Talauci ba uzurin da zai hana karatu ba ne a gwamnatin Tinubu — Ministar Ilimi

Ministar ta bayyana hakan ne yayin ziyarar duba ayyukan shirin AGILE a wasu makarantun ’yan mata da ke Kano.

Talauci ba uzurin da zai hana karatu ba ne a gwamnatin Tinubu — Ministar Ilimi

Tinubu

Ƙaramar Ministar Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmad ta ce a ƙarƙashin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, talauci bai kamata ya hana kowane yaro zuwa makaranta ba.

Ta ce, shirye-shiryen gwamnati irin su: Hukumar Bayar da Bashin Karatu ta Najeriya NELFUND, da ke ba ɗaliban manyan makarantu rance, sun taimaka wajen cire matsalar rashin kuɗi a matsayin cikas wajen neman ilimi.

Ministar ta bayyana hakan ne yayin ziyarar duba ayyukan shirin AGILE a wasu makarantun ’yan mata da ke Kano.

A cewarta, banda biyan kuɗin makaranta, ɗalibai na samun tallafin yau da kullum domin sayan abinci, sufuri da kayan karatu.

Ta kuma ce, gwamnati ta samar da shirye-shiryen koyon sana’o’i ta intanet kyauta, tare da bayar da alawus da kayan fara sana’a ga matasa.

A yayin ziyarar, ta umarci shugabannin makarantu da su gyara kura-kuran da aka gani a azuzuwa, xakunan gwaje-gwaje da wuraren tsafta cikin makonni uku.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ilimi na Kano, Ali Haruna Makoda, ya ce jihar ta ware Naira biliyan 24 domin gina sababbin makarantu 49 da kuma gyaran wasu 300 a faɗin jihar.