Talauci A Najeriya: kalubalenku shugabanni
Malam Isma’il Sani Yabo Sakkwato, ya yi nazari mai tsawo game da yanayin zamantakewar rayuwa a Najeriya. Ya dora babban laifi a kan shugabanni, yadda suke kara fadada tazara tsakaninsu da wadanda suke mulka, musamman ta fuskar rayuwa. Ga abin da nazarin nasa ya haifar: Babu wata kasa a duniya da ta tara mutane nakasassu, […]
Malam Isma’il Sani Yabo Sakkwato, ya yi nazari mai tsawo game da yanayin zamantakewar rayuwa a Najeriya. Ya dora babban laifi a kan shugabanni, yadda suke kara fadada tazara tsakaninsu da wadanda suke mulka, musamman ta fuskar rayuwa. Ga abin da nazarin nasa ya haifar:
Babu wata kasa a duniya da ta tara mutane nakasassu, marasa galihu da rashin kulawa kamar wannan kasa ta Najeriya mai tsananinn gaba da talaka. Babu wata gajiya da aka kebe don nakasassu ko marasa galihu da take iya wadatar da su a wannan kasa. Da yawa za ka ji an ce an fitar da wani shiri don taimaka wa nakasassu da marasa galihu, ana iya fadar haka har a gidan rediyo. Kai za ka ci gaba da jira, ba za ka sake jin duriyar maganar ba. In ko har an sami wata jaha ko karamar hukuma ta gabatar, za ka ga abin bai taka kara ya karya ba kuma ba dukkansu ne za su samu ba.
Wani abin ban haushi da al’ajabi shi ne, maganar hana bara da koyaushe ake kai ba tare da la’akari da abin da ya kamata a maida hankali a kansa ba, in an kula da yanayi da halin kaka-ni-kayi na talauci da rashin tsaron da wannan kasa take ciki. Arzikin talakan Najeriya kodayaushe kasa yake yi, in dan kasuwa ne ko manomi; domin babu tallafin gwamnati a kan talaka in shi ba dan siyasa ba ne. In ka ji ana kuwwar takin zamani, kai za ka zata abin kirki ne sai an ba ka sa’annan za ka shaida da maganata. Tallafin takin na nufin su wa aka dama da su a fafutukar siyasa? Su ne za su raba wannan gajiya. Shi manomi bai da labarin kalar miyar da ake sha, kabewa ce ko kuka? Yana dai iya tuna ranar da dan takara ya yi hawaye a karkararsu, har ya yi alkawarin bayar da isasshen takin zamani.
Tsiyar wutar lantarki kawai aka bar mu da ita, ba mu san ina ne za mu sanya kawunammu ba. Muna rayuwa ne cikin kunci da tagayyara kuma ba mu da magani, wane talaka ne zai ce ya more wa wadatacciyar wutar lantarki da kasar nan ke samarwa? Yau fiye da shekara 20 muna jiran sai gobe, an kusa kammalawa nan da wata mai kamawa ko a ce karshen shekara ko watan daya na sabuwar shekara. Wane irin rashin tausayi ne da iya jajircewa da son kai, haba! Me ya sa wai shuwagabanninmu su ba sa iya kwanciya cikin duhu da zafi da sauro? Me ya sa ba sa tuna cewa mu ma ’yan Adam ne, muna jin dadi da ciwo, muna son lafiyarmu da rayuwarmu? Me ya sa kuka manta da rantsuwar da kuka yi na muradin inganta rayuwarmu? Ba haka muka yi alkawari da ku ba, ashe ba mu kuke kishi ba, kanku da ’ya’yanku ne kawai abin da kuka sanya a gaba, yayin da kuka yi amfani da kudademmu kuka sayi manyan injina, domin ku wadata da iska, sanyi da kuma hasken korar duhu da karatun jarida, kuka ware wani injin a gefe don ko aka yi in dayan ya sami matsala, a koma ga dayan.
