Tallafin N8,000 zai biya bukatun iyalai da dama — Gwamnan Nasarawa
Akwai wadanda suke ganin N8,000 ba wasu kudade ba ne da suka taka kara suka karya.
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce tallafin N8,000 da Gwamnatin Tarayya ke kokarin rabawa domin rage radadin janye tallafin man fetur zai biya wa iyalai da dama bukatunsu.
Da yake zantawa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, Gwamna Sule ya ce Naira dubu takwas kudi masu yawan gaske ga iyalai da dama da ba sa iya samun wannan adadi a wata guda.
- Matata ce ta sa ni bidiyon barkwanci – Bello Galadanci
- Ma’aikatan ƙananan hukumomi na neman ƙarin kashi 300 na albashi saboda janye tallafin fetur
Ya yi tsokaci kan yadda gwamnatin da ta shude ta rika rabawa iyalai tallafin N5,000, lamarin da ya ce yunkurin da gwamnatin yanzu ke yi na raba N8,000 abun ma a yaba ne.
“Na yarda cewa akwai wadanda suke ganin N8,000 ba wasu kudade ba ne da suka taka kara suka karya, amma duk da haka a wurin wasu iyalan da ke cikin talauci kudin zai yi musu rana nesa ba kusa ba.”
Aminiya ta ruwaito cewa a bayan nan ne dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sake nazari kan shirinsa na raba N8,000 ga matalauta domin rage radadin janye tallafin man fetur.
Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Dele Alake ya ce Tinubu ya sauya shawara kan shirin ne sanadiyyar sukan da yake sha daga ’yan Najeriya.
Lamarin na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawa ta sahale wa Gwamnatin Tarayya raba N8,000 ga matalauta miliyan 12 tsawon watanni shida domin rage radadin janye tallafin man fetur.
Majalisar Tattalin Arzikin ta shimfida sabbin matakai
Majalisar Kula da Tattalin Arziki ta Najeriya (NEC) ta sanar da wasu sabbin matakai da gwamnati za ta dauka don samar wa ‘yan kasar saukin rayuwa sanadin wahalhalun janye tallafin man fetur.
Majalisar ta sanar da matakan ne a karshen taron wata-wata da ta yi a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
Taron na tsawon kimanin sa’a shida ya fi mayar da hankali a kan batutuwa guda biyu da suka fi tasiri wajen jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin hali — janye tallafin mai da kuma karyewar darajar naira.
Bayan tafka muhawara da musayar yawu, taron ya amince da daukar wasu matakai na gaggawa domin tsamo ‘yan Najeriya musamman mafi ya rauni daga cikin halin da suka shiga.
Daga ciki akwai bukatar kowacce jihar ta tsara yadda za ta samar wa jama’arta sauki ko dai ta hanyar raba tallafin kudi ko kuma ta hanyar da ta fi dacewa.
Haka ma an amince da bai wa ma’aikatan gwamnati tallafin kudi a kan albashinsu, tsawon wata shida, sannan kowacce jiha ta tabbatar ta biya ma’aikata da ‘yan fansho dukkan basukan da suke bi.
Wadannan in ji majalisar za a aiwatar da su ne ta hanyar amfani da rarar kudin da gwamnati za ta samu saboda janye tallafin man fetur da kuma daidaita harkar canjin kudi.
Bugu da kari, taron ya amince da aiwatar da wani tsari na sauya makamashin da ababen hawa suka fi amfani da su daga man fetur wanda ya yi tsada yanzu zuwa wani nau’in iskar gas da ake kira CNG a takaice wanda Najeriya ke da shi mai tarin yawa kuma ga arha.
Jihohin kasar sun amince za su fara juya motocin jigilar ma’aikata zuwa masu amfani da iskar gas.