Talauci da kafirci suna da zumunta

Hausawa suna cewa ‘ko da magani wuya ba dadi, ‘ Manzon Allah (SAW) shi ma ya roki Allah Ya kare shi daga talauci da kafirci, wanda ya nuna cewa lallai akwai alaka a tsakanin talauci da kafirci. Sanin kowa na cewa yanzu talauci ya yi wa mutane katutu ta yadda har ta kai ga wadansu […]

Talauci da kafirci suna da zumunta

Hausawa suna cewa ‘ko da magani wuya ba dadi, ‘ Manzon Allah (SAW) shi ma ya roki Allah Ya kare shi daga talauci da kafirci, wanda ya nuna cewa lallai akwai alaka a tsakanin talauci da kafirci.

Sanin kowa na cewa yanzu talauci ya yi wa mutane katutu ta yadda har ta kai ga wadansu musulmi suna rasa imaninsu saboda tsananin talauci da suka fada, wadansu kuma sun kasa daurewa sun rikide sun zama ‘yan ta’adda.

A Najeriya ta yau babu inda talauci ya samu gindin zama kamar yankin arewacin kasar nan inda a kullum talakawa sai karuwa suke yi maimakon raguwa.

Hakan yana faruwa ne saboda kyashi da hassada da rashin tausayi na al’ummar yankin, domin da dama daga cikin mutanen yankin ba su so su ga dan uwansu ya ci gaba, sun fi so su rika ganin ‘yan uwansu suna tafiya cikin tsumma, ba su iya dinka riga sai dai idan su ne suka cire na jikinsu suka ba su.

Idan mutum ya himmatu wajen neman na kansa, maimakon a taimaka masa sai a taru a karya shi, ko da kuwa yana kokari wajen taimaka wa ‘yan uwansa da sauran jama’a.

Shugabanni kuma da ya kamata su tallafa wa talakawa babu ruwansu, hasali ma dai su ne kan gaba wajen karya talakawan nasu, saboda ba su son su yi karfi har su zama barazana a gare su. Sun ware makarantun ‘ya’yansu daban, asibitocinsu daban, unguwanninsu daban, abincinsu daban, su a wurinsu isa ne su rika cin farfesun kaza talakawa kuma suna roron kasusuwan da suka zubar suna tsotso.

A halin yanzu talauci ya karu saboda rashin aiki, wadansu shugabannin kuma maimakon su taimaka a samu aikin sai ma korar wadanda suke yin aikin suke yi. Mutane masu kokarin da suka rungumi sana’a suna samun rufin asiri an kore su daga wuraren da suke zaune, an rusa masu rumfuna an shuka fulawoyi a wurin, kuma ba a nuna masu wani wurin da za su koma ba.

Irin wannan mawuyacin halin da ake tura mutane ne yake sanyawa aikata miyagun ayyuka suke karuwa, domin idan tsanani ya yi yawa mutumin kirki ya kan zama mutumin banza.

Da dama daga cikin Fulanin da aka kama suna garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa cewa suke yi sun fara da satar shanu ne saboda an sace dabbobinsu suka koma ba su da komi, daga satar shanu ne suka koma yin garkuwa da mutane, wanda suka ga ya fi satar shanu sauki da kuma saurin samun kudi.

Idan aka bari mutumin kirki ya fara aikata mugun aiki, idan ya ji dadi hana shi zai zama abu ne mai wahalar gaske, domin raba mutumin da yake samun miliyoyin kudi cikin lokaci kankane ya koma ya zauna kafin ya samu Naira guda sai idanunsa sun yi ja zai yi wahala, domin ba kowa ne zai iya hakura ya ci gaba da zama a cikin wannan halin ba.

Saboda haka takura wa mutane da ake yi ta hanyar karya su da sunan gyara kasa ko gyara gari ba zai haifar da alheri ba, matsala kawai hakan zai haifar ga kasa, domin zai kara yawan masu zaman kashe wando ne kawai, kuma matukar aka samu karuwa marasa aikin yi to babu zaman lafiya, domin dole ne su nemi abin da za su ci.

Saboda haka don Allah shugabannin Arewa ku rika taimaka wa ‘yan uwanku domin su tsaya da kafafunsu, ba dabara ba ce fito da hanyoyin takura wa mutane da ake yi a halin yanzu, domin matakan da ake dauka a halin yanzu sun fi cutar da yankin Arewa fiye da ko’ina a kasar nan.

Shugabannin sauran sassan kasar nan idan sun samu dama kokari suke yi su rage talakawan da ke yankunansu, su kuma kara karfafa attajiransu. Ba cewa aka yi shugabannin Arewa su kawar da kansu daga sauran yankunan kasar nan su mayar da hankalinsu ga yankin Arewa kadai ba, a’a so ake yi su tabbatar da karuwar arziki a yankin Arewa maimakon gurgunta tattalin arzikin yankin. Yadda idan sun sauka daga mulki za a rika alfahari da su saboda sun gina mutane da yawa, arziki ya karu, jama’a da yawa suna walwala, kuma an rage masu tagumi da yawa.

Kamata ya yi kafin hukuma ta dauki wani mataki mai zafi da zai kuntata wa jama’a, ta fara samar da matakin da zai rage masu radadin da za su ji tukun. Ko a asibiti yanzu idan za a yi wa majinyaci aiki ana fara yi masa allurar kashe zafi ne kafin a yi aikin domin ya samu saukin radadi. Haka ya kamata hukumomi su rika yi, ba su rika kawar da kansu daga mawuyacin halin da mutane za su fada saboda matakin da za a dauka ba.

Karuwar talauci a kasa fitina ce, domin talauci ba bata tarbiya kawai yake yi ba, har kafirci yake tura mutane a ciki. Kamar yadda ake samun rahotannin da ke nuna cewa ana amfani da kudi ana kafirtar da mutane a wadansu yankuna na Arewa.

Allah Ya sanya shugabanni su rika daurewa suna tausaya wa talakawansu, maimakon su rika fifita kawata gari suna tauye talakawansu domin su burge wadansu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos