Talauci da rashin tsaro na damun ’yan Najeriya

Yanzu da zabe yake dada karatowa ’yan siyasa za su ci gaba da fito da dabaru iri-iri domin ganin su samu goyon bayan jama’a. Jam’iyyaradawa ta APC wadda ta samu sakamakon yadda Jam’iyyar PDP take neman kai kasar nan ga halaka ta tashi haikan wajen nuna gazawar jam’iyya mai mulki, kuma jiki magayi ko da […]

Talauci da rashin tsaro na damun ’yan Najeriya
Talauci da rashin tsaro na damun ’yan Najeriya

Yanzu da zabe yake dada karatowa ’yan siyasa za su ci gaba da fito da dabaru iri-iri domin ganin su samu goyon bayan jama’a. Jam’iyyaradawa ta APC wadda ta samu sakamakon yadda Jam’iyyar PDP take neman kai kasar nan ga halaka ta tashi haikan wajen nuna gazawar jam’iyya mai mulki, kuma jiki magayi ko da wani bai fada man aba jikin mu yana ga ya mana cewa al’amura sun kai magaryar tukewa wajen tabarbarewa da lalacewa. Babu tsaro ga kuma talaucin tsiya sun dabaibaye mu a kasar nan ta yadda muna rayuwa ne kamar a gandun dabbobi. Galibin mutane ba su san inda suka fito ba, ba su san ina za su je ba, kowa ka gani hankalinsa ba a jikinsa yake ba. Mutane na neman wani maceci da zai kwato su daga wannan bakar jaraba, wato PDP wadda Allah Ya ara mata daman a tsawon shekara 16, amma ta kasa yin amfani da wannan dama wajen inganta makomar kasar nan da muka yi fafata don ganin sojoji sun bar gadon mulki don ba jama’a damar kafa gwamnatocin da suka zaba da kansu.

