Tallafin COVID-19: Cikin wadanda suka samu ya duri ruwa

Bankin NIRSAL ya ce dole sai wadanda suka ci sun biya, suka kuma sun ce ba su san bashi ba ne

Tallafin COVID-19: Cikin wadanda suka samu ya duri ruwa

Mataimaki na Musamman ga Manajan Daraktan Bankin NIRSAL, Dokta Muhammed Ghazzali

Lokacin da Gwamnatin Tarayya ta fara shirin nan na ba da tallafin da ake kira da tallafin Kwarona, mutane da yawa sun nemi tallafin ta hannun bankin nan na NIRSAL, wanda shi ne ke kula da ba da wannan tallafi.

Mutane da dama ne da suka ci gajiyar wannan tallafi, sai dai ga alama mafi yawan wadanda suka karbi tallafin sun dauka cewa sun ci bagas ne.

An kafa Bankin NIRSAL ne domin shiga tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN) da masu neman tallafin a matsayin bashi, kasancewar idan mutum yana neman bashi a bankunan ’yan kasuwa, sai ya kawo wanda zai tsaya masa ko kuma wata kadararsa.

Amma da aka kirkirar Bankin NIRSAL, sai ya kasance bankin ne zai dauki wannan nauyi na tsaya wa mai neman bashin.

Bankin ne zai karbo kudin daga Bankin CBN, sannan ya rarraba wa masu nema, kuma shi ne aka dora wa alhakin karbo kudin idan lokacin karbar ya yi.

A kwanakin baya bankin na NIRSAL ya fitar da wata sanarwa cewa duk wadanda suka amfana daga wannan tallafi, lokaci ya yi da za su fara biya, wanda hakan ya daga hankalin mutanen da a farko suke tunanin kudin kyauta ce, sun cinye kuma ba za su biya ba.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa daga cikin wadanda suka amfana da tallafin kalilan ne suka yi amfani da kudin wajen kasuwanci ko wata sana’a.

‘Ba mu san bashi ba ne’

Wata matsala da Aminiya ta gano dangane da wadansu daga cikin wadanda suka karbi tallafin ita ce sun dauka kyauta aka ba su kudin inda da dama suka bayyana cewa ba a shaida musu cewa bashi ba ne, saboda wadansu daga cikin ma’aikatan bankin suna karbar wani kaso daga cikin tallafin kafin su ba mutum.

A Jihar Kaduna Aminiya ta gano akwai matasan da suka samu kudin, amma maimakon su yi amfani da shi wajen sana’a ko sayen kadara, sai suka kashe kudin kawai.

Wani mai suna Abubakar da ya samu kudin ya bayyana wa Aminiya cewa da kudin ya biya kudin hayar gidan da yake zaune, sannan ya canja waya kudin suka kare.

“Wai kana nufin za mu mayar da kudin nan? Anya kuwa! Bari dai mu gani lokaci ya yi, amma da wahala mu mayar da kudin,” inji shi”

Da Aminiya ta tambaye shi ko ya san bashi ya ci, sai ya ce, “Na san bashi ne, amma sau nawa ake cin bashin gwamnati irin wannan da ake kira tallafi ba a biya ba? Mu tallafi aka yi mana lokacin kullen Kwarona. Sai ya zama dole zan biya kudin gaskiya.”

Abubakar ya bayyana cewa akwai wadanda ma suka samu kudin, suka shirya walima suka gayyaci abokai aka ci aka sha da kudin, sannan suka kashe sauran, inda ya ce wadansu daga cikinsu yanzu ma ko Naira dubu 10 ba su da shi.

Wata mata mai suna Ummi da Aminiya ta zanta da ita ta ce harkar karbar kudin ta jawo mata matsala a tsakaninta da dangin mijinta.

Ta ce tana zaune aka kira ta wai ta bayar da lambar asuunta na banki da kuma lambar BBN. Ta ce da farko ta yi shakkun bayarwa, amma sai ta daure ta bayar, bayan dogon lokaci ta ga an saka mata kudi a asusun bankinta.

Ta ce matsalar ta fara ne bayan samun wannan kudi da ba ta san shin bashi ne ko tallafi ba.

Dangin mijinta da su ne suka yi mata hanya, aka ce ta ba da na goro daga cikin kudin.

Matar ta ce ta so ta bayar amma da ta tuntubi yayanta wanda ma’aikacin banki ne, “Sai ya shaida min cewa kudin nan fa bashi ne, hakan ya sa na yi musu bayani amma sam suka ce ba haka ba ne, sun taimake ni, amma ni ina son yi musu halin duniya.

