Talauci a tsakanin talakawa

Ba wanda ya san talauci sai wanda talauci ya kama! Ta yaya wanda yake samun abinci sau uku a rana zai kirayi kansa talaka? Amma da za ka wuni nema, ka kare da kudin kwano daya rak za ka gane me ake nufi da babu, ka san mene ne talauci! Wani lokaci akan iske mutum […]

Talauci a tsakanin talakawa
Talauci a tsakanin talakawa

Ba wanda ya san talauci sai wanda talauci ya kama! Ta yaya wanda yake samun abinci sau uku a rana zai kirayi kansa talaka? Amma da za ka wuni nema, ka kare da kudin kwano daya rak za ka gane me ake nufi da babu, ka san mene ne talauci!

Wani lokaci akan iske mutum na da aikin yi, amma yana fama da talauci, saboda da wasu dalilai, kamar rashin darajar kudi ko yau da gobe su matse ribar da dan kasuwa ke samu!

Talauci da yunwa ’yan uwa ne, daya ba ya rayuwa sai da daya! Yunwa ita ce ma’aunin talauci na farko. Yanzu wadansu yara na fama da talauci saboda maraici, sai sun yi talla kafin su sayi abinci, sai sun debo ruwa kafin zuwa makaranta, wani lokacin haka za su je makaranta cikin yunwa, dauda da damuwa!

Haka jahilci yana da alaka da talauci, shi ya sa mafi yawan talakawa za a iske ba su da ilimin addini ko na zamani, kuma kusan a zaune suke ba sana’a. Haka suke zama babu dabarar amfani da karfin da Ubangiji Ya ba su wajen tabuka wani abu. Har wadansu kan yi tunanin ko sun yi Sallah ba a karba, saboda talaucinsu da karancin fahimtar addini.

Akwai bambanci tsakanin ’ya’yan talakawa da na masu abin hannu, shi ya sa za mu ga koshin ba daya ba ne, talaka ba ya samun kayan abinci masu gina jiki, sai ka iske ko wajen haihuwa masu abin kan haihu cikin sauki, yayin da matar talaka kan yi faman numfashi kafin dan ya fito, saboda karancin jini da yanayi.

Matsaloli kan fara tun kafin haihuwa, saboda ita kanta uwar ba ta koshi ba. Yara ba nauyi tun a haihuwa, a zo a yaye da da wuri, babu abincin kirki ga rashin tsabta. Lokacin kuruciya babu bitamin!

Su kuma wadansu maza kan je teburin mai shayi su kashe kwai su ci tsire a kasuwanni, amma gida bai wuce masara ba.

Wata matar ma takan rasa kayan da za ta sa sai tsumma, ko gamin bauta, zane daban, riga da dan kwali daban, ba kwalliya, ba takalma, ba bargon rufa.

Wadansu talakawan kan kwana a waje, ga iska kuma ruwan sama yana yi musu duka, babu kudin biyan gidan haya, ko daki daya wani ba ya iya kamawa, dole ya koma kasar gada ko cikin tasha ko masallaci ko rumfar kasuwa ko karkashin bishiya ya kwanta! Ba maganar gado ko katifa ko tabarmar ake ba, wannan sai masu rabo, a dai samu a kwantar da hakarkari.

Masu dukiya kan mayar da talaka matsiyaci, ba wanda yake saurarensa, ba ruwan kowa da ra’ayinsa, ana kallonsa a matsayin wanda ya gaza a rayuwa, wanda bai zo da sa’a ba, ba ya da wayo, wawa, jahili. Duk wadannan dalilan kan sa talakawa su kaurace wa mutanen kirki.

Ba kudin tura yara makaranta, ko a makarantun kyauta, yaran kan gaza saboda ba su iya tsayar da tunaninsu a waje daya saboda yau! Tunanin yaran da talauci ya addaba kamar duwatsu ne, ta yadda malami ba zai iya shuka komai a kansu ba. Karatu ko zuwa makaranta ba nasu ba ne, sai garari a sarari inda ake harbin iska.

