Talauci ne ya sa na kashe dana -Titilayo

Wata matashiya  ’yar shekara 20 mai suna Titilayo Odedele ta fada wa kotun gargajiya da ke unguwar Ebute Meta a Legas cewa tsananin talauci ne ya sa ta kashe danta mai shekara biyu mai suna Opeyemi.Lamarin  ya auke ne a unguwar Ajagunro da ke yankin Ikorodu a Legas a watan jiya na Nuwamba.Titilayo, wacce ’yan […]

Talauci ne ya sa na kashe dana -Titilayo

Titilayo OdedeleWata matashiya  ’yar shekara 20 mai suna Titilayo Odedele ta fada wa kotun gargajiya da ke unguwar Ebute Meta a Legas cewa tsananin talauci ne ya sa ta kashe danta mai shekara biyu mai suna Opeyemi.
Lamarin  ya auke ne a unguwar Ajagunro da ke yankin Ikorodu a Legas a watan jiya na Nuwamba.
Titilayo, wacce ’yan sanda suka gurfanar a gaban kotu kan zargin aikata laifin kisa, ta ce ba za ta  iya ci gaba da daukar dawainiyar yaron ba, bayan da mahaifanta suka kore ta daga gida sakamakon cikin shege da ta yi.  “Makarantar firamare kawai na kammala, ban je sakandare ba kafin na samu ciki.  Wata ranar Juma’a na je wani coci da niyyar yada yaron cikin dare, amma sai na kasa. Bayan na bar harabar cocin da safiyar ranar Asabar, sai na lullube yaron da zani na sanya hannu a wuyansa na shake shi har sai da ya mutu. Ba komai ne ya sa na kashe shi ba, sai tsananin talaucin da ya addabe ni. Ba ni da aikin yi, dakyar nake samun abinci. Sau da yawa sai na yi bara nake samun kudin da zan ci abinci, balanatana abincin da zan ba yarona ko kuma kudin da zan saya masa sutura”. Inji ta
Dubun Titilayo ya cika a ranar da ta kashe yaron, yayin da ta rasa yadda za ta yi da gawarsa sakamakon tsoro ya kama ta, lamarin da ya sa nan da nan mutane suka gano abin da ta aikata suka mika ta ga ’yan sanda, inda ta amsa laifinta yayin da suke yi mata tambayoyi.
Takardar karar da ’yan sanda suka shigar kotu ta nuna cewa abin da Titilayo ta yi ya saba wa sashe na 221 na kundin dokokin Jihar Legas na shekarar 2011’.
Alkalin kotu, O. O. Olatunji ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Titilayo a gidan wakafi har zuwa lokacin da sashen da ke nazari kan hukuncin manyan laifuka zai ba da shawara a kan ta, kuma ta dage shari’ar sai ranar 3 ga watan Fabrairun badi.