Tallafa wa ’yan kasuwa zai bunkasa tattalin arziki – Abba Muhammad

  Sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Singa da ke birnin Kano Alhaji Abba  Muhammad Bello ya ce tallafa wa ‘yan kasuwa shi ne tushen ci gaban tattalin arzikin kasa ta fuskar cinikayya daga masana’antu  zuwa  kasuwanni  a kowace kasa ta duniya. Ya yi wannan tsokaci ne  a zantawarsu  da wakilinmu, inda ya ba da  misali  da […]

Tallafa wa ’yan kasuwa zai bunkasa tattalin arziki – Abba Muhammad

 

Sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Singa da ke birnin Kano Alhaji Abba  Muhammad Bello ya ce tallafa wa ‘yan kasuwa shi ne tushen ci gaban tattalin arzikin kasa ta fuskar cinikayya daga masana’antu  zuwa  kasuwanni  a kowace kasa ta duniya.

Ya yi wannan tsokaci ne  a zantawarsu  da wakilinmu, inda ya ba da  misali  da cewa a kasashen da suka bunkasa ta fannin tattalin arziki ‘yan kasuwa suna samun kulawar gwamnatocin su, musaMman wajen ba da tallafi ga ‘yan kasuwar,  kuma bisa la’akari da yanayin kasuwanci kowane dan kasuwa  da sana’arsa.

Sannan ya bayyana cewa  ‘yan kasuwa suna fuskantar iftila’i  iri daban-daban  walau na gobara ko fasa shaguna  ko dai wani abu na asara  kuma suna bukatar samun tallafi daga gwamnatoci da manyan ‘ya kasuwa kamar yadda ake gani a kasashen da suka ci gaba ta fuskar ciniki da masana’antu  domin su sake farfado da kasuwancin su.

Alhaji Abba Bello  yayi amfani da wannan dama wajen godewa gwamnatin Jihar Kano da shugaban rukunin kamfanonin dangote watau Alhaji Aliko dangote bisa kokarin da suka yi na kaddamar da asusun tallafawa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a kasuwanni  biyar  na jihar da suka yi asarar dukiyoyin su a lokuta daban-daban.

Sannan ya sake yin kira ga gwamatin jihar kano data kara yawan gudummawar data bayar duba da yadda jihar take a sahun farko na harkokin kasuwanci a fadin kasar nan tare da yin la’akari da yawan ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyin su sanadiyyar wadannan  jerin gobara da Allah ya saukar a kasuwannin su.

a karshe ya yi fatan cewa za’a sanya amintattun mutane cikin  kwamitin rarraba tallafin ta yadda kowane ‘dan kasuwa da ya yi asara kuma aka tantance shI zai samu tallafin da ya kamata, sannan ya yi godiya ga shugaba ‘yan kasuwar ta Singa, watau Alhaji Uba Zubairu Yakasai saboda  jagoranci na adalci da yake yi wa kasuwar tun lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaba.