‘Talauci da tsadar rayuwa za su kashe armashin Babbar Sallah’

Ya ce ana samun rago mafi karancin kudi a Kasuwar Alaba Rago a kan Naira dubu 40.

‘Talauci da tsadar rayuwa za su kashe armashin Babbar Sallah’

Dubun dubatar raguna a kasuwar dabbobi a Kano

A ranar Laraba mai zuwa ce za a yi Babbar Sallar bana, inda masu hali daga cikin Musulmi suke yanka dabbbin Layya da sauran hidindimu.

Aminiya ta zagaya domin ganin yadda farashin dabbobin Layya da sauran kayan masarufi da kuma yanayin tafiye-tafiye suke.

Wakilanmu sun gano cewa farashin dabbobi ya ninka na bara a fadin Najeriya, wanda bai rasa nasaba da tashin farashin man fetur da karyewar darajar Naira saboda tashin farashin litar mai daga Naira 195 zuwa Naira 540 ko fiye da haka ya jawo karuwar kudin sufuri.

Masu shigo da dabbobin daga kasashe makwabta kuma na fama da karayar darajar Naira wacce ta jawo ake sayar da Dala a Naira 750 ko sama a kasuwar canji.

A Birnin Tarayya, Abuja, wakilin Aminiya da ya kewaya kasuwannin dabbobi a Abuja ya tarar a Kasuwar Jabi farashin rago ya fara ne daga Naira 180,000 zuwa 700,000.

A Karar Kubwa, farashin rago ya kama daga Naira 60,000 zuwa Naira 320,000.

A Jihar Kano Sallar ta zo da sauye-sauye da dama kama daga kan yadda ake gudanar da cinikin dabbobi da kuma yadda ake hada-hadar kayan Sallah da kayayyakin abinci.

A zantawarmu da yawa daga cikin masu sayar da dabbobin sun ce yanayin cinikin dabbobin ya ragu sosai idan aka kwatanta da bara.

“A bana abubuwa sun sauya matuka. Hakan ya faru ne sakamkon faduwar daarajar Naira da kuma janye tallafin man fetur da aka yi.

“Yanzu idan muka je sayo dabbobi a kasashen kusa da mu muna sayowa da tsada sakamakon faduwar darajar Naira.

“Haka muna fama da tsadar kudin dauko dabbobi zuwa kasuwanninmu. Hakan ya sa dole mu kara kudi.

“Mutane babu kudi a hannunsu a bana, shi ya sa ba a zuwa saya sosai. Ga tsada ga kuma rashin kudi a hannun mutane,” wani mai sayar da dabbobi, Nayaya a Kofar Na’isa ya bayyana wa wakilinmu.

A bangaren mazauna garin wasu sun bayyana cewa a bana ba lallai ne su yi Layya ba, yayin da wasu kuma suka ce za su bari sai sun ga yadda ta kaya kafin Sallah.

Abdul’aziz Ibrahim, magidanci mai ’ya’ya 4 da mace daya, ya ce a bara kamar haka tuni ya sayi ragon Layya.

“Amma a bana ina jira in ga yaya za ta kaya. Babu kudi kuma dabbobin sun yi tsada. Mutane da dama da suke yanka shanu yanzu za su hakura su yanka rago wasu ma ba za su yi ba gaba daya.

“Ni ma zan je kasuwar kauye idan na samu mai sauki sai in saya,” in ji shi.

A daya bangaren iyaye na ta shirye-shirye don gudanar da shagulgulan Sallar.

Baya ga tanadin Layya, akwai shiryeshirye da dama ciki har da tanadin girkegirken abincin Sallah, wanda hakan ya sa kasuwancin kayan abinci ke karuwa.

Wani magidanci, Shu’aibu Muhammad Haruna ya bayyana wa wakilinmu cewa duk da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, yanzu haka ya mallaki ragon Layya da kayayyakin girki don gudanar da bikin Sallar.

Ya kara da cewa kasancewar ba kasafai ake yin dinki a Babbar Sallah ba, akan yi sayayyar takalma da gyale da ’yan kunne na yara da sauransu.

Ita ma wata uwar marayu biyu, Ramatu Garba cewa ta yi suna jiran a yi albashi ne.

“Yawanci a irin wannan lokaci mu ma’aikata muna samun kalubale saboda rashin yin albashi. Ga shi Sallah ta zo kuma kusa da karshen wata, amma dole mu kalli jama’a suna ta hada-hada,” in ji ta.