Wahala  da zafi da sanyi, shan ruwa marar kyau da cin abincin da ba dadi, cuttutuka da sauro su ne abubuwan da talaka yake fama da su. Shi ya sa kasashen da ke fama da talauci sun fi fuskantar karancin rayuwa, yayin da masu ci gaba suka fi dadewa ana rayuwa cikin jin dadi! Idan ba ka da lafiya ga asibiti, ga likitoci ga magani, a nan gida ko ka je inda ake kira asibitin, likitoci sun bace, ba ka ganin maganin, ya gudu!

Ba inda mutum zai ga talauci a bayane sai a kauyuka ko karkara, inda kowa ke neman abin da zai ci, musamman da bazara. Mabukata da masu neman a agaza musu sun yi yawa, a kan haka ake matsa wa ’yan uwa da abokai su taimaka. Da an ga bako, an ga nama! Saboda haka wadansu kan yi kaura daga kauye su tare a birni.

Duk da halin da ake fama a kauyuka, a birane akwai daidaiku da suka yi kudi cikin lokaci kankane, sun yi kazamin kudi, musamman  a shekarun nan na dimokuradiyya.

Sau da yawa masu kudi kan samu kudi ta hanyoyi da talakwa ba su bi kuma ko sun je tashar ba a daukarsu, ba sukuni! Wato kamar a tsoma mutum a asusun gwamnati don nasaba ko wata alfarma ta musamman. Sai mutum ya samu jari ko a samu daloli a sama, haka filayen gwamnati da sauran abubuwan more rayuwa, a ba shi tun a sahun gaba.

Yayin da mu a nan talaka bai fi karfin ci da sha ba, ko wutar lantarki da wurin kwana, ko a makarantu akwai bambanci, haka a abin hawa da ruwan da suke sha, wadansu su sha na leda wadansu na kwalba ko na roba, wadansu na rafi ko na randa wadansu ruwa mai launin kasa suke sha.

Mutane nawa suke iya biyan kudin wutar lantarki? Kudin makaranta, na asibiti ko kudin haya da kansu, ba tare da sun nemi taimako ko tallafi daga ‘yan uwa ko kungiyoyin taimakon marayu da gajiyayyu ba? Duk da haka da kyar ake kokarin biyan ma’aikaci karin albashi, kai wai ma’aikatan nawa ne da ake wannan dambarwar?

Tabbas ta hanyar aiki da karatun addini da na zamani za a iya rage tazarar d ake tsakanin attajirai da talakawa. Wani abin takaici game da ilimi a kasar nan shi ne ko mutum ya gama jami’a sai ka iske ba ya iya kare abin da ya karanta, kuma ba ya iya komai sai jiran aikin gwamnati. Ba sana’a, ba horo kan dogaro da kai duk da bautar kasa da ake cewa ta ba shi wannan horon.

Kai ko wadanda ake cewa an ba su horo, ya kamata a fito da tsarin ba su jari su kafa kansu, a taimaka musu a gwamnatance. Ta yadda matasa za su tsayu da kafafuwansu, kadan ya fi ba dadi. Amma a halin yanzu ba wadanda ake cuta sai matasa ’ya’yan talakawa an bar su a wulakance, sai an zo zabe a nemo su, da an ci a yi watsi da su.

A farfado da tsarin raya karkara, ta yadda duk abin da za ka nema a birni akwai shi a kanannan hukumomi, amma a yau ko jarida, banki, man salak, kake nema sai ka shigo birni. Kuma a kai kamfanoni kauyuka, inda za a kafa kananan masana’antu.

A sa ido don kore dabi’ar yin kudi dare-daya, ta hanyar kyautata wa wadanda suka yi abin kirki. Ta yadda sarki zai gayyace su ya yaba a ba su sarautu tare da karrama su a fada don kwazonsu. Sabanin yadda muke gani a yau ana ta karrama mabarnata, wadanda ba a san asalin dukiyoyinsu ba, wadanda ba su taimakon al’umma.

