Gobe za a bayyana Gwarzon Dan Kwallon Afirka na bana

A gobe Talata ake sa ran Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) za ta sanar da Gwarzon Dan Kwallon Afirka na bana. Za a yi bikin ne a Masar inda ake sa ran masu horar da kungiyoyin kwallon kafa na kowace kasa a Afirka da kyaftin-kyaftin da manyan ’yan jarida da masu ruwa- da-tsaki […]

Gobe za a bayyana Gwarzon Dan Kwallon Afirka na bana

A gobe Talata ake sa ran Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) za ta sanar da Gwarzon Dan Kwallon Afirka na bana.

Za a yi bikin ne a Masar inda ake sa ran masu horar da kungiyoyin kwallon kafa na kowace kasa a Afirka da kyaftin-kyaftin da manyan ’yan jarida da masu ruwa- da-tsaki a harkar kwallon kafa da ’yan kwallo da suka taba lashe wannan gasa a Afirka za su kada kuri’a don zabo gwanin na bana.

A bangaren maza za a fafata ne a tsakanin ’yan kwallo uku da suka hada da Mohammed Salah dan asalin Masar da Sadio Mane dan asalin Senegal da suke kwallo a kulob din Liberpool na Ingila da kuma Riyad Mahrez dan asalin Aljeriya da ke kwallo a kulob din Manchester City na Ingila.

Duk wanda ya fi samun kuri’u ne zai lashe gasar ta bana.

Baya ga bangaren maza za a gudanar da gasar a bangaren mata da bangaren kwallon kafa na maza na matasa da kasashen da suka fi nuna kwazo da kocin da ya fi nuna kwazo da sauransu.

A duk shekara ce ake gudanar da wannan gasa.