Tallafin Naira dubu biyar ga marasa aikin yi
Mai girma Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, zan yi farin ciki mai yawa in har ya samu damar karantawa da yin nazari kan sabon da na rubuta masa cikin bauna da sosayya, tare da fatan samun nasarar gwamnatinsa.Abin da nake son jan hankalin Shugaban basa a kai shi ne; kan shirinsa mai farin jini ga matasa […]
Mai girma Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, zan yi farin ciki mai yawa in har ya samu damar karantawa da yin nazari kan sabon da na rubuta masa cikin bauna da sosayya, tare da fatan samun nasarar gwamnatinsa.
Abin da nake son jan hankalin Shugaban basa a kai shi ne; kan shirinsa mai farin jini ga matasa na ba da tallafin Naira 5,000 ga matasa marasa aikin yi miliyan 25, a kowane wata da nufin rage musu radadin talauci, kuma ya ba da kariya ga shiga ayyukan da suka saba wa doka da barna da rashin kishin basa.
In an duba amfanin wannan shiri ta fuskar siyasa, ya kuma kamata a duba wani sashi da wannan shirin ke da nabasu, daga ciki akwai maimakon magance matsalolin da suka sa aka birbiro shirin, wannan tallfin bai isa ya biya kadan daga cikin manyan bubatun matasa ba. domin Naira 5,000 kacal ba za ta iya hana matasa shiga ayyukan barna ba, abubuwan da hasali ma shirin zai bude wa wasu marasa kishin basa bofar cin dukiyar jama’a ta haramtacciyar hanya, wannan baya ga biliyoyin Naira ko ma in ce triliyoyin Naira da za a kashe kan shirin, ga shi kuma basa na fama da matsin tattalin arziki da manyan bubatu na rashin kyawawan hanyoyin mota, da lalatattun ajujuwan a makarantunmu na firamare da sakandare; ga fama da ake da barancin magunguna da bwararrun likitoci a asibitocin gwamnati, ga matsalolin fashi da makami, ga kuma uwa-uba, rikicin Boko Haram da na ’yan tada bayar baya a Neja-Dalta da na masu fafutukar kafa basar Biyafara da sauransu.
Bayan tarin wadannan matsaloli da ake fama da su, yawan kudin da shirin zai lashe abin tamabaya ne, domin ma’aikatan gwamanati ma da byar suke samun albashinsu, baya ga basusukan masu fensho, ga shi har wasu gwamnoni na ibrarin ba za su iya ci gaba da biyan albashi mafi baranci na Naira18,000 bisa dalilai na barancin kudin shiga.
Abin yi kan wannan al’amari duk da cewa Jam’iyyar APC ta dauki albawari kansa, maimakon haka, kamata ya yi gwamnatin Mai girma Muhammadu Buhari ta yi amfani da kudin jama’a kan al’muran da za su magance manyan matsalolin wannan basa mai albarka. Wato kamata ya yi a yi wani fasali wanda zai samar da tabbataccen tsaro a kowane sashi na Najeriya, a kuma yi wani tanadi na cikin gida wanda zai bunbasa tattalin arziki, ya kuma samar wa miliyoyin matasa aikin yi, musamman in aka yi dabarar bunbasa sana’o’in hannu na gargajiya da na zamani, a kuma bunbasa harkokin noma da kiwo da sun kifi da harkokin da suka danganci bunbasa gandun daji, domin amfani da albarkatun da Allah Ya halitta.
Manufa a nan ita ce; a yi nazari ta yadda za a fito da wasu ayyukan raya basa na gyaran manya da banana hanyoyin mota, a gina barin makarantu da ajujuwa, a gyara wadanda suka lalace, a kuma bullo da ayyukan da za su bunbasa tattalin arzikin basa da jama’arta.
Magana ta gsakiya,wannan shiri yana da nauyi matuba bisa la’akari da mabudan kudin da zai labume, har sama da Naira billayan 125, a kowane wata, wannan baya ga biyan wadanda za su dauki dawainiyar kula da shirin, wannan kudi ya wuce kason da daukacin bananan hukumomin Najeriya 774 ke samu a wata-wata daga Asusun Tarayya, domin a watan Mayu, 2015, Naira billiyan 59.998 suka samu yayin da a watan Yuli 2015 suka samu Naira biliayan 86.610, kamar yadda a watan Oktoba, 2015 suka samu Naira 59.181.
