Tallafa wa ’yan kasuwa da jari zai sa farashin kaya ya yi kasa – Alhaji Altine

Aminiya: Ko akwai matsalolin da ‘yan kasuwar babbar kasuwar Sakkwato ke fama da su. Abubakar Altine: Akwai matsaloli da ‘yan kasuwar ke fama da su tun bayan sake bude kasuwar da gobara ta cinye a shekarun baya kasuwar ta kasa cika da mutane na baje hajojinsu a wajen kasuwa, an yi wa  masu sayar da […]

Tallafa wa ’yan kasuwa da jari zai sa farashin kaya ya yi kasa – Alhaji Altine

Aminiya: Ko akwai matsalolin da ‘yan kasuwar babbar kasuwar Sakkwato ke fama da su.

Abubakar Altine: Akwai matsaloli da ‘yan kasuwar ke fama da su tun bayan sake bude kasuwar da gobara ta cinye a shekarun baya kasuwar ta kasa cika da mutane na baje hajojinsu a wajen kasuwa, an yi wa  masu sayar da nama wata kasuwar, ga shi hukuma na bayar da shago ga wadanda ba ‘yan kasuwa ba. 

Sai ka samu a bakin shago wani ya yi kashi don an dade ba a bude shagon ba hakan ya sanya ‘yan kasuwa suka rika kama shagunan suka  mayar da su wurin ajiyar kayansu da yin kasuwanci yanayin tattalin arziki ya sanya wasu sun rufe shagunan, amma hukumar kasuwa ta ce sai mutum ya bude ko a karbe, a matakin kungiya mun shiga tsakani duk da muna samun takun saka da ma’aikatan na kasuwa mun yi tsaye muna son a yi mana lamuni duk wani dan kasuwa ya rika biyan kudin shagonsa don ba ya yiwuwa dan kasuwa ba wurin ajiye kaya a dukkan kasuwannin duniya, akwai ma’ajiya kan wannan muke son hadin kai a bar wa dan kasuwa shagonsa matukar an tabbatar da nasa ne yana biyan haraji, kuma daya ne daga cikin mambobin kungiyoyin ‘yan kasuwa 87 da muke da su, don gudun samun bara gurbi a kokarinmu na samar da zaman lafiya da tsaro da hadin kai tsakanin ‘yan kasuwarmu masu mabambantan addini da harshe don kowace kabila muna da a kasuwar nan.  

Aminiya: Kawar da ‘yan kasuwa a wurare daban-daban da suke kasuwanci da  gwamnati ta yi a birnin Sakkwato wacce matsaya kungiyarku ta yi?

Abubakar Altine: Duk abin da gwamnati za ta yi in ta kyautata kasuwanci tattalin arziki zai gyaru abin da muke so ga gwamnati duk wadanda ta tayar daga wurinsu to ta ba su wani wurin da za su sake kasa hajarsu don kasuwancinsu shi ne adalci. Yanzu zamani ne na kyautata birni akwai bukatar bunkasa kasuwanci tare suke tafiya a kula da taimaka mana in ka taimaki dan kasuwa guda kamar ka taimaki mutum 100,  muna goyon bayan gwamnati dari bisa dari kan haduwa da shawarwarinmu da take dauka kuma gwamna ya tabbatar mana a shirye yake ya taimaki ‘yan kasuwa kuma mun ga ya fara in da ya ba da tallafin gobara a kasuwar kara da tsohuwa da ta daji fiye da miliyan 160, ya gina wurin kashe gobara da na’urorin kashe wuta 1000, da alkawarin sabbin tashar mota da kasuwanni za a ba mu bashi marar ruwa abin da muke bukata fiye da komai don bunkasa kasuwancinmu in ka ba dan kasuwa dubu 100 a kalla mutum 20 su amfana tattallin arziki ya wadatu  lungu da sako, ga shi zai gyara masana’antun jihar nan abu ne mai kyau don a yanzu manyan masana’antunmu su ne kujeri da wurin yin ruwan leda(pure water) ka ga tallafi zai bunkasa masana’antun babu cigaba ka sayo bashi ka sayar bashi kudirin mai girma gwamna yana da kyau. Taimakon kananan ‘yan kasuwa ne zai tsayar da masana’anta in an yi tare da sani da shawarar ‘yan kasuwar rashin jari na cimana tuwo a kwarya ba mu son zama ‘yan kallo a harkar kasuwanci a Sakkwato in mutanen Sakkwato mun kai miliyan bakwai shida da rabi ‘yan kasuwa ne amma kashi 15 cikin 100 ke da jarin sana’o’insu 

Aminiya: Mutanen gari suna zargin kungiyoyin ‘yan kasuwa ne ke sanya kaya tsada da hauhawar farashi a jiha mi za ka ce kan wannan

Abubakar Altine: Ba gaskiya ba ne duk wanda ka ji yana fadin haka ba dan kasuwa ba ne bai san abin da ake cewa kasuwanci ba mu ‘yan kasuwa fasinjoji ne a cikin mota kamfanoni ne direba yadda suke so za su ja mu sauki ne ribar kasuwanci mai saye ya sayar baya kara ko rage farashi na masana’anta ne, wadatar kaya ke sanya sassaucinsu, da gwamnati za ta taimaka mana da jari da kaya sun fadi kasa, masu ganin ana boye kaya su sani shi dan kasuwa juyawa yake yi boye kaya  baya da riba a dai taimaka musu a gani don gidan kowa a Sakkwato akwai dan kasuwa.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna