Tallafin Aikin Hajji: A rushe NAHCON, ba ta da amfani —Gwamnan Neja
Gwamnan ya ce akwai buƙatar a rushe hukumar tare da mayar da al’amuran alhazai ga jihohi.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta jagoranci shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
Gwamnan ya bayyana haka ne ga manema labarai a Saudiyya, kan yadda aka gudanar da aikin Hajjin na bana.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 7 a wani sabon hari a Katsina
- Yadda dangantakar ɓangaren zartarwa da majalisa ta kasance daga 1999 zuwa 2024
Bago ya yi kira ga majalisar dokoki ta binciki NAHCON kan yadda ta kashe kuɗin tallafin aikin Hajji Naira biliyan 90 da Gwamnatin Tarayya ta bai wa hukumar.
Kazalika, ya ce a matsayinsa na gwamna zai buƙaci ƙungiyar gwamnoni ta yi kiran a rushe hukumar saboda ba ta da amfani.
Ya ce ya kamata shirya aikin Hajji ya koma ƙarƙashin ikon jihohi ba gwamnatin tarayya ba.
“Gwamnatin Tarayya ta girmi shirya aikin Hajji, wannan abu ne da ƙaramar hukuma za ta iya shiryawa, don haka ina kira a bar jihohi su riƙa shirya aikin Hajjin jihohinsu, kamar yadda wasu ƙasashe ke yi.”
“A ce kakakin majalisar wakilan Najeriya da wasu gwamnoni sun kasa samun wajen da za su kwanta a filin Minna wannan abun takaici ne.
“Wasu na cewa muna ƙorafi ne saboda abun ya shafe mu, haƙiƙa ya shafe mu saboda haka lokaci ya yi da za mu tashi mu yi kira a mayar da shirya aikin Hajji ƙarƙashin jihohi”, in ji gwamnan.
Gwamnan ya kuma koka kan yadda ya ce mahajjata sun biya kuɗi masu yawa amma suka kasa samun wadataccen kuɗin guzuri daga hukumar NAHCON.
“Ta yaya mutum zai biya Naira miliyan takwas amma ace dala 400 kawai za a ba shi? wannan abu ne da hankali ba zai ɗauka ba.”
Gwamna Bago ya ce da hukumomin jihohi ne ke ɗaukar nauyin shirye-shiryen aikin Hajji, da ba a fuskanci matsalolin da alhazai suka fuskanta a bana ba.
“Ya kamata a bar jihohi su riƙa tantance alhazansu, su san irin lalurorin da alhazan ke ɗauke da su, tare da irin magungunan da suke sha, domin sanin matakan da za su ɗauka na lura da waɗannan alhazan, amma babu wanda ya yi hakan, saboda NAHCON ce ke da alhakin gudanar da hakan,” in ji shi.
Ko da aka buƙaci shugaban hukumar NAHCON ya yi martani kan kalaman gwamna, ya ce baya buƙatar yin musayar yawu da gwamnan ma Neja kan wannan lamari.