Tallafin N5,000 ga matasan da ba su da aikin yi

An tayar da jijiyar wuya a majalisar dattijai cikin makon da ya wuce, lokacin da aka bijiro da bukatar ganin Jam’iyyar APC ta cika alkawarin yakin neman zabenta na bai wa matasan da ba su da aikin yi a kasar nan tallafin Naira 5,000 a kowane wata, inda kudurin ya ci kasa a hannun ’yan […]

Tallafin N5,000 ga matasan da ba su da aikin yi
Tallafin N5,000 ga matasan da ba su da aikin yi

An tayar da jijiyar wuya a majalisar dattijai cikin makon da ya wuce, lokacin da aka bijiro da bukatar ganin Jam’iyyar APC ta cika alkawarin yakin neman zabenta na bai wa matasan da ba su da aikin yi a kasar nan tallafin Naira 5,000 a kowane wata, inda kudurin ya ci kasa a hannun ’yan jam’iyyar APC, al’amarin da ke da matukar daure kai. dan majalisa Bassey Albert Akpan (wakilin Akwa Ibom a PDP) ya gabatar da kuduri mai taken “Bukatar gaggawa wajen shawo kan rashin aikin yi a Najeriya.” dan majalisa Philip Aduda (wakilin Birnin Tarayya, a PDP), sai ya gabatar da bukatar yi wa kudurin kwaskwarima, inda ya roki Gwmanatin Tarayya ta fara biyan Naira dubu biyar a kowane wata ga matasan da ba su da aikin yi, tamkar yadda ta yi alkawari lokacin yakin neman zabe.
’Yan majalisar daga APC sun dauka gyaran da Aduda ya bijiro da shi na da wata mummunar manufa, don haka Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bukaci a kada kuri’a kan kudurin, inda sanatocin jam’iyyar APC suka ki amince da shirin,. Yayinda ’yan PDP suka kada kuri’ar amincewarsu. Don haka wannan kuduri ya sha kasa. Kuma ba da dadewa ba, sai sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, minister ayanzu, Lai Mohammed ya ce jam’iyyarsa za ta cika alkawarinta na yakin neman zabe, inda za ta biya ’yan Najeriya mutum miliyan 25 da ke fama da matsala Naira 5000 kowane wata. Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da mummunan nufin ’yan PDP wajen kawo rudani game da shirin.”Lai y ace, “za a fito da managarcin tsari, wanda bama kan biyan kudin zai tsaya ba, har ma da cika sauran alkawuran yakin neman zabe.”
A cewar Lai Mohammed, rashin aiwatar da wannan tsari ya auku ne saboda ba yi masa tanadi a cikin kasafin kudin shekarar 2015, wanda Gwamnatin Jonathan ce ta tsara shi. Idan kuwa haka ne, to muna sa ran ganin tabbatarsa a kasafin kudin Gwamnatin Tarayya na shekarar 2016, wanda kwananan nan za a gabatar da shi ga Majalisar kasa, ta yadda za a fara aiwatarwa a shekara mai zuwa, amma akwai tababar yiwuwar shirin.
A gaskiya, Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana a jawabin taron biki karo na 10 a Jami’ar Crewscent da ke Abeokuta, ba da dadewa ba, cewa, Gwamnatin Buhari na shirye-shiryen cika alkawarin yakwin neman zabenta na biytan Naira dubu biyar ga ’yan Najeriya matalauta a daukacin fadin kasar nan. Ya ce gwamnati na tsara dabaru mafui dacewa wajen kawar da tsarin aikewa da kudi da kyautatajin dadin jama’a da ake amfani da shi, don tabbatar da daidaito da gyare-gyare. Osinbajo ya ce: “Idan har aka kammala wannan, za mu aiwatar da kashin farko na shirin, ta hanyar samar da alamar gane mutanen, tare da biyan kudi yadda ya dace.”
A sauran barayin, mun samu tabbaci daga mataimakin shugaban kasa da mai Magana da yawun jam’iyyar APC, cewa jam’iyyar ta jajirce wajen cika alkawarin da ta yi wa ’yan Najeriya masu fama da talauci da matasa marasa aikin yi a lokacin yakin neman zabe. Irin wadannan alkawura sun samar da dimbin kuri’u, ammam alkawarin na buktar kyakkyawan nazari kafin a aiwatar da shi. Duk da cewa muna bayar da cikakken goyon bayan matakan yaki da talauci a Najeriya, muna tunatar da shugabannin jam’iyyar PACe tsohuwar Karin maganar nan, cewa, ‘A koyar da mutum kamun kifi ya fi a ba shi kifin.’
Biyan tallafi a kowane wata ga ’yan Najeriya masu fama da talauci, na iya haifar da mummunar illa tamkar yadda tallafin man fetur ya zama. Mutum na iya fahimtar cewa yawan ’yan Najeriya mutum miliyan 25 da ke fama da talauci ya yi kadan. Domin kididdigar da aka samar a hukumarnce, shi ne akwai akalla kashi 60 cikin 100 na mutanen kasar nan da ke rayuwa a kan kasa da Dala kowace rana. Irin wannan biyan kudin tallafi hakika gwamnatin Obasanjo ta taba gwadawa a farkon wa’adin mulkinta. Abin da kawai ya auku shi ne, shugabannin jam’iyyar PDP sun rubuto jerin sunayen”mnatasa” wadanda a wasu lokutan sun hada da ’ya’yansu da matansu cikin wadanda za su karbi tallafin.
Najeriya ba ta da karancin hukumomi da tsare-tsaren shawo kan fatara da talauci. Hukumomin da suka hada da Hukumar samar da Aikin yi ta kasa (NDE) da Shiribn Kawar da Talauci (NAPEP) da Hukumar Bunkasa kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEDAN) da sauran shirye-sgirye na wucin gadi da aka yi tsawon shekaru ba su cika yin tasiri ba wajen kawar da talauci a fadin kasa. Tsari mara inganci da rashin kulawa da sakaci wajen bibiyar ayyuka, tare da cin hanci da rashawa su suka tattaru suka haifar da matsalar. Idan har tsarin Gwamnatin Buhari na yaki da fatara na son kauce wa yadda aka kwata a baya, dole ya yi maganin dimbin matsalolin da ke dabaibaye da shirin a baya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno