Tamabayoyin Duniyar Ma’aurata 3

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha Allah za mu ci gaba da amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko masu nasaba da bayanan da suka gabata kan hanyoyin farfado da soyayya tsakanin ma’aurata. Tambaya 3 Matata […]

Tamabayoyin Duniyar Ma’aurata 3
Tamabayoyin Duniyar Ma’aurata 3

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha Allah za mu ci gaba da amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko masu nasaba da bayanan da suka gabata kan hanyoyin farfado da soyayya tsakanin ma’aurata.

Tambaya 3

Matata na samu ta saka min layu guda biyu a cikin filon da nake matashi da shi. Wane mataki ya dace na dauka kanta domin ina cikin fargaba na kasa natsuwa da ita.

Amsa: Gaskiya wannan kam babban abin fargaba ne, Allah Ya sawwake, amin. To ga abubuwan da Ya kamata ka yi daya bayan daya:

  1. Rufin asiri: Mafi muhimmanci shi ne ka bar wannan abin tsakaninka da Allah, kada ka fada wa kowa; ka rufa mata asiri saboda Allah da dangantakar da ke tsakaninku; in ka tona mata asiri kamar ka tona wa kanka ne a matsayinta na matarka. In ka rufa mata asiri Allah zai ba ka lada kuma kai ma zai rufa maka asiri.
  2. Kada ka yi saurin yanke hukunci ko daukar mataki a kanta: Don gudun kada ka zartar da abin da daga baya za ka yi da- na-sani ko abin da zai haifar da barna mai yawa sama da gyara; ka ba kanka lokaci ka yi nazarin abin cikin kwanciyar hankali don samun mafita mafi alfanu.
  3. Natsuwa: Ka yi kokarin ganin ka natsar da zuciyarka da ma’aikatar hankalinka game da wannan al’amari ta hanyar yawan zikiri da karatun Kur’ani, in ma da hali ka hada har azumin nafila har sai ka ji natsuwa da aminci sun wadatu a zuciyarka.
  4. Ka sani kowanne dan Adam tara yake bai cika goma ba: Kowa da irin nakasunsa; don haka ka yi kokarin yi mata izina ta hanyar duba wasu kyawawan halayenta da ka sani, wannan zai taimaka maka wajen yin zabi mafi alfanu duk lokacin da ka tashi yanke hukunci.
  5. Bayan ka tabbatar ka samu natsuwa a zuciyarka sai ka zaunar da ita ka yi mata tambayoyi game da al’marin kuma ka bukaci lallai ta gaya maka gaskiya gaba dayanta har in tana son a samu daidaituwa a tsakaninku.
  6. In ta fada maka gaskiya kuma to nemi gafara: To alhmadulillahi sai ka yafe kuma ka yi amfani da bayanin da ta yi maka don toshe wannan muguwar kafa a rayuwar aurenku. Misali in wani ne ya koya mata kamar kawa ko ’yan uwa da sauransu, to sai a raba ta hulda da su gaba daya don babu alheri a cikin irin wannan tarayya. In kuma rashin ilimi ne sai a yi kokarin karantar da ita illar irin wannan aiki da kuma girmansa da yadda zai salwantar da rayuwarta duniya da Lahira. In kuma tana da ilimi karancin imani ne, sai a taimaka mata da hanyoyin sabunta imani; ta fara da yin kyakykyawar tuba ga Mahaliccinta Allah Madaukakin Sarki don Shi ta saba wa sama da komai da kowa, sannan ta yi niyya da kudurin ko da wasa ba za ta kara aikata irin wannan mummunan aiki ba. Sannan ta dage da karin ayyukan karuwar imani kamar tsare Sallah cikin lokacinta, yawan zikiri da karatun Kur’ani da yawan sadaka da yawan istigifari da tsayuwar dare da azumin nafila da sauransu.
  7. 7. In kuma ta ki fadar gaskiya, ko ta tsaya kame-kame, ko ta nuna isa da girman kai to sai ka bi hanyoyin ladabtarwa kamar yadda ya zo a aya ta 34 cikin Suratun Nisa’i: wato ka fara da wa’azi da nasiha da fadakarwa; in ta ki biyayyar ta fada maka gaskiya abin da ya kai ta aikata wannan mummunan aiki sai ka kaurace mata a wajen kwanciya, in ta ki sai ka buge ta dan kadan, bugu ba tare da ka cutar da ita ba. In duk wannan ya ki sai ka kai abin gaban magabata don a yi muku shari’a.
  8. Lallai amfani da layu da ma duk sauran kayan tsibbace-tsibbace da sihiri shirka ce mai girma mai tabbatar da asara duniya da Lahira; don haka lallai ka dage ka ga ka toshe wannan kafa toshewar dindindin yadda ba za ta sake bullowa cikin rayuwar aurenku ba. Kuma kai kanka ka dage ka ga cewa ka kara dulmiya cikin rikon addini domin wannan zai yi tasiri ga iyalinku su zama nagari; sannan zai zama ganuwa gare ka daga duk wani tsibbu da sihiri da za a yi da sunanka ba zai yi tasiri ba balle har ya cutar da rayuwarka ko ya juya maka hankali ka zama kamar rakumi da akala. Allah Ya taimaka Ya fitar da ku daga wannan jarrabawa da alheri da ci gaba a rayuwa da karuwar imani, amin.