Tallar haja da sako a jaridar Hausa
Tallata haja ko isar da sakonni a jaridar Hausa, na da matukar muhimmanci, musamman a wannan kasa ta mu da Hausa ta zama daya daga cikin manyan harsuna da ake amfani da su a wajen mu’amalar zamantakewa da ta kasuwanci da harkokin mulki. Don haka kamfanoni da hukumomi da daidaikun mutane za su iya bayar […]
Tallata haja ko isar da sakonni a jaridar Hausa, na da matukar muhimmanci, musamman a wannan kasa ta mu da Hausa ta zama daya daga cikin manyan harsuna da ake amfani da su a wajen mu’amalar zamantakewa da ta kasuwanci da harkokin mulki. Don haka kamfanoni da hukumomi da daidaikun mutane za su iya bayar da tallace-tallace na kayan sayarwa ko fadakarwa game da wani sabon shiri da aka bullo da shi don kyautata rayuwar al’umma.
Jarida na wayar da kan al’umma a kan abubuwan da ke faruwa a ciki da da wajen kasar nan, musamman dimbin al’amuran da suka jibinci rayuwar mu. Domin haka, manufar jarida, ita ce, ilmartarwa da nishadantarwa da sanarwa da sauransu. Lallai Jarida tana nuna mana yadda za mu kyautata rayuwarmu ta zamantakewa.
Idan ka yi niyar sanya talla ko sako, to lallai ne, ka samu ingartacciyar jarida wacce ta yi fice da zama gagarabadau cikin sa’o’inta. Kuma ta zama ta fi karbuwa wurin mutane makaranta. Ita kuwa jarida ta yi fice yana tattare da kwararrun ma’aikatansu da suka gogu a fannonin ilimin Jarida da ko karin shigar da ita kowane lungu. Saboda haka ka sanya kudinka ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu. An ce sayan nagari maida kudi gida. Domin riba kake nema. Kana son mutane su san da zamanka, manufarka da irin hajar da kake nufin tallatawa. Yekuwa cikin jarida za ta zaburar da mutane wajen bukatar kayanka. Zai fito fili a idon jama’a.
Fa’idar da ke tattare da yekuwa ko talla cikin jarida, alfanunsa yana da yawa, daga ciki yana kara haskaka sakonka ko hajarka ta janyo hankalin masu bukata zuwa ga sanarwa ko tallatar da aka buga a jarida.
Talla a jarida na kara kwarjini ga abin da aka tallata, hart a kai ga sauya zuciya da tunanin mutum ga son haja ko manufofin hukuma da aka baje su a shafin talla. Ba shakka talla na fadakar da mutane kan sanin bayanai da manufar abin talla ke kunshe cikin sakon. Lallai hakkin mai yin talla ne ya san sahihiyar hanya ko tsani da za ka bi wajen isar da sakon ko tallar hajarsa zuwa ga jama’a domin jawo hankalinsu. Samun nasara yin talla cikin Jarida su ne, sakon talla da kake son yekuwa ka tabbatar zai yi tasiri da karbuwa ne kadai, in an yi ta hanyar da ta dace zuwa mahangar ka. Hanyar da ta dace kuwa, ita ce, ka nemi kwakkwarar jarida wacce ta fi karbuwa sosai cikin mutane.
Sahihiyar hanya ko tsani kuwa, ita ce, ka yi tallarka cikin fitacciyar jarida a cikin al’umma. Amma fa sai ka tsara sakonka cikin hikima da basira, wanda kai da kanka ko ka ba kwararru su tsara maka sakon tallan. Alal hakika ke kwawar tsari lallai yana iya zaburar da mutum ya kwadaita da hajjarka da ka baje masa cikin sakon a lokacin. Kuma ka kwana da sanin cewa, talla na iya zama sanadin masu bukatrar kayanhka su karu ko da nan gaba.
Ga kadan daga cikin ma’auni ko sikeli da za ka duba wajen zabar Jaridar da za ka sanya tallarka. Ga abubuwan lura kamar haka: Ka tabbatar jarida ce wacce ta samu gagarumar karbuwa cikin dimbin jama’a, ka tabbatar kowane lungu-lungu da sako-sako na ko’ina ana ganinta , kuma jaridar da ta jibinci manufofin da wanda mutane ke da ra’ayinta da kuma ta fi karbuwa.
Dalilan yin talla cikin jarida su ne domin sanar da mutane kan bukatunka.Wannan zai ba ka damar sanin masu bukatar kayanka ko sana’arka, Hakazalika suma masu sayen kayanka za susanka. Kuma talla yana sanar da mutane wurin da za a sameka da kayanka, farashinsu, amfaninsu, yadda ake amfani da sauransu. Akwai bukatar yin bayani sakonin da suke cikin jarida tamkar zanen dutse ne, kuma za ta daga sama domin al’umma su ganka
Ga wasu daga cikin fa’idodin Jaridar kamar haka. Za ka iya isar da sako, za ka iya ajiyewa domin tarihi, Karanta ta za ta kara inganta karatunka da sannin wasu kalmomi da fasaha. Kuma tana iya zama shaida da sauran dimbin alfanu. Domin ita jarida na iya kaiwa inda ba a zata ba.
Akwai bukatar kasan wane ne kake son ka isar wa sakon ka ko tallarka. Kasan yadda yake rayuwarsa da halayensa da al’adunsa. Domin sanin wannan zai ba ka dama da fahimtar ta yadda za ka shirya sako da zai janyo hankalinsa zuwa ga bukatarka. Sanin mutumin zai ba ka dama sanin yadda za ka jawo hankalinsa domin ya so da kuma cusa masa sha’awar da zai iya ingiza shi sayen kayanka ko amincewa da sakonka.
Idan kana bukatar yin talla cikin jarida sai ka tanadi sako, sa’annan ka tsara da shirya yadda kake son sa. Kuma ka tanadi hotuna da sauran su idan akwai bukata. Sannan sai ka za bi wacce jarida za ka yi talla. Sannan sai ka tanadi kudinka wanda zai daidai da fadin filin da kake son saya a cikin jaridar. Duk mai neman bayani zai iyaa duba jadawalin farashin kowace jarida.
Wani abu da masu bayar da talla a jarida suka manta, shi ne, duk da cewa, tallace-tallacensu hanyar samun kudin shiga ce, amma idan kwalliya ta biya kudin sabulu, sai su zama masu samun gwaggwabar riba. Sanin kowa ne dai Bahaushe ya ce, “mai talla shi ke da riba.”
Umar Muhammad Idris Ma’aikaci ne a kamfanin buga jarida na Dailytrust.