“Kai in takaita maka zance wannan lamari ya kai sai da muka rabu da mijina a kan haka amma da ya gano gaskiya ya zo ya ba da hakuri ga babana na koma.

“Kuma wallahi har yanzu suna ganin wai an cuce su, wa ya taba mayar da kudin da gwamnati ta bayar? To sai ga shi yanzu ana nema mu mayar da kudin,” inji ta.

Hakazalika ta ce ita inda Allah Ya taimake ta shi ne ta ba babanta kudin ya yi mata jari da su kuma haka aka yi, yanzu haka ana juyawa kuma sai godiya ga Allah.

“Kuma a shirye nake in mayar da kudin da aka ba ni, ka ga yanzu da na bayar da wancan Naira dubu 250 wa gari ya waya?”

Shi kuwa Malum Ba’a wani matashi dan gudun hijira da ya samu tallafin ya ce ya yi amfani da su wajen kiwon dabbobi yana sayarwa inda a yanzu ya kara wasu kudin don ya fara noma, kuma a shirye yake ya mayar da kudin sabanin wadansu abokansa da suka yi ta facaka da kudin.

Wani tela mai suna Madu ya ce ya samu wannan tallafin kudin kuma ya yi amfani da su wajen sayen shagon da yake dinki a cikinsa da kuma kara sayen kekunan dinki, amma ya ce yadda aka yi musu bayani, tallafi ne ba a fada musu ba cewa  bashi ba ne. Sai dai ya ce tunda an nemi su mayar dole su mayar.

Madu ya ce gaskiya suna gode wa wannan gwamnati ta Buhari don ta tallafa wa rayuwarsu, domin bai taba tsammanin zai samu har Naira dubu 450 ba, sai ga shi ya samu a matsayin tallafin kwarona, kuma ya ci moriyarsu sosai.

Bashi ne kuma dole a dawo da shi —NIRSAL

Da Aminiya ta tuntubi Bankin NIRSAL kan batun da yadda zai bi wajen dawo da kudin, Mataimaki na Musamman ga Manajan Daraktan Bankin NIRSAL, Dokta Muhammed Ghazzali ya ce, “Idan mun samu irin wannan dama, muna kokarin ganin mun wayar wa mutane kai cewa wannan bashin da aka bayar ba kyauta ba ce, su yi kokarin su biya don su taimaka wa kansu su taimaka wa ’yan uwansu don su ma su amfana, kuma su taimakwa kasa.

“Na biyu kuma mun yi kokari mun kirkiri wani abu a Intanet mai suna GSI wanda zai rika biya mutum bashi koda bai shirya ba, na san masu karatu za su yi mamaki, shafin na Intanet yana kokari ya gano duk inda kake da kudi ta hanyar BVN dinka a kowane banki zai kwaso kudaden ya biya maka bashi kana zaune ba tare da izinika ba. Don haka zai fi dacewa a matsayinka na dan kasa nagari ka biya ba tare da an kai ga wannan ba,” inji shi.

Ya ce “Kawai dai bashi da aka ba ka, taimaka maka aka yi, zan iya tunawa malamai da dama sun yi kira cewa idan aka ba mutum bashi taimaka masa aka yi, to kai ma da aka taimaka kamata ya yi ka biya ka ga ka taimaka wa kanka.”

Game da wadanda suka nemi bashin, amma ba su samu ba, sai ya ce, “Yawan mutane shi ne amsa, saboda mutum dubbai sun nemi wannan bashi kuma kudin ba su da yawan da kowane mutum zai samu, wanda Allah Ya sa zai samu to zai samu, duk wanda Allah Ya kaddara ba zai samu ba, duk yadda ka yi ba zai samu ba sai dai ya yi hakuri.”

Aminiya ta tambaye shi ko ana bin wata hanyar ko na ba da cin hanci a samu kudin? Sai ya ce, “Gaskiya ni a sanina babu.

“Hanya daya ta samun tallafain idan ka cika ka’idoji za ka samu, in ba ka cika ba kuma ba za ka samu ba. Idan bangaren ’yan ka-yi-na-yi ne wannan zan iya cewa ba za a rasa ba, kuma muna kokari mu dakile su, domin kawo karshen abin gaba daya.”

Za a iya kallon bidiyon tattaunawarmu kan dawo da bashin a shafukanmu na Aminiya: [email protected] da Aminiya Trust a manhajar YouTube.