Talata za a fara gasar cin kofin zakarun kulob-kulob a Nahiyar Turai
A ranar Talata 17 ga watan Satumba da kuma Laraba 18 ga watan ne ake sa ran kungiyoyin kwallon kafa guda 32 da ke sassa daban-daban a Nahiyar Turai za su fara kece raini a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.A tarihin kwallo, idan aka cire kofin duniya, […]
A ranar Talata 17 ga watan Satumba da kuma Laraba 18 ga watan ne ake sa ran kungiyoyin kwallon kafa guda 32 da ke sassa daban-daban a Nahiyar Turai za su fara kece raini a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
A tarihin kwallo, idan aka cire kofin duniya, babu wani kofi da ke da armashi da ya wuce na zakarun kulob-kulob a Nahiyar Turai.
Hatta gidajen da ke nuna kwallo musamman wadanda ke kasar nan sun fi samun kudin shiga a lokacin da gasar ke gudana.
A gasar da aka yi a bara kulob din Bayern Munich da ke Jamus ne ya samu nasarar lashe kofin bayan ya lallasa takwaransa Borussia Dortmund da ke Jamus da ci 2-1 a wasan karshe.
A wannan shekarar kuma ana sa ran kungiyoyin kwallon kafa kimanin 32 ne za su fafata a matakin farko.
Kulob da dama irin su Real Madrid da FC Barcelona da ke Sifen da na Manchester United da Chelsea da Arsenal da Man City dukkaninsu a Ingila da kuma Jubentus da AC Milan da ke Italiya da PSG da Napoli da ke Italiya duk sun shirya don tunkarar gasar ce ta hanyar cefano zaratan ’yan kwallon da suke ganin za su kai su ga tudun-mun-tsra a gasar.