Sai dai a lokacin da muka zagaya kasuwannin da suke sayar da kayyakin abinci da kayan sawa mun tarar al’amura sun fara bunkasa, inda mutane suka fara sayayyar kayan suyan nama da sauransu.

Wani mai sayar da kasko da murhu a Kasuwar Sabon Gari da ke Kano, Abdulkadir Musa ya ce a yanzu haka yakan iya sayar da kasko 10 zuwa 15 a rana, yayin da a baya da wuya ya sayar da biyar.

Wani mai sayar da kayan kanshi da sinadaran miya, Mukhtar Aliyu ya ce “A duk shekara a irin wannan lokaci muna ciniki sosai.

“Musamman a wannan Sallar domin kuwa ana sayan sinadaran miya da sauran kayan kanshi na soya nama da kuma abincin Sallah. Sai dai har yanzu cinkin bai kankama ba.”

Akwai karancin hada-hada a Sallar bana — ’Yan Kasuwar Legas

A Jihar Legas, Kasuwar Alaba ce tushen kasuwar kananan dabobbi, a cewar Alhaji Husaini Muhammad Lajawa, Kasuwar Alaba Rago ta haifar da kasuwannin raguna da dama a Legas da Ogun da suka hada da Kasuwar Isheri da ke Karar Basi a Jihar Ogun, wacce ita ke tashe a yanzu a kasuwancin ragunan Layya.

Husaini Lajawa ya ce a bana raguna ba su yi tsada ba musamman a Arewa inda ake sayo su, duba da matsalar sauya kudi na tsohuwar gwamnatin Buhari, wacce ta tilasta wa masu kiwon dabbobin suka yi ta sayar da dabobbin araha.

Ya ce ana samun rago mafi karancin kudi a Kasuwar Alaba Rago a kan Naira dubu 40, yayin da babban rago ke kaiwa Naira dubu 250 zuwa 400, sai kuma matsakaici a kan Naira dubu 120 zuwa dubu 200.

Aminiya ta zagaya Kasuwar Kayan Abinci ta Mil 12 inda ’yan kasuwar suke kukan rashin ciniki, lamarin da suka alakanta da tsadar kayan lura da yanayin damina da ake ciki da kuma uwa uba janye tallafin mai na Gwamnatin Tarayya.

A bangaren tafiye-tafiye zuwa Arewa domin Sallah kuwa, Aminiya ta zaga wasu daga cikin tashoshin mota da ake jigilar jama’a daga jihohin Legas da Ogun, kuma a nan ma direbobi da ’yan kwamasho sun koka da karancin matafiya.

Muhammad Fayama Jarimi, shi ne Shugaban ’Yan Kwamasho na Tashar Isheri da ke daura da Karar Basi a Jihar Ogun, ya ce duk da tsadar man fetur farashin mota daga Legas zuwa Kano bai kai yadda aka dauka a lokacin Sallar bara ba, amma babu fasinjoji.

“Ka ga a baya a irin wannan lokaci motoci sun fara karanci saboda yawan fasinjoji masu tafiya Arewa, amma a yanzu babu haka, ka ga tun bayan karin kudin man fetur Naira dubu 15 muke dauka zuwa Kano a motocinmu na bas, homa amma a Sallar bara duk da babu tsadar mai Naira dubu 15 muka dauka a irin wannan lokaci saboda yawan fasinja, a yanzu kudin mota bai karu ba saboda rashin fasinja,” in ji shi.

A Jihar Kaduna, Aminiya ta gano cewa farashin dabbobin sun fara ne daga Naira dubu 36 zuwa dubu 300 a Kasuwar Dabbobi ta Zango da ke Tudun Wada, Kaduna.

A cewar daya daga cikin masu sayar da dabbobin, Haruna Allah Ya-Amfana iya kudin mutum iya shagalinsa.

Ya ce dabbobin sun yi tsada ne saboda tallafin man fetur da aka cire wanda hakan ya sa kudin motar da ake dauko dabbobin zuwa kasuwa ya karu.

Malam Bala wanda ya ce surukinsa ya samu ragon Naira dubu 36, ya ce babu laifi yana da dan girma duk da cewa ba a Kasuwar Zango ya saya ba.

Ita kuwa Malama Halima cewa ta yi saboda tsadar dabobbi musamman rago a bana tana ganin da akuya za ta yi Layya.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji