Talata za a fara Gasar Zakarun Turai

Shekara kwana, kamar yadda masu iya magana kan fadi.  A ranar Talata mai zuwa 17 ga Satumba za a fara Gasar Zakarun kulob na Turai.  Idan za a tuna a bara kulob din Liberpool ne ya lashe gasar bayan ya lallasa na Tottenham a wasan karshe da ci 2-1. A ranar Talatar wasannin da za […]

Talata za a fara Gasar Zakarun Turai

Jurgen Klopp

Shekara kwana, kamar yadda masu iya magana kan fadi.  A ranar Talata mai zuwa 17 ga Satumba za a fara Gasar Zakarun kulob na Turai.  Idan za a tuna a bara kulob din Liberpool ne ya lashe gasar bayan ya lallasa na Tottenham a wasan karshe da ci 2-1.

A ranar Talatar wasannin da za su fi daukar hankali su ne na tsakanin Borussia Dortmund na Jamus da FC Barcelona na Sifen da wasan Napoli na Italiya da Liberpool na Ingila da kuma wasan Balencia na Sifen da Chelsea na Ingila.

Sai a washegari Laraba wasannin da ake ganin za su fi daukar hankali su ne na Paris Saint Germain (PSG) na Faransa da Real Madrid na Sifen da kuma wasan  Atletico Madrid na Sifen da Jubentus na Italiya.

Kulob din Real Madrid na Sifen ne ya fi yawan lashe kofin inda ya dauka sau 13 sai Liberpool ke biye da kofuna 6 sai FC Barcelona mai kofuna 5 da sauransu.

Gasar tana gudana ne duk shekara a tsakanin watannin Satumba zuwa  Mayu.