Wannan kusan daya ne da yaki da cin hanci da rashawa kada a tsaya ana kama barayin awaki bayan ga manyan barayi na nan suna shan iskar ’yanci. Idan mutane suka samu kulawa da karin albashi tare da sadaka da zakka ga wadanda suka fi cancanta, hakan zai toshe kafar kwadayi da zari da rage talauci.

Su ma talakawa suna cuta, tun suna kananan sukan yi cuta don su rayu su kimshe, ko su kai kudin talla gida, haka direbobi, masu haya, ’yan garuwa da sauransu. Ko yara kan boye canji. Wannan wayo ne amma kuma mafarin cuta da zari ke nan. Talauci gida-gida ne, akwai talauci a kowane gida a nan kasar.

’Ya’yan talakawa su ke fadawa hadarin karuwanci da zinace-zinace a unguwanni, saboda talauci ake daukarsu a yi luwadi da madigo da su. Kafin ka ce kwabo masu tallar gyada, tura ruwa, fura da nono da masu sai da rake tare da yara almajirai su ma sun yada wannan annoba a kauyuka da karkara.

’Ya’yan attajirai na fadawa irin wadannan hadura amma bisa nishadi! Sai ku ga tsoho ya mayar da kansa dan daudu, yana shafa hoda, ba ya barin gemu ga kyashin ’yan uwa wai shi dan birni.

Arziki daraja daraja ne, amma mafi darajar arziki shi ne attajirai su fitar da talakawa daga talauci.

Talakawa su ne suke zama iyayen yaran da ake haifa don a sayar kamar yadda muke gani a Kudu, inda ake samun mata a tara a gida a yi musu ciki don su haihu a sayar da jariran!

Ana haka ne duk don a tsira, a tsere daga kasar ta kowane hali don hawa tudun mun tsira.

’Yan siyasa na amfani da ’ya’yan talakawa wajen bangar siyasa, shi ya sa ba za ku taba ganin ’ya’yan gwamnoni ko matansu suna jagaliya ba. Amma sai ka iske mata sun raba dare suna jiran honorabul ya dawo.

Ya kamata gwamnati ta tashi tsaye, ta yi da gaske wajen yaki da talauci domin yaran da suke fama da talauci wat ’ya’yan talakawa kan kamu da hawan jini olsa da sauransu, kuma su suka fi yiwuwar zama ’yan ta’adda da su addabi al’umma.

A yi kan-da-garke a yi wa tufkar hanci ta yadda za a haifi yara masu ladabi da biyayya. A bude makarantu a sa kujeru a samar da ajujuwa, sannan a ba tarbiyya muhimmanci a wajen daukar darrusa.

Akwai talauci, kuma mutane da dama na fama da wannan fitinar! Idan ba a yi da gaske ba mayunwata na karuwa wadanda za su iya zama barazana, domin idan yunwa ta bugi mutum, yakan fita daga hayyacinsa ya rumgumi zaki, ko su kifar da kasar ita kanta.

Ya kamata masu kudi su bar hantarar talakawa, domin ba wanda ya dora wa kansa talauci. Su kansu talakawa su yi mu’amala mai kyau tsakaninsu da masu kudi ko sarakuna da ’yan kasuwa da girmamawa tare da mutunta juna, tabbas daga cikin talakawa ake samun shugabanni, ’yan siyasa da attajirai!

Saboda haka ina kira ga ’yan uwana talakawa mu dawo mu bi Allah mu tsira, idan ba mu samu ba a nan, mu samu a can. Ubangiji Ya daukaka wadansunmu a kan wadansu, amma karshe wato makoma ita ke nuna wanda ya yi nasara. Sau da yawa dukiya ta zama sharri, kuma a kan yi dacen talaka da halaye masu nagarta, hakuri da hikimomi wadanda za su kai shi ga Aljanna.

Buhari Daure

Yana zaune ne a Kofar Kaura, Katsina za a iya samunsa ta imel: [email protected]