Kun tsani wahala ko kadan ba ku so, kukan garzaya kasashen ketare don duba lafiyarku. In da a nan ne aka tsare wa ma’aikatan lafiya hakkokansu, aka ba su tarbiya tagari da horarwa don gano ciwo da daukar matakin kai tsaye, kuka bar mu ba kudi ba magani a asibiti, ba kayan aiki a asibiti ba kulawa. Wani sai marar lafiya zai zo likita ya ce bai gane ciwon ba saboda hoton ya yi dushi-dushi. Ko a asibitin ma babu tsayayyar wutar lantarki. Ana warin magani zuruta da kazantar rashin shara, ga dan karen zafi. Dole a yi wa majinyaci fifita, domin wadanda kuka tanada don wannan aikin ba su dace da mu ba, don kusan kyamarmu suke.
Kuna ji kuna gani kodayaushe muna asarar rayukanmu kan lalatattun tituna da kuka ce za ku gyara, har ranar farawa kuka sanya. Me ya sa ku ba ku bi ta wadannan hanyoyi? Kun fi gane wa hanyoyin sama. barayi fa na yawan kashe mu a hanya, domin wadannan ’yan sandan kuka girke a kan hanya kun sani aikin ya fi karfinsu kuma akwai tazara tsaninsu da wadannan dogayen hanyoyi da suka yi sunan mazaunar barayi. Yawan ’yan sandan ya yi kadan, kwarewarsu ma ba ta kammala ba. Ba su da kayan aiki na zamani, domin ba ku ba su ba.
Hanyoyin sadarwar sun toshe, domin babu tanadin cika alkawarin da aka yi wa aikin dan sanda don wadata shi da alkawarin nauyin daukar iyalinsa, in har rayuwa ta yi aikinta (mutuwa). Ya zama dole dan sanda na mutuwa iyalinsa na fara tarbon bala’in kora daga gidan haya, kuma ni na san a can ketare inda kuke zuwa kuna ganin ’yan sanda, wadanda suka amsa sunan ’yan sanda, kuna ganin yadda adalan shuwabanni suka sada soyayya tsakanin ’yan sanda da mutanen gari.
Akwai jituwa ta kud-da-kud tsakanin ’yan sanda da al’ummar gari a wasu kasashe, domin shi fa dan sanda aikinsa kare rayuwa da dukiyar al’umma hade da muradin kare kasarsa daga kowace irin kazanta, rashin tarbiya, ciwo da dai sauransu.
Ita kuma kasarsa ta girmama tare da karramawa ga dan sanda don kauce wa tusgowar baraka, abar kyama. Aikin dan sanda yana da ka’idodin dauka, dole mutun ya kasance mai kirki da da’a da juriya da jarumtaka da kishin kasa. Anya sai da kuka yi wannan diddiga sannan kuka dauki wadannan yan lauka-lauka.
Ban taba ganin inda ba a jin kunya ba kamar Najeriya. Na taba shiga wata unguwa a yanar gizo. inda na ci karo da ’yan sandan duniya, suna takama da aikinsu, sun ci kwalliya sun yi shirin ko-ta-kwana abin gwanin burgewa da sha’awa, amma da na zo ga dan sandan Najeriya sai na hadu da shi tsugunne yana kashi. Da na kara gaba sai na hadu da wasu suna fada. Na sake dagawa sai na riski wasu na wasoson kudi, ban bar sashen ba har sai da na ci karo da wanda ya yi barci gindin itaciya da bindiga a hannunsa, wannan ai abin kunya ne!
Me ya sa shuwagabanni suka fi kishin ’ya’yansu kan namu? Akwai mamaki da kuka yanke tarayyar ’ya’yanku da na talakawa, akwai hadari gaba in yaran suka tashi, kun haddasa kiyayya tsakaninsu. Makarantar yaranku daban ta yaranmu daban. Wannan ba dan karamin zalunci ba ne, kun san makarantun gwamnati ga dai su ga yadda suke. Matattara ce ta kadangarru da ’yan sayar da kwalama a filin wasan kwallo ne da zukar tabar wiwi. Malaman firamare abin tausayi ne, da wane albashi malam zai ciyar da yara hudu da mata biyu, ya biya wutar lantarki da ruwa? Kuma in ya ki siyasarka ko albashin ba ya samu. Wannan ya yi daidai da karin maganar malam Bahaushe da ya ce; a buge ka a hana ka kuka!