Talakawan Najeriya mu farka
Ya ‘yan uwa talakawan Najeriya lokaci ya yi da zamu farka daga barcin da muke domin fuskantar kalubalen dake gabanmu. Tun kafin wankin hula ya kaimu dare. Idan mu ka yi la’akari da halin kuncin rayuwar da muka tsincin kawunanmu, da suka hada da: talauci da fatara, yunwa, jahilci da cututtuka da rashin ayyukan yi […]
Ya ‘yan uwa talakawan Najeriya lokaci ya yi da zamu farka daga barcin da muke domin fuskantar kalubalen dake gabanmu. Tun kafin wankin hula ya kaimu dare. Idan mu ka yi la’akari da halin kuncin rayuwar da muka tsincin kawunanmu, da suka hada da: talauci da fatara, yunwa, jahilci da cututtuka da rashin ayyukan yi da fashi da makami da kuma fashi da biro.
Abin sai dai a yi shiru kurum! amma ya wuce dukkan inda ake tunani! Sannan uwa uba fargaba da rashin kwanciyar hankali sakamakon kashe-kashe na ba gaira ba dalili. Sun jefemu cikin kidima da rashin sanin abin yi! Ya ‘yan uwa dole mu yi fargar jaji domin dakile wadannan masifu tun kafin su ida kai mu ga kushewa. Lokaci ya yi da zamu yi karatun ta nutsu, mu san ciwon kanmu ta hanyar damka amanar jagorancinmu a hannun mutanan dake kishinmu. Tilas mu yi watsi da dabi’ar kwadayi da maula da fadanci, tare da tumasanci ga wadanda ba su san kimarmu ba ko darajarmu a matsayinmu na wadanda ake jogoranta. Mu daina sayar da ‘yancinmu da abin da ba ya iya magance mana talaucin da muke ciki. Kai! Ko karin kumallo ba ya wadatar da mu.
Ya ‘yan uwa idan mu ka yi la’akari da al’amuran da suka guduna tun bayan komawar Najeriya bisa tafarkin dimokuradiyya. Kimanin shekaru 15 ke nan bana. Babu abin da za mu iya bayyanawa a matsayin roman dimokuradiyya da muka ci gajiyarsa. Face shekaru ne na mawuyacin hali da tsadar rayuwa.
Shugabannin siyasa sun sha daukar alkawura a lokacin yakin neman zabe, akan za su ingantata mana rayuwa da kawo saukin halin kuncin da muke ciki, matukar muka ba su dama, ta hanyar jefa masu kuri’unmu. Mun sha fita a lokuta daban-daban, a yanayi daban-daban da ya hada da damiuna da hunturun sanyi da zafin bazaar, don kada kuri’unmu ga zaben shugabaninmu. Sai dai abin takaici da bakin ciki da zarar mun kammala turin motar, sai ta tashi ta bulbulemu da hayaki, ko kyallin ta ba mu kara gani. Don haka nike kara jan hankalinmu game da shugabanin siyasar nan, yadda ba sa cika mana alkawuran da suka dauka. Mu yi duba ga wakilanmu tun daga kan majalisar dokoki na jiha da ta wakilai a matakin tarayya da kuma majalisar dattawa kan yadda suke yawan bijire wa ra’ayoyinmu.
Idan muka kalli kalmar wakili, ko wakilci tana nufin ka aiki, ko ku aiki wani mutum, ko wasu mutane da wani sako da ake so a isar, amma sakamon wani dalili da ka iya zama tarnaki ga samun damar halarta da kanka/ku, wanda ka iya kasancewa rashin lafiya, ko rashin ilimi akan batun, ko kuma ya kasance akwai hadari da wahalarwa game da zuwa da kanka/ku. To sai ka/ku tura wakili a madadinka/ku. Sannan shi wakilin nan ba ya da wani ra’ayi nasa, idan ba naka/ku ba, ba shi da damar yanke wani hukunci face abin da yake daidai da ra’ayinka/ku. Dukkan wani al’amari da ka iya tasowa wurin isar da sakon, ko tattaunawar da ya yi hannun riga da abin da aka aike shi akai. To sai ya tuntubeka/ku, domin jin matsayarka/ku. A takaice wannan dan guntun bayanin da na yi a sama shi ne ma’anar wakili ko wakilci a karamar fahimta ta. Amma a yau an wayi gari wakilan da muka zaba a majalisun kasar nan don su wakilcemu, sun koma suna wakiltar kawunansu ba mu ba. Idan muka yi duba ga batutuwan da ake tattaunawa, ko ake mahawurarsu a majalissun kasar nan.
To a kashi dari, kashi casa’in ba ra’ayin talakawa ba ne, amma ake zartar da su. Misali mu kalli abin da ya faru lokacin maganar janye tallafin man fetur. Wakilanmu suna gani aka jefa mu cikin kuncin rayuwa ba tare da daukar wani mataki ba. Saboda man fetur ya shafi rayuwar kowa da kowa, mai abin hawa da wanda ba shi da abin hawan! Haka batun cuwar-cuwar tallafin man fetur da kananzir shiru kake ji, ba abin da suka yi don kwato mana hakkin mu. Sannan ga maganar wutar lantarki da ta hadiye miliyoyin daloli, kuma ta ki samuwa, har yanzu muna cikin duhu.
A gabansu aka yi rub da ciki da kudin fansho, da kuma sayen motocin alfarma da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta yi. Da maganar badakalar jirgin ministar albarkatun man fetur. Kai da ma sauran abubuwan da ba sa lissafuwa a wannan filin. Wani yunkuri suke yi don tsayawa kai da fata don ganin an mayar mana da hakkokinmu? Ai mu suke wakilta ba kansu ba.
Ga kuma sabuwar fitinar da ta bullo, ta yunkurin tsige gwamnonin adawa, wadda har ta rutsa da Gwamnan Adamawa. Sai kuma mu kalli yadda a Jihar Nasarawa talakawa suka tashi tsaye wajen kare wanda suka zaba ya jagorancesu a bisa ‘yancinsu da suka tabbatar! Sabo da haka talakawa mu sani kamar yadda dokar zabe ta ba mu damar aika wakili don wakiltarmu, to haka kuma a hannu daya ta ba mu damar jefa kuri’ar kiranye ga dukkan wakilin da ya bijire wa ra’ayinmu. To ya rage garemu ko musabunta rayuwarmu ta hanyar tabbatar da aika wakilai nagari da kuma mayar da wanda ba ya wakiltar gida, ko kuma mu dauwama cikin kaskanci. Allah Ya saukake, ‘Amin’.
Injiniya Jibril Abdul Daura 08038997861,08022997043