To, amma yadda al’amura suka kazance a lokacin mulkin farar hula na PDP, musamman a zamanin Shugaba Jonathan abin akwai ban tsoro, domin mun kai wani mataki da kowanen mu yake fita daga gida ba tare da tunanin zai iya komawa gidansa da rai ba.
Duk wadannan abubuwa sun biyo bayan rashin hadin kan mutanen kirki ne, don su hadu su ceto kasar nan, inda suka bar wasu tsarari, mugaye suka hadu suka maida arzikin kasar mallakarsu da sunan mulki da wakilci. Yanayin ya kai matsayin da babu wata jam’iyyar siyasa ko wani zabe da zai canza halin da ake ciki, matukar galibin jama’a ba su gyara halinsu sun tsarkake imaninsu tsakani da Allah ba.
Duk jam’iyyun sun haddasa rigingimu a tsakanin mabiyansu, musamman ’yan takara, abin da ya jefa masu zabe suka shiga rudu, har suke zabar duk wanda zai ba su kudin da ba su taka kara sun karya ba, ko da ba su san shi ba, ko da ba su gamsu da akidarsa ba.
Duk wasu mashahuran barayi da suke zuwa da kudi suna ta raba wa ga shugabannin jam’iyyu da jami’an tsaro da sarakuna da malaman addinin domin a ce su ne suka ci zabe, ya kamata jama’a su rika nuna musu kyama. Ban yarda ma da masu cewa idan barayi n siyasa suka kawo muku kudi kukarba amma ku ki zabensu, a’a duk wanda ya kawo maka kudi don yana son ka zabe shi, ka gaya masa a idonsa cewa ba za ka karba ba. Ka gaya masa cewa ka gaji da bakin mulkinsu na zalunci da sata da zubar da jinin jama’a. Ka shaida masa a kan idonsa cewa za ka gwammace ka mutu da talauci domin ’ya’yanka da jikokinka su samu ’yanci daga bakin mulkin da ke sakaci da tsaron rayuka da dukiyar jama’a. Ka shaida masa gwanda talauci ya kasheka ’ya’yanka su samu damar da za su yi karatu su samu aikin yi da ka karbi kudinsa da zai tabbatar da kai a cikin talauci.
Akwai wajibcin mu fara fitowa muna nuna wa ’yan siyasa da masu mulki zababbu da nadaddu cewa, dukiyarsu ta haram da suka tara ta handama da cuta da karya, ba ita muke bukata ba, muna bukatar a kare mana rai da dukiya da addini da mutunci fiye da Naira ko Dalar da suke dofar amana.
Yanzu dai kowa ya ga yadda rashin tsaro ya kai mu, kowa ya ga yadda talauci ya kai mu, shin za mu yi wani yunkurin amayar da kasar nan kan turban a kwarai mu bude sabon babi na samar da adalci a tsakanin al’ummar Najeriya, ko za mu ci gaba da sayar da ’yanci da martabar mu da ta ’ya’yanmu, saboda kawai wani kansila mafarin cuta yana ba mu Naira 500-500, ko saboda wani danmajalisar jiha bi-ta zaizan gwamna yana ba mu turmin atamfa ko Naira 2000-2000, ko shugaban karamar hukuma, tsumma makunshin cuta yana ba mu ragon suna idan matan mu suka haihu, kodan majalisar tarayya da Sanatan da suka zuwa lokaci-lokaci suna gina mana burtsatse ko lambatu a unguwannin mu ko gwamna uban rub-da-ciki da yake gina mana rumfar kasuwa ko ajin makaranta ba kwararrun malamai ko asibitin sha-ka-tafi ba likitoci?
Yanzu na yi Imani galibin mutanenArewa, ba ma na jihohinArewa maso Gabas kadai ba, zaman lafiya da kwanciyar hankali suke nema ba ma batun wani aiki ba, don haka tilas ne talakawa su fahimci cewa lokacin sayar da ’yancin su saboda Naira dubu zuwa dubu 10 ya wuce. Lokacin da za su bari miyagu su ci gaba da mulkarsu, suna bari a zubar da jininsu da lalata dukiyarsu don kawai sa ran za su samu wani mata’i ya wuce. Wajibi ne talakawa su hada kansu, su fito kwansu da kwarkwatarsu, su zabi shugabanni nagari masu adalci, kuma su ne milallai a ba su abin da suka zaba. Tilas talakawan Najeriya su yunkuro kamar yadda talakawan Masar suka yi, tilas talakwan Najeriya su yunkuro kamar yadda talakwan Burkina Faso suka yi, tilas talakawan Najeriya su yi yunkuri kamar yadda talakwan Kwaddibu wasu ka yi.
Muna bukata shugabanni ne da za su tsare rayuwarmu da dukiyar mu kafin komai. Muna bukatar shugabannin da za su inganta noma da kiwo, ba wadanda za su mayar da hankalin su wajen samun Kason kudin mai su sace ba. Muna bukatar shugabannin da za su mayar da kududdufan Jihar Kano kadai wajen samar da adadin kifin da ake bukata a duk Najeriya, ta hanyar maida su wuaren kiwon kifi na zamani maimakon cike su da ake yi da shara a dora gini a kai har da benaye. Ga madatsun ruwa da ake da su har 27 a Jihar Kano kadai, wadanda sun isa a yi noman rani da zai ci da Najeriya idan aka yi kyakkyawan amfani da su a zamanance, sannan su ma za su taimaka wajen kiwon kifin. Kuma za a iya amfani da su wajen samar da wutar lantarki, musamman idan aka hada da dimbin shara da aka bari take cutar da al’umma a yanzu.
Gwamnoni da daidaikun mutane suna ta la’antar wadanda suka sa yi masana’antu suka rufe, amma ba sa tunani a kan ina man ’yan kamfanoni irinsu UAC da John Holt da GBO da PZ da CFAO da UTC da GALS da CHALK da KINGSWAY da LEbENTIS da makamantansu, ko’ina Nigeria Airways da jiragen ta na sama da Nigeria Railways da jiragenta na kasa? Ina NEPA da NITEL da KTL da UNTL da Arewa Tedtile da makamantansu? Me yasa mu noman gyada da auduga? Me yake kassara kiwo? Me ya kasha jima da rini da kira suka mutu kurmus! Su kuma laifin wane ne? Amma an samu gwamnonin da suka sa ci biliyoyin Naira da Dala, suka gina gidaje a manyan biranen kasar nan da kasashen waje, ba su iya gina ko kamfanin da zai inganta wadannan sana’o’i ba?
Allah Yana taimakon duk wadanda suka yunkura wajen taimaka wa kansu ne. Idan Allah ya saukar da ruwa, ya rage ga masu shuka su je su yi. Ikonsa ne Ya fito musu da abin da suka shuka, har su girba.
AbdulkarimDaiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
08060116666, 08173106666, 08023106666.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi