Talauci ya sa dalibi karatu da lantarkin hanya
Kyamarar sa ido ta CCTB ta dauki hoton wani matashi dan shekara 12 daga birnin Moche, a kasar Peru, inda yake nazarin karatun da aka yi masa a makaranta, ya zauna a gefan hanyar da ake wucewa yana amfani da hasken fitilun hanya, saboda iyayen sa ba suda halin biyan kudin wutar lantarki a gidan […]
Kyamarar sa ido ta CCTB ta dauki hoton wani matashi dan shekara 12 daga birnin Moche, a kasar Peru, inda yake nazarin karatun da aka yi masa a makaranta, ya zauna a gefan hanyar da ake wucewa yana amfani da hasken fitilun hanya, saboda iyayen sa ba suda halin biyan kudin wutar lantarki a gidan su. ‘Yan sandan garin ne su ka yi ta fallasa wannan hoton wanda hakan yasa miliyoyin jama`a suka yi ta bayar da martani a kafafen shafukan sadarwa na zamani.
Wani ma’aikaci a tsangayar `yan sandan Moche, ya ce da farko ya gano wani matashi mai suna Bíctor Martín Angulo Córdoba a watan da ya gabata, lokacin da yake duba kyamarorin tsaro, sai ya gano wani yaro matashi zaune a kusa da wata fitila hanya da daddare wanda da farko ya yi zargin ko mai laifi ne.
Sai da suka fadada bincike suka gano cew, yaron yana zaune yana rubutu da karatu a litattafan sa, yana amfani da hasken fitilun wanda suke taimaka masa ne kawai.
Hakan yasa jami’an `yan sandan suka ga hazakarsa a fannin nazari, daga nan suka wallafa a shafin su na Facebook, mabiya shafin suka yi ta yada hotunan hakan yasa ya yi fice ga mabiya shafin.
A lokacin da ake hada rahoton wannan matashin sama da mutum miliyan 5 ne suka bude bidiyon su na yabawa da hazakar yaron a duk duniya.
Wata kafar sadarwa ta garin ta nemo yaron da mahaifiyarsa, inda suka tambayi mene ne dalilin da yasa yaro yake karatu a bakin hanya da daddare a maimakon ya yi a gida.
Binciken kafar sadarwa da suka gudanar ya nuna, iyayen yaron dan shekara 12 talakawa ne ba suda halin biyan kudin wutar lantarki a gida. Idan dare ya yi su na kunna wutar kandir ne kawai don su ga haske
A duk lokacin da rana ta fadi sai Bíctor Martín ya yi kokarin kammala wasu karatun da zai yi ta amfani da wutar lantarkin hanya a maimakon ya yi amfani da wutar kandir.
A tattaunawar da kafar sadarwa ta Panamericana TB ta yi da mahaifiyar matashin Rosa Angulo Córdoba ta ce, “ Wani lokaci da na, ya taba fada min cewa, idan ya ci gaba da amfani da hasken kandir ba zai iya samun kwarin gwiwa a fannin karatun sa ba, don haka na yanke shawarar in fita wajen gidan mu in kammala karatu na.
Rosa Angulo Córdoba, ta ce a kullum Bictor yana fita kiwo da awakin gidan, kuma ya dauki karatunsa da muhimmanci don haka yake samun nasara da kyakkyawan sakamako a makaranta.
Bayan labarin Bíctor Martín ya gama garin sai shugaban karamar hukumar Moche ya ziyarci gidan su Bictor, ya kara wa yaron kwarin gwiwa a fannin karatunsa kuma ya yi wa iyayen Bictor alkawarin zai rika biya masu kudin wutar lantarki a maimakon ya rika fita da daddare yana karatu da hasken fitilun hanya.
Bíctor Martín, ya ce burinsa shi ne, bayan kammala karatun sa ya zama jami’in dan sanda don ya kawo karshen cin hanci da rashawa.
Gidan su Bíctor Martín Angulo Córdoba na daya daga cikin, kashi 5 cikin 100 wadanda ba su iya biyan kudin wutar lantarki.