Talauci da Rashin Tsaro: Tinubu ya ayyana dokar ta-baci
Tinubu ya amince cewa matsalar tsaro da talauci mai yaduwa suna daga cikin manyan ƙalubale ga ci gaban ƙasa
Yunwa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a kan talauci da matsalar tsaro, yana mai bayyana su a matsayin bukatun gaggawa ta ƙasa.
Tinubu ya kuma yi gargadin cewa wadannan matsaloli na ci gaba da barazana ga jin daɗin ma’aikata, ƙarfinsu da kuma bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
A jawabinsa yayin bikin Ranar Ma’aikata ta 2026 a Abuja, Tinubu ya ce ba za a iya samun aiki nagari ba a inda jama’a ke rayuwa cikin tsoro, kuma albashi ba ya iya ciyar da iyali ba.
Jawabin nasa ya yi daidai da taken Ranar Ma’aikata ta Duniya da ya ta’allaka kan shirin Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO) na Kudurin Aiki na Mutunci, wato “Decent Work Agenda.”
- Mun fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga kangin talauci —Tinubu
- APC ta shiga rikici kan tikitin takarar kai-tsaye
Shugaban Ƙasa, wanda ya wamu wakilcin Sakataran Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya amince cewa matsalar tsaro da talauci mai yaduwa suna daga cikin manyan ƙalubale ga ci gaban ƙasa.
Sai dai ya tabbatar wa ma’aikata cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai na musamman da kuma na dogon lokaci don shawo kan matsalolin.
A cewarsa, “Ba za a iya samun aiki nagari ba idan ma’aikata na rayuwa cikin tsoro, albashi bai iya ciyar da iyali ba, ko kuma rashin ya hana zuwa gonaki, masana’antu da kasuwanni,” in ji shi.
Tinubu ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirye-shirye da dama a ƙarƙashin Renewed Hope Agenda, ciki har da shirin Rundunonin Tsaron Al’umma, wand ya riga ya ɗauki matasa 45,000 don ƙarfafa tsaron al’umma tare da samar da ayyukan yi.