Tallafin Gwamnatin Tarayya ne hangen Dala ne – Gwamnan Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya bayyana cewa tallafin kudi da ake cewa Gwamnatin Tarayya za ta ba jihohi don fitar da su daga kangi ba wani abu ba ne face hangen Dala ne.Gwamna Mohammed Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da ya ziyarci hedkwantan kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya […]
Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya bayyana cewa tallafin kudi da ake cewa Gwamnatin Tarayya za ta ba jihohi don fitar da su daga kangi ba wani abu ba ne face hangen Dala ne.
Gwamna Mohammed Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da ya ziyarci hedkwantan kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Abuja, inda ya ce har zuwa lokacin da yake magana bai samu wannan tallafai daga bankunan da aka ware ba.
“Tallafin yana neman zama hangen Dala , ba ina sukar Gwamnatin Tarayya ba ne, sun yi nufin alheri, suna da kyakkyawar niyya don ceto jihohin, amma sai suka fahimci su ma suna bukatar a cece su. Ba su da kudin da za su ceto jihohin.”
Gwamnan ya ce “Ni wakili ne a kwamitin mutum hudu da suka tattauna da Gwamnan Babban Bankin Najeriya bayan taron Majalisar Zartarwa ta kasa game da ceto jihohin. Don haka bayan dogon Turanci da gaza cika alkawuran, a karshe an nemi mu zabi bankuna, mun dauka za a tura kudin zuwa asusun bankunan amma a karshe sai Babban Bankin ya rubuta wa bankunan cewa su ba mu bashi mai sassauci a matsayin shirin ceto jihohin.”
Ya ce ya samu nasarar warware mafi yawan bashin albashin jiharsa ne da taimakon wasu ma’aikatan gwamnati. “Lokacin da na zo…su (ma’aikatan) sun zo sun same ni suka ce, ‘ranka ya dade mun boye wasu asusun ajiya daga gwamnatin da ta gabata saboda mung a suna facaka wajen kashe duk kudin da ya zo.’ Ta wannan hanya na ajiye kudi lokacin da na tafi taron rabon dukiyar kasa na farko ni kadai. Na ajiye wasu kudi daga ciki kuma a yanzu haka ina ci gaba da ajiye wasu ’yan kudin. Za ku ji mamaki a halin rashin da ake ciki amma ina ci gaba da ajiye wasu kudin, na bude wani asusu daban da inda gwamnati asusu gwamnati yake na ajiye wasu kudi. Ta wannan hanya ce na samu dama tara kudin albashin wata daya na biya kafin Sallah.”
Ya kara da cewa “Da aka yi haka sai aka samu babban sauki, kuma bayan haka ne muka sake zuwa rabon dukiyar kasa inda na dauki dukkan kudin na biya albashin wani wata. Sai kuma aka samu kudin iskar gas, ba tallafi ba ne. Kudin iskar gas kudi ne na asusun tarayya amma a baya Gwamnatin Tarayya take karkatar da su. Don haka da sabuwar gwamnati ta zo da suka samu bayani daga Kamfanin Mai na kasa (NNPC) cewa muna da Dala biliyan biyu da miliyan 100 da za a raba, sai aka raba nan ma na sake sadaukar dab kudin wajen biyan albashi. Za ku iya samun zarge-zarge cewa wasu jihohin sun yi amfani da kudin wajen sayen wasu abubuwa amma ni na yi amfani da daukacin kudin ne wajen biyan albashi.”
Idan za a iya tunawa kwanakin baya Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shirin tallafin ga jihohin da ma’aikata ke bin su bashin albashi da sauran hakkokinsu. Kuma fiye da rubu’in jihohi 36 na kasar nan ne ma’aikata ke bi bashin albashin da aka ce sun kai na Naira biliyan 110.
Jihohin da ma’aikata suka fi bin bashin albashin sun hada da Osun da Ribas da Oyo da Ekiti da Kwara da Kogi da Ondo da Filato da Benuwai da kuma Bauchi.