Tallafin Naira miliyan 5 ya kawo rabuwar kai a Kasuwar Kurmi

A karshen makon  jiya ne aka samu rabuwar kawuna a tsakanin ’yan Kasuwar Kurmi sakamakon rabon tallafin Naira miliyan biyar da Shugaban Asusun Kula da Manyan Makarantu na Kasa Dokta Abdullahi Baffa Bichi ya bayar ga wadanda bala’in gobara ya shafa a kasuwar a lokuta daban-daban. Lokacin da Dokta Baffa Bichi ya je kasuwar ya damka […]

Tallafin Naira miliyan 5 ya kawo rabuwar kai a Kasuwar Kurmi
Tallafin Naira miliyan 5 ya kawo rabuwar kai a Kasuwar Kurmi

A karshen makon  jiya ne aka samu rabuwar kawuna a tsakanin ’yan Kasuwar Kurmi sakamakon rabon tallafin Naira miliyan biyar da Shugaban Asusun Kula da Manyan Makarantu na Kasa Dokta Abdullahi Baffa Bichi ya bayar ga wadanda bala’in gobara ya shafa a kasuwar a lokuta daban-daban.

Lokacin da Dokta Baffa Bichi ya je kasuwar ya damka kudin ne a hannun Shugaban Kasuwar wanda ake zargin bai ba wadanda bala’in gobarar ya shafa ba sai ’yan uwansu, inda ake zargin sun raba kudin ne a tsakanin ’yan uwansu.Abdullahi S. ’Yandoya yana daga cikin shugabannin kungiyar ’yan kasuwar kuma ya bayyana cewa tun daga lokacin da aka karbi kudin ba su sake jin duriyarsu  ba. Ya ce shugaban kasuwar ya dauki wadansu ’ya’yan kungiyar wadanda ba shugabanni ba suka tafi suka raba kudin a tsakanin junansu da kuma ’yan uwansu ba bisa ka’ida ba.

’Yan Doya ya kara da cewa saboda haka ne wadansu daga cikin shugabannin kasuwar suka dauki matakin dakatar da shugaban nasu don samun damar gudanar da bincike a kan yadda aka yi rabon kudin. “Sakamakon ba mu gamsu da yadda aka yi rabon kudin ba don haka a matsayinmu na wadanda ke rike da mukamai a shugabancin kasuwar muka dakatar da shugaban namu har zuwa lokacin da kwamitin da aka kafa zai kamala bincikensa,” inji shi.

Sai dai da yake mayar da martani Shugaban Kasuwar Kurmi, Alhaji Ya’u Karas ya ce bi-ta-da-kulli ce kawai ake yi masa domin ya raba kudin ne yadda ya dace.

Ya’u Karas ya nuna mamakinsa game da yadda ’yan uwansa shugabannin kungiyar suka yi masa wannan zargi kasancewar sun san halinsa ba mutum ne da kudi ya rufe wa ido ba. “Abin da ya ba ni mamaki shugabannin nan sun san halina ba na shiga duk cikin abin da ba na gaskiya ba. Kuma na yi wa Allah godiya kasancewar ban dauki ko kwabo a cikin kudin nan don kaina ba,” inji shi.