Taliban ta dakatar da yaki don bikin Salla
Kungiyar Taliban ta dakatar da kai hare-hare a kan sojojin Afghanistan domin hutun karamar Salla da ke farawa daga ranar Lahadi. Umurnin na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Taliban ta tsananta kai hare-hare kan dakarun gwamnatin kasar. Kungiyar ta umurci mayakanta su dakatar da bude wuta na kwana uku a fadin kasar domin […]
Kungiyar Taliban ta dakatar da kai hare-hare a kan sojojin Afghanistan domin hutun karamar Salla da ke farawa daga ranar Lahadi.
Umurnin na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Taliban ta tsananta kai hare-hare kan dakarun gwamnatin kasar.
Kungiyar ta umurci mayakanta su dakatar da bude wuta na kwana uku a fadin kasar domin bikin karamar sallah.
“Kar ku kai wa abokan gaba hari a ko’ina amma ku kare kanku idan aka kawo muku,” inji kakakin Taliban Zabihullah Mujahid a cikin wata sanarwa.
- Ranar Sallah: Kasashen Afirka da suka yi Idi kafin Saudiyya
- Dalilin da ya sa muka yi Idi ranar Asabar —Dahiru Bauchi
- Trump ya umurci a bude masallatai da coci-coci.
Shugaba Ashraf Ghani ya yi maraba da matakin, tare da alkawarin bin sharuddan tsagaita wutan na Eid Mubarak.
Shugaba Ashraf Ghani ya ce, “Na ba sojoji umarnin su kiyaye ka’idojin tsagaita bude wutan”, a shafinsa na Twitter.
Ana fatan matakin tsagaita kai hare-haren zai dore.
A baya kungiyar ta dakatar da kai hari llokacin bukukuwan salla, amma ba ta tsawaita wa’adin matakin nata.