Tallafin Man Fetur: NLC za ta tsunduma yajin aiki ranar Laraba

NLC za ta shiga yajin aikin ne don nuna rashin gamsuwarta game da cire tallafin man fetur.

Tallafin Man Fetur: NLC za ta tsunduma yajin aiki ranar Laraba

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) za ta fara yajin aikin gama gari daga ranar Laraba mai zuwa.

Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan bayan wani zaman gaggawa da kwamitin zartarwa na kungiyar ya gudanar kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar farashin man fetur a fadin kasar nan, tun bayan ayyana cewa tallafin man fetur ya zama tarihi a jawabin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi bayan shan rantsuwar kama aiki a ranar Litinin.

Tun bayan batun cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi, aka shiga samun dogayen layuka a gidajen mai.

Bayanai sun ce gidajen mai sun daga farashin litar man fetur, inda a wasu jihohin ake sayar da lman fetur din a kan Naira 550 zuwa 570 duk lita.

A kasuwar bayan fage da aka fi sani da ’yan bunburutu kuwa, tuni man ya kai Naira 700 kan kowace lita.

Lamarin dai ya sanya kudin sufuri da na kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi.

Tuni talakawa suka fara kokawa kan lamarin, inda suka ce hakan na iya jefa miliyoyin mutane cikin tsaka mai wuya.

A ranar Laraba ne dai, Kungiyar Kwadago ta gana da wakilan Gwamnatin Tarayya don tattauna batun shirin cire tallafin man fetur din.

Sai dai zaman bai haifar da da mai Ido ba, inda aka tashi baram-baram ba ta cire da cimma matsaya a tsakanin bangarorin biyu ba.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya