Talauci a cikin wadata

Wasu za su yi mamakin hada talauci da wadata a waje daya, amma duk wanda ya yi nazarin kasar nan da ake kira Najeriya zai ga haka ya yi daidai da yadda kasar ke tafiya! A mafi yawan kasashen duniya kasa na kara arziki, mutane na zama cikin wadata, koshi da walwala. Yayin da a […]

Talauci a cikin wadata
Talauci a cikin wadata

Wasu za su yi mamakin hada talauci da wadata a waje daya, amma duk wanda ya yi nazarin kasar nan da ake kira Najeriya zai ga haka ya yi daidai da yadda kasar ke tafiya! A mafi yawan kasashen duniya kasa na kara arziki, mutane na zama cikin wadata, koshi da walwala. Yayin da a Najeriya samun man fetur da komawa kan tafarkin dimokuradiyya da irin ribar da aka samu maimakon a more sai ake fama da bakar wahala.
Duk da arzikin albarkatun kasa da Allah ya yi wa kasar nan, ga kasa da ma’adanai, inda za ku iske Najeriya tana da arzikin da ko Amurka ba ta isa ta ce ba ruwanta da kasar ba, akwai man fetur da albarakatun a kwance a ko’ina cikin kasar. Hakan ya sa masana da dama ke tambaya shin matsalar kasala ko ragwanci ce, ko kuma tsinuwa ce ta Ubangiji da ya jarrabe kasar da azzaluman shugabanni da malamai kidahumai, domin ita ce ta shida a arzikin man fetur, amma ‘yan kasar na fama da wahalar da ko kasar da bata da ma’adani daya ba su fuskanta!
Sannan ga mutane, komai ya daidaita a shirin sarrafawa. Ga masana, masu ilimi, masu karfi, ‘yan kwallo, dalibai da sauran karikicen! Amma duk a banza an gaza fito da kasar daga kangi, musamman domin a halin da ake ciki a yanzu babu na tsakiya, sai dai kana fama da tsananin talauci ko kai attajiri ne, a fili yake cewa tazara tsakanin mai shi
da maras shi ta yi yawa.
Masana na ganin kamar an jarrabe kasar da rashin shugabanni na gari, wanda shi ne musabbabin duk fitinun da kasar ke fama. Hakan ya kara nuna matsala game da harkokin siyasa a kasar, inda an gaza samun ingantaccen zabe, an gaza yaki da cin hanci da rashawa ko a jam’iyyun adawa, su ma so suke su samu, su tatsa!
Ba a bada kwangiloli, balle talakawa su yi kwadago, magina, masu fenti, sayar da katako, siminti, masu abinci da fiyawata su sami ciniki, ba don ma ana zafi ba! Ko wadanda suka sami kwangiloli sai ka iske babu kudin aiwatarwa, kuma sai an aiwatar ga masu karfi kafin masu karamin karfi su samu.
Wata babbar matsala ita ce ta lalace watau dogaro da wani, tare da yin ha’inci wajen aiwatar da aiki don ka samu wani abu daga ciki, yanzu halin ya fara damun kowa ta yadda wanda ya karbi kwangila zai yi kwange, masu aiki zasu yi, masu sayar da kayan aikin ma sun kawo masu arha maras inganci don su kara samun riba, hohoho wayyo kasata Najeriya!
Duk da haka sai ka iske ana bada bayanan karya game a takarda ko a kasafi game da irin ci gaban da ake samu a tattalin arzikin Najeriya, bayan a zahiri talauci na karuwa. Ko akwai masu jin dadi kalilan ne, domin kafin ka sami mutumin da ya sami ci gaba sai ka iske sai ka gamu da mutane da suka rasa aiki ko jari ko wadanda ma basu ma fara aikin ba!
Wasu kasashe suna fama da fatara don basu da arziki, amma mu ana cikin talauci duk da wadatar da Allah ya albarkace mu! Wai a haka ma tallafin za a janye! Albashi ba ya isa sai an hada da bashi! Ya za a yi da kasar da ke da kyaun noma an gaza noman!
Ko attajirai kan yi fama da fatara, idan suna gidajensu, yayin da suka fita kasashen waje sai su ji dadin dukiyarsu su mori wadatar da Allah ya masu, amma sai ka iske suna maneji a kasarsu. Bugu da kari ko damar saye da kunna janareto duk ba dadi bane, kara, guba da sayen mai sun iske kowa, duk kudinsa!
A halin da ake ciki a Najeriya a yanzu babu matsakaita, daga wanda yake cikin wadata, sai wadanda suke cikin tsananin talauci. A fili yake cewa tazara tsakanin mai shi da maras shit a yi yawa. Yayin da duk kudin talaka na tafiya a kan abinci, kudin hayar gida ko shago, sufuri, neman ilimi, kayan gwanjo da samun shiri.
A daya bangaren attajirai kan yi amfani da komai na kasashen waje, kuma ko a bangaren da ake gani yana samun ci gaba watau bangarorin man fetur da wayoyin sadarwa su kansu kan dogara da kayan kasashen ketare. Musamman don a cikin gida masana’antu sun dakushe, ko abincin da za a ci sai an shigo da shi daga Birazil, kayan da za a sa sai an shigo
dasu, motoci da baburan ma haka, a irin tsarin da babu ayyukan yi ga matasa, kuma babu gasa ga masana’antu, kuma ana kara haihuwa, a haka ana kara kaimin rashin aikin yi da talauci.
Babban bakin cikin shi ne yadda a cikin shekaru hamsin Caina ta fita daga kangi da mulkin mallakar masarautu, mutanen Sin sun tashi haikan har sun zama na biyu a wajen ci gaba da bunkasar tattalin arziki a duniya, kuma haka ya zo da more abbaben jin dadin rayuwa da wadata ga talakawan Caina, kuma mun ki daukar darasi.
Wai yanzu ba kasar da ake kwatanta ta da Najeriya sai Nijar da Mali da Habasha da Kongo da Gabon da Sudan da Togo da kasashen da suka gaza su Somaliya da Iraki da Afganistan. Har an yi binciken da ya tabbatar da cewa sama da rabin ‘yan Najeriya na fama da tsananin talauci ta yadda suke rayuwa a kasa da Dala daya ta Amurka a rana daya! Mu dai mu yi fatan damina mai albarka.

Buhari Daure
Muryar Talaka
+2347035986444
[email protected]

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna