Tallafin rigakafi: Gwamnatin Yobe ta yaba wa Gidauniyar Bill Gate da ta dangote

Gwamnatin Jihar Yobe ta yaba wa Gidauniyar Bill and Bilinda Gate da ta dangote dangane da hobbasar da suke yi wajen kawo karshen yaduwar cututtukan da ke addabar yara a jihar. Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam wanda Mataimakinsa Injiniya Abubakar Ali ya wakilta ne ya bayyana haka a lokacin da manyan jami’an cibiyoyin suka kai […]

Tallafin rigakafi: Gwamnatin Yobe ta yaba wa Gidauniyar Bill Gate da ta dangote
Tallafin rigakafi: Gwamnatin Yobe ta yaba wa Gidauniyar Bill Gate da ta dangote

Gwamnatin Jihar Yobe ta yaba wa Gidauniyar Bill and Bilinda Gate da ta dangote dangane da hobbasar da suke yi wajen kawo karshen yaduwar cututtukan da ke addabar yara a jihar.

Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam wanda Mataimakinsa Injiniya Abubakar Ali ya wakilta ne ya bayyana haka a lokacin da manyan jami’an cibiyoyin suka kai masa ziyara a gidan gwamnati da ke Damaturu.
Gwamna Gaidam ya ce bada tallafin allurar rigakafin da cibiyoyin ke bayarwa a kananan hukumomin jihar 17 abin a yaba ne. Don haka ya bukaci sauran cibiyoyi da kungiyoyin gida da waje da masu hannu da shuni da daidaikun jama’a su shiga a dama da su cikin wannan aiki na ceto yara.
Da suke bayani manyan jami’an cibiyoyin Dokta Ahmed Iya na Gidauniyar dangote da Mista Misheal Galibe na Gidauniyar Bill and Milinda Gate sun jinjina wa gwamnatin Yobe ne kan yadda take sarrafa tallafin da suke bayarwa. Sun bada tabbacin ci gaba da bada tallafin rigakafin don ganin an samu matasa masu kuzari da za su jagoranci al’umma a nan gaba.