‘Talauci ya sa na sayar da dana’

Wani magidanci, Kanayo Awurumi, dan shekara 29 da ya shiga hannu kan zargin sayar da dansa mai suna Samuel Kanayo, dan kimanin shekaru biyu da haihuwa da ke unguwar Egbe a yankin Ikotun a Jihar Legas ya ce talauci ne ya sa ya sayar da dansa. Magidancin, wanda yake sana’ar fenti, ya bayyana wa manema […]

‘Talauci ya sa na sayar da dana’
‘Talauci ya sa na sayar da dana’

Wani magidanci, Kanayo Awurumi, dan shekara 29 da ya shiga hannu kan zargin sayar da dansa mai suna Samuel Kanayo, dan kimanin shekaru biyu da haihuwa da ke unguwar Egbe a yankin Ikotun a Jihar Legas ya ce talauci ne ya sa ya sayar da dansa.

Magidancin, wanda yake sana’ar fenti, ya bayyana wa manema labarai cewa wani abokinsa mai suna Emmanuel shi ya ba shi shawarar ya sayar da dansa don ya samu kudin da zai biya bukatunsa.
“Ni dai sana’ar fenti nake yi a lokacin ina zaune da iyalina a garin Owerri da ke Jihar Imo kuma nakan yi sana’ar fim daga bisani sai abubuwa suka tabarbare mani ba na samun fenti kuma harkar fim din da nake yi ba na samun komai sai na yanke shawarar zuwa Legas don na nemi kudi. Da na zo sai abubuwa suka kara tabarbarewa ga shi kuma ina son na kama haya inda zan zauna da iyalina, sai wani abokina da ake kira Emmanuel ya ba ni shawarar cewa na sayar da dana don na samun kudin da nake bukata kuma shi abokin nawa ne ya hada ni da wata mai suna Obi da ta sayi yaron a kan Naira dubu 450.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Saboda haka sai na yi wa matata karya cewa matar da za ta sayi yaron ’yar uwata ce da za ta dauke shi ta ci gaba da rainonsa. Da kudin na biya kudin hayar gidan da muke ciki.”
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas sun kame Kanyo yayin da matarsa Kelechi ’yar shekara 28 ta fallasa al’amarin a lokacin da mijinta ya kasa cika alkawarinsa na dawo da yaron don ya ga iyayensa.
Daga bisani bayan da ’yan sanda suka tsananta bincike a kansa sai ya fada musu cewa ya sayar da yaron ga wata mata mai suna Obi a garin Fatakwal, inda ya jagorance su zuwa gidanta. Ita kuma ta kai su gidan matar da ta sayi dan daga wurinta mai suna Nwatu da ke zaune a garin Agbani da ke Jihar Inugu.
’Yan sanda sun kama sauran mutanen da ake zargi da hannu a sayar da yaron a garin Inugu amma sauran sun gudu. Sai dai Nwatu ’yar kimanin shekaru 42 da ke zaune a garin Agbani da ke jihar Inugu ta bayyana cewa ta sayi Samuel a kan kudi Naira dubu 650 don ya kasance danta.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas, Kenneth Nwosu ya bayyana cewa ’yan sanda na neman sauran mutanen da ke hannu a cikin al’amarin ruwa a jallo.