Tallafin kudi: ’Yan fim na jihar Legas sun koka

Jarumai da masu shirya fina-finan Hausa a Jihar Legas sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ba ta tuna da su ba yayin da ta raba tallafin kudi ga masana’antar fim ta Kannywood da ta Nollywood. Masu harkar fim da Aminiya ta tattauna da su a sassa da dama na Jihar Legas a ranar Litinin sun […]

Tallafin kudi: ’Yan fim na jihar Legas sun koka
Tallafin kudi: ’Yan fim na jihar Legas sun koka

Jarumai da masu shirya fina-finan Hausa a Jihar Legas sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ba ta tuna da su ba yayin da ta raba tallafin kudi ga masana’antar fim ta Kannywood da ta Nollywood.

Masu harkar fim da Aminiya ta tattauna da su a sassa da dama na Jihar Legas a ranar Litinin sun yi zargin cewa an yi musu rashin adalci.
daya daga cikin fitattun masu harkar fim a Jihar Legas, Hafizun Bege ya bayyana cewa “Gaskiya gwamnati ba ta yi mana adalci ba. Ya kamata a ce gwmanati ta tuna da mu, amma ba ta yi haka ba sai ta ba ’yan Kannywood da Nollywood. Gwamnati ta manta cewa duk wani dan fim idan ya zo kudu mu zai nema idan yana so harkokinsa su tafi daidai.”
Wani jarumi mai suna Ibrahim dankwalisa ya ce “Abin da gwamnatin tarraya ta yi mana ba ta kyauta ba. Muna yin harkar fim din nan, sannan rashin kudi shi ne babbar matsalarmu. Da an ba mu tallafin kamar yadda aka ba sauran da mun ji dadi.”
Jarumi Abdullahi wanda ake yi wa lakabi da Autan Anti cewa ya yi “Ba mu ji dadin abin da gwamnatin tarayya ta yi mana ba, don muna da kamfanin shirya fim mai suna Aya Production, inda muke shirya fina-finai da wakoki, kuma finafinanmu har a gidan talabijin na DSTb ake haska su. Ya kamata a rika tunawa da mu.”
Gwamnatin tarayya ta ba ’yan fim na Kannywood Naira miliyan 40 don su bunkasa sana’arsu. Daga cikin wadanda suka samu tallafin har da Sadiya Gyale wacce kamfaninta mai suna Gyale fim Production ya samu tallafin. Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta bullo da tsarin bayar da tallafin ne don ta taimaka wa wadanda suke harkar shirya fina-finai.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa