Taliban ta sha alwashin mara wa IS baya
Reshen kungiyar Taliban da ke kasar Pakistan ya bayyana aniyyarsa na mara wa mayakan kungiyar Daular Musulunci ta IS baya da ke gwagwarmaya a kasashen Siriya da Iraki. A wata sanarwa da ta fitar lokacin bukukuwan Babbar Sallah, kungiyar ta yi kira ga masu kishin addini da su hada kai guri guda don yakar “makiya” […]
Reshen kungiyar Taliban da ke kasar Pakistan ya bayyana aniyyarsa na mara wa mayakan kungiyar Daular Musulunci ta IS baya da ke gwagwarmaya a kasashen Siriya da Iraki.
A wata sanarwa da ta fitar lokacin bukukuwan Babbar Sallah, kungiyar ta yi kira ga masu kishin addini da su hada kai guri guda don yakar “makiya” wanda sanarwar ta bayyana da hadakar Amurka da kawayenta.
kungiyar IS ta karbe iko da galibin yankuna a kasashen Siriya da Iraki, amma ta kwashe lokaci tana fafata wa da mayakan kungiyar al-kaeda. Reshen kungiyar Taliban da ke Pakistan ya fara gwagwarmaya da gwamnatin kasar ne an shekarar 1997.
Sanarwar ta ranar Sallah da mai magana da yawun shugaban kungiyar ya fitar, ta ce “Muna alfahari da farmakin da kungiyar IS take kaddamarwa akan makiyanmu, muna tare da su duk dadi, duk wuya.”
Ya kara da cewa: “A wannan mawuyacin halin, muna kira gareku da ku nuna juriya da hadin kai kamar yadda abokan gabar ku suka hada kai don yakar ku. Mu manta da duk wata rashin jituwa da ke tsakanin mu.” Har ila yau, sanarwar ta ce “al’ummar Musulmin duniya za su ba ku goyon baya a wannan mawuyacin halin kuma za su taimake ku.”
Sai dai wakilin kafar yada labarai ta BBC da ke birnin Islamabad ya ce ba wasu kwararan alamomi da ke nuni da cewa kungiyoyin biyu sun samu cin ma wata yarjejeniya a tsakaninsu, amma masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa an tsinkayi wasu mambobin kungiyar IS a yankin arewa-maso-yammacin birnin Peshawar da ke Pakistan, suna raba wasu takardu da ke yabo ga kungiyar IS.
Tun a cikin watan Yunin bana ne kungiyar IS ta zafafa kai hare-hare a Iraki, wannan ya sa Amurka da kawayenta suka fara kai farmaki ta sama ga kungiyar a farkon watan Agustan da ya wuce.