Shugavan EFCC xaga mukaminsa?
Xanlaxi Pasali: Wato gaskiyar magana kowa ya san cewa avin xa ya shafi naxa shugavan hukumar EFCC yana hanun shugavan kasa ne. Kuma a ka’ixa ixan ka xuva xokar ma va a ce, a kai majalisar xattawa xomin ta amince va. Savoxa an sami shugavan kasa ne wanxa yake vaiwa kowa xamarsa, shi ne ya saurare su. xon haka ‘yan majalisar xattawan nan suna yauxarar kansu ne kan maganar naxa Magu. Savoxa waxansu xaga cikinsu tsofaffin gwamnoni ne waxanxa kowa ya riga ya san yaxxa suka ji xaxin harkar cin hanci xa rashawa a kasar nan. Savoxa haka suna ganin yaki xa cin hanci xa rashawa xa gwamnatin vuhari take yi, kamar tana yi xa su ne. Suna vata lokacinsu ne kawai. xomin al’ummar Nijeriya suna goyon vayan gwamnatin vuhari kan wannan yaki xa cin hanci xa rashawa xa take yi.
Ya kamata kowa ya tsaya kan ka’ixar xa tsarin mulki ya va shi. Maganar yaki xa cin hanci xa rashawa a kasar nan, ko mutum yana so ko vaya so xole ne ya yarxa. xomin Shugavan kasa ya riga ya cusa wannan yaki a zuciyar talakawan Nijeriya. xon haka va zasu yarxa wasu mutane su cigava xa kwashe xukiyar Nijeriya va.
Kuma ya kamata mu fahimci cewa kasar nan tana tafiya xaixai a wannan gwamnati ta shugavan kasa Muhammax vuhari. xomin an sami nasarori xa xama an wayar xa kan mutane, ma’aikata kowa ya xauki sai ti. An sami cigava ta vangaren tsaro xa vangaren aikin noma. xon haka ‘yan majalisa su sani cewa lokacinsu ya kusa karewa. Kuma xuk xan majalisar xa al’ummar Nijeriya suka gano cewa yana xaya xaga cikin masu yi wa gwamnatin vuhari kafar ungulu za su yi maganinsa a zave mai zuwa.
Aminiya; Mene ne zaka ce kan maganar rashin lafiya Shugava vuhari xa ake ta magana a kai?
Xanlaxi Pasali: ‘Yan axawa xa waxanxa suka hanxame kuxaxen Najeriya a kullum suna vaxa fassara iri-iri kan wannan rashin lafiya. Ixan ka xuva shugavan kasa shugava ne mai vin ka’ixa. Kuma ya sami mataimaki xa ya san avin xa yake yi wanxa kusan ra’ayinsu xaya. Ixan ka kula kafin shugava vuhari ya sake fita sai xa ya karvi ‘yan matan Chivok xa aka sako ya yi masu jawavi. Amma kafin hakan wasu ma cewa suke yi vaya ‘iya fita vaya iya yin magana xa xai sauransu. Shi shugava vuhari mutum ne mai ka’ixa ixan likitansa ya ce ayi wani avu, ya kan tsaya ya ga cewa an yi wannan avin. Kuma ina son na tavvatar maka cewa muna xa cikakken vayani cewa ya sami sauki kan rashin lafiyar xa yake yi. Muna ganin a cikin wannan mako in Allah ya yarxa zai xawo Nijeriya ya ci gava xa aikinsa.
Aminiya; Wane irin guxumawa ne al’ummar Filato suka vayar wajen kafa wannan gwamnati ta canji, musamman Jos ta Arewa?
Xanlaxi Pasali: Ixan ka vinciki yawan kuri’un xa aka jefa a Najeriya a zaven shugavan kasa a 2015 a matsayinka na xan jarixa zaka gano cewa a cikin kananan hukumomi guxa 774 xa ake xa su a Nijeriya. karamar hukumar Jos ta Arewa ce kan gava wajen yawan kuri’un xa aka jefawa shugavan kasa Muhammax vuhari. Savoxa tun lokacin xa ya fara fitowa takara mutanen Jos suke zavensa, va su tava zaven wani va a matsayin shugavan kasa in va shi va. Savoxa mutanen Jos sun xauki shugava vuhari kamar xan Jos ne. Savoxa zaman xa ya yi a garin wasu xa xama sun san shi, sun san halayensa. xon haka sun xauke shi kamar xan Jos, xon haka suka vashi kuri’a fiye xa kowa a Najeriya. Haka kuma a vangaren zaven gwamnan Jihar Filato Simon Lalong mutanen Jos ne suka tsaya suka vaxa guxunmawa wajen zavensa. xon haka xa gwamnatin jihar Filato xa gwamnatin tarayya xukkansu mutanen Jos suna alfahari xa cewa sune kan gava wajen vaxa guxunmawar zavensu.
Kuma Allah ya taimakemu mun sami gwamna Lalong mutum ne wanxa yake tafiya xa kowa a gwamnatinsa. vavu ruwansa xa kavilanci ko vanvancin axxini, xon haka ya jawo kowa xa kowa a gwamnatinsa. xon haka yanzu an sami zaman lafiya xa kwanciyar hankali a jihar a cikin shekara viyu. Jihar xa aka yi shekara 16 ana fama xa rikice rikice, amma yanzu zaman lafiyar xa aka san jihar xa shi ya xawo. Yau an fara yin taki a jihar ana kaiwa wasu jihohi, ga ayyukan raya kasa nan ta ko’ina a jihar ana yi.