Tallafi na masu hazaka ne

Editan Aminiya, ka ba ni dama in bayar da shawara ga hukumomin ilimi da kamfanoni da kungiyoyin da ke bayar da tallafin karatu ga dalibai. Lallai lokaci ya yi da za a rika bayar da kaso mai tsoka na tallafin karatu ga dalibai masu hazaka, don ta haka ne za a samu farfado da martabar […]

Tallafi na masu hazaka ne
Tallafi na masu hazaka ne

Editan Aminiya, ka ba ni dama in bayar da shawara ga hukumomin ilimi da kamfanoni da kungiyoyin da ke bayar da tallafin karatu ga dalibai. Lallai lokaci ya yi da za a rika bayar da kaso mai tsoka na tallafin karatu ga dalibai masu hazaka, don ta haka ne za a samu farfado da martabar ilimi a kasar nan. A yi kokarin cusa kishin kasa a zukatan dalibai, ta yadda za a samu mutanen da za su bayar da gagarumar gudunmuwa wajen bunkasa kasar nan. Yin haka ya zama dole, musamman ganin yadda ’ya’yan talakawa ba su cika samun tallafin ba, in kuma sun samu bai kai na ’ya’yan hamshakan attajirai ba. Sannan ’yan siyasa kan kiarkatar da akalar kason da gwamnati ke bayarwa ga al’umma, musamman guraben karatu a kasashen waje. Akwai bukatar a duba wannan matsalar, matukar ana son samar da kwararru a fannonin ilimi da dama, don ci gaban al’umma da raya kasa. Daga AbdurRahseed Shehu Kiluki, dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina.

Ga likitoci
Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da yajin aikin da likitoci ke yi a Najeriya. Hakika yajin aikin ba hanya ce mai bullewa ba, ganin yadda talakawa ke shan wahala, saboda ba kowane ke da kudin zuwa asibitun kudi ba. Ya kamata gwamnati da likitoci su zauna su sasanta, domin kawo karshen yajin aikin. Daga Muhammad Aminu Baka noma 08069735151.

Alkawuran ’yan siyasa
Edita ka ba ni dama in yi tsokaci, game da irin alkawurran da ‘yan siyasa ke yi wa Jama’ar su a wajen yakin neman zabe. Hakika ya kamata ‘yan Siyasa, susan irin alkawurran da suke yi wa jama’arsu, wadanda za su iya cika wa jama’ar su, idan har Allah yasa aka zabe su, domin Allah (S.W.T) ya ce: ku cika alkawari, don shi alkawari abin tambaya ne a wajen Allah. Ina jan hankalin talakawa da sauran Jama’a cewa: a wannan zaben da muke gab da shiga dama ce a gare mu na zabar shugabannin da za su Jagorance mu tsawon shekara hudu. ‘Yan Najeriya a yi amfani da wannan damar domin zaben shugabannin da suke ji za su iya kwatanta adalci da cika alkawurra idan aka zabe su. Gani ga wane dai, ya ishi wane tsoron Allah. Daga Aminu Dankaduna Amanawa. 09035522212.

bision Fm a Katsina.
Muna murna da samun tashar rediyon bision FM a Katsina. Domin tashar ta zo ne daidai lokacin da al’ummar Katsina ke bukatar ta. Da fatan ma’aikatan rediyon za su kara kaimi sosai, wajen samar da shirye-shirye masu ilimantarwa/da fadakarwa da nishadantarwa. Al’umma kuwa, tare da gwamnati da fatan za su bai wa wannan tashar rediyo cikakken goyon baya, domin ta dogara da kanta sosai.Ta hanyar samarwa tashar tallace-tallace da duk abin da ya dace, wanda zai tallafa wa tashar domin ci gaban jihar. Daga Haruna Muhammad Katsina, Shugaban kungiyar Muryar Jama’a 07039205659.

Ga Sardaunan Kano
Aminiya ina so ku ba ni dama in mika gaisuwata ga Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Gwmanan Gobe da yardar Allah, Malam Salihu Sagir Takai da duk masoyan annabi Muhammad (SAW). Daga Mariya Musa Fagge 08186897285.

Ga masoyan Najeriya
Masu kaunar Najeriya abin mamaki ne ace kuna son PDP. Allah Ya taimaki Buhari ya lashe zabe, ya kuma yi kokari wajen fitar da kasar nan daga kanin matsalolin da suka baibayeta. Amin summa amin. Daga Sulaiman SBK 07038999155.

Ga Hukumar zabe
Salamun alaikum. Aminiya ku mika min sakona ga Hukumar zabe, shin wadanda ba su da gari ko ’yan gudun hijira yaya rajistarsu take? Komawa za a yi ko sayarwa za a yi.kaddarallahu manyasha Allah. Daga Maisalati Beli 08064479195.

Ga Sakkwatawa
Aminiya an yada cewa iyalan marigayi Tsoho dan amale ba su yi wa tsohon Gwamnan Sakkwato, Baffarawa adalci ba. Mu dai ba mu san abin da ya sa ake yada wannan jita-jita ba. Daga Alhaji AbdulRa’uf Tsoho Amali 08060675303.

Ga Sanata Kabiru Gaya
Aminiya a isar min da sakon fatan alheri ga Sanata Kabiru Gaya. Ka yi mun gani. A lokacink muka smau wutar lantarki Abdu sani Rogo ya yi shugaban karamar hukuma na shekara 8, bayan wannan ya yi kwmaishinan kananan hukumomi, amma ba a yi wa Rogo aikin miliyan biyu ba. Daga Yakubu Abdullahi Fulatan Kano, karamar Hukumar Rogo. 08065192933.

Ga Tambuwal
Gaba dai, gaba dai, Allah Ya kare Aminu waziri Tambuwal, Ya karemu baki daya. Babanmu duk mako sai ya sayo mana Aminiya ranar Juma’a. Daga Masoyiyar Aminiya 08162209074.

Haba Sahabi Ya’u kaura?
Kamanta irin ruwan kuri’ar da aka yi maka a shinkafi da Badarawa da Birnin Magaji da zurmi amma tunda ka je Abuja ba ka yi wa yankin aikin komai ba, har yau idan kaura za ta kawoka to ta kawoka ? Don haka Badarawa kasan yadda aka yi da kai ? To babu komai muna nan jam’iyyarku ba za mu je ko ina ba. Domin koda kuka zo . Daga ASB Badarawa Shinkafi, Jihar Zamfara sai Mamuda. 08026629640

Ta’aziyya ga rediyo Gotel
Aminiya ku mika min ta’aziyya ga takwaranku na rediyo Gotel da ke adamawa, bisa rasuwar mahaifiyarsa, wato Yusif Modibbo Tukur. Daga Husaini Almusaya Gombe 08130446601.

Addu’a ga Buhari
Salam. Aminiya muna fatan alheri ga Shugaban kasar gobe. Talakawan Najeriya Allah Ya kawo muku mafita. Allah Ya taimaki Janar Muhammadu Buhari. Allah Ya fitar da shi kunya, ta yadda da zarar ya lashe zabe ’yan Najeriya su samu mafita daga kangi. Daga 09030366586.

A ci gaba da tsage gaskiya
Fatan alheri ga ma’aikatan Aminiya, Allah ya kara basira, a ci gaba da tsage gaskiya duk dacinta. Allah na tare da ku. Allah ya tsare ku da tsarewarsa Amin. Daga Muhammd Fagge.