Wani abin lura, shi ne, da wuya wannan Naira 5000 ta biya bubata, hasali ma a fahimtata biyansa zai zama wani babban balubale, ta fuskar haifar da wasu matsaloli da za a kasa shawo kansu cikin saubi, sakamakon wasu abubuwa da za su biyo baya kan kasa ci gaba da biyan ko na samun jinkiri, wannan baya ga halin rashin yarda da bambancin wurin zama, bambancin babilanci da addini, wadanda tilas ne su yi tasiri kan rabon, ga shi kuma basa na fama da matsin tattalin arziki ga manyan bubatu da tarin matsaloli da suke bubatar samun kulawar gwamnati.
Ni a fahimtata, shirin ba da tallafin kudi ga marasa aikin yi tamkar karin maganar nan ne, da Hausawa kan ce “A dauri kashi ko a bata igiya,” ko daukar karan mahaukaciya, bayan da tara ta kasa dauka sai ta sun ce igiyar, ta shiga baro wani karan, a barshe dai a nan za ta bar igiyar da duk abin da ta tara. Bayan wahala babu wata fa’ida sai bata lokaci da asarar dukiya.
Allah Ya taimaki Najeriya da jama’arta da shugabaninta gaba daya.
Yalwa Babangida Muhammad, ya rubuto mabalarsa daga Hadeja Jihar Jigawa [email protected].
Ina canjin da muke nema a Najeriya?
Amsa daya ita ce; daya mafarin birga, ma’ana neman canjin shugabancin da muka yi tamkar, sharar fage ce wajen kawo wa basarmu canji. Bisa la’akari da cewa, daga liman ne Sallah kan baci, domin in liman sallarsa ta gyaru, to sauran mabiya tasu ma za ta yi kyau, amma in sun yi bobarin bibiyar babli da ba’adin sallar.
Don haka ya za ma dolen-dole mu al’ummar Najeriya mu canja, a bangarenmu tun daga canja halayenmu da ba su dace ba zuwa ga rungumar kyawawan halaye. In har da gaske ne har a cikin zukatanmu canjin muke nema. Domin ba ranar da basar mu za ta taba zama a kan turba tagari, zaman lafiya da wadatar arziki ya tabbata gare mu, muddin ba mu kawar da munanan halayenmu ba.
La’akari da halin bunci da rashin makoma tagari da yanzu haka muke kai, duk da canjin shugabancin da muka samu, kullum muna cikin kukan rashi ya yi mana katutu. Kuma duk wannan ya faru ne sanadiyar rashin gaskiya da ribon amana da rashin bin shimfidaddun dokokin Allah Ta’ala.
Idan muka yi dubi da abubuwan suke faruwa yanzu haka, inda kullum burinmu shi ne mu ga ’yan uwanmu na cikin wani mawuyacin hali, mu bara jefa su, cikin mawuyacin halin. Misali yanzu haka barancin man fetur da muke ta fama da shi a kowane lungu da sabo na basarmu, duk da mun san ba gwamnati ta bara kudin man fetur din ba, amma biri-biri wasu ’yan tsirarun mutane sun jefa al’ummar Najeriya cikin mawuyacin hali. Haba ’yan uwana ’yan Najeriya, ta yaya Allah zai jibanmu ba mu jiban kanmu ba?
Ya kamata mu tuna fa cewa Allah Yakan ji kunyar tauye arzikin wanda ya jiban bawanSa. Don haka ke nan muddin muka kyautata halayenmu, ta hanyar tausaya wa na basa da mu, sai Allah Ya yi mana baiwar arziki mai dorewa. Ko ba komai dai Allah Ya arzurta basarmu da arzikin da mu kanmu ba mu san iyakarsa ba.
A barshe nake robon Allah Ya ba mu ikon ribe gaskiya da ribon amana a dukkanin lamurranmu. Ya Allah Ka fitar da basarmu daga cikin wannan halin da take ciki. Allahumma amin.
Abdulmalik Sa’idu Mai Buredi, Tashar Bagu, Gusau (Jami’in Hulda Da Jama’a Na bungiyar Muryar Talaka ta basa Reshen Jihar Zamfara)
08069807496.
[email protected]