Tamabayoyin Duniyar Ma’aurata 4

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha Allah za mu ci gaba da amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko masu nasaba da bayanan da suka gabata kan hanyoyin farfado da soyayya tsakanin ma’aurata. Tambaya ta 4: […]

Tamabayoyin Duniyar Ma’aurata 4

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha Allah za mu ci gaba da amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko masu nasaba da bayanan da suka gabata kan hanyoyin farfado da soyayya tsakanin ma’aurata.

Tambaya ta 4: Me ya sa wadansu maza da sun yi aure, kwana biyu sai kuma ka fara ganinsu suna faman waya da ’yan mata; laifin matan nasu ne ko kuma halin mazan ne?

-Kwamared Gumel.

Amsa: To sai dai ya zama halin mazan ne kawai; domin ko namiji mara aure ba kamala ba ce a gare shi ya rika faman waya da ’yan mata; balle kuma mai aure. A shari’ar Musulunci duk wani zumunci da za ka kulla da mace wacce ba muharramarka ba, to haramtaccen zumunci ne; balle kuma yawan waya da ’yan mata suna kashe murya ana jin dadin kalamansu. Wannan kusantar zina ce wadda kuma babban alkaba’iri ne domin Allah Madaukaki Ya yi hanin yin duk wasu abubuwa da za su kusantar da mutum ga zina ta hanyar motsa masa da haramtacciyar sha’awar mace ajnabiyya a gare shi. Da fatan Allah Ya gyara, Ya shiryar da mu hanyar da za ta isar da mu zuwa ga yardarSa, amin.

 

Tambaya 5: Tamabayata ita ce shin kamar yadda aka ce mace in mijinta ya bukace ta ba ta je ba mala’iku za su tsine mata kuma in mijinta na fushi da ita Allah ma Yana fushi da ita; to in ita ce take bukatarsa ya ki, ba wani sakamako da zai shafe shi? In shi ne yake kunzuga mata mugunta ta yi fushi da shi, ba wani abu da zai same shi? Sau da yawa idan na gaji da aikin gida da dawainiyar yara; amma ba na yi masa kyuya in ya bukace ni, amma ni duk lokacin da juyawar wata ta karo mini karsashin bukatar aure in dai har shi bai jin yi to ba zai kula ni ba; ni kuwa ko ban jin yi dole in kula shi saboda fargabar fada wa sabon Allah, don Allah a warware mini zare da abawa. Na gode,

Maman Sumayya.

Amsa: More ibadar aure da samun biyan bukatar sha’awa hakki ne na mata da miji ba wai ga miji kadai ba; hikimar da ke cikin tsaurara gargadi a kan ’ya mace saboda yanayinta na yadda a yawan lokuta takan yi aiki da shauki sama da hankali saboda shauki ya fi nauyi a ma’aikatar hankalinta. Dalili na biyu shi ne sha’awar da namiji babba ce, gawurtacciya ce sama da sha’awar ’ya mace don haka koyaushe cikin nemanta yake kamar yadda yake neman abinci in ya ji yunwa. Sannan in mace na fama da tsananin gajiya, ko rashin lafiya ko kawai ta ji a wannan lokaci kwata-kwata ba ta da sha’awa ko kuzarin yin ibadar aure; tana iya sanar da maigidanta ta hanya mafi dacewa; ba a ce dole a kowane hali take mijinta ya bukace ta dole ta je ba. Abin da ba a so shi ne a rika yi da gangan don cutarwa, ko a rika yi masa yanga; ko kuma kiri-kiri a hana shi gaba daya; ko kuma da maigida ya yi wani dan laifi da bai taka kara ya karya ba sai a kaurace masa. Ko ya taka kara ya karya din bai kamata ba in dai ya bukata; abin nufi dai shi ne ya kