Tallar Jonathan ta fusata Babangida
Tallar da gidajen talabijin suke yi ta yayata Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta fusata tsohon Shugaban Mulkin Soja Janar Ibrahim Babangida, bayan da tallar ta rika bata shugabannin mulkin soja tare da nuna ba su da kwarewa. Janar Babangida ya bayar da misali da shiri na musamman da wani gidan talabijin mai zaman kansa ya […]
Tallar da gidajen talabijin suke yi ta yayata Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta fusata tsohon Shugaban Mulkin Soja Janar Ibrahim Babangida, bayan da tallar ta rika bata shugabannin mulkin soja tare da nuna ba su da kwarewa.
Janar Babangida ya bayar da misali da shiri na musamman da wani gidan talabijin mai zaman kansa ya watsa wanda ya ce, “Da gangan aka ci mutuncin Janar Olusegun Obasanjo da Janar Muhammadu Buhari da ni kaina Janar Ibrahim Babangida da marigayi Janar Sani Abacha da Janar Abdulsalami Abubakar da kuma Janar T.Y danjuma.”
Janar Babangida wanda ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba a wata takarda da ya fitar ya kara da cewa: “Ina da matukar ja da abin da ke cikin shirin da kuma inda shirin ya dosa. Baya ga yayata kamfe din batanci da kiyayya wanda a fili yake kushe gudunmawar da tsofaffin shugabannin kasar suka bayar, sharhin da aka rika gabatarwa a shirin na bata tsofaffin shugabannin ya kufular da ni.”
Janar Babangida ya ce babu wanda zai hana wani gudanar da kamfe na tallata dan takararsa, amma bai dace a kushe gudunmawa da kishin kasa da sadaukarwar da tsofaffin shugabannin suka bayar ba, balle har a kira su da marasa kwarewa.
Janar Babangida ya tunatar da masu kamfe wa Jonathan cewa “Su tuna ba wai alfahari ba, tunanin kafa Jam’iyyar PDP wadda ta zama ‘jam’iyya mafi girma a Afirka’ ya fara ne a gidana da ke nan Minna. Tare da goyon bayan abokai muka tsara wannan tafiya ta dimokuradiyya wadda ta kai mu ga halin da muke ciki a yau. Mun aza harsashin gina dimokuradiyya tare da tsara ta. Wadanda suke nuna su ne ’yan dimokuradiyya a yau, duk an dama da su a gwamnatocin mulkin soja. Kuma da sanina na ja gefe na ki busa algaitata na zabi yin shiru kan batutuwa da dama da suka shafi Najeriya, inda nake bayar da shawarar da ta kamata ga duk shugaban da ya hau mulki,” kamar yadda sanarwar ofishinsa na hulda da manema labarai ya fitar.
Tsohon Shugaban kasar ya ce, shigar janar-janar masu ritaya cikin harkar siyasa ba laifi ba ne, domin dimokuradiyya ta kowa da kowa ce. “Don haka abin takaici ne yadda masu tallata Shugaba Gooodluck Jonathan suke kokarin batunci da cin zarafin tsofaffin shugabannin soja domin bata mutunci. Wannan rashin adalci ne,” inji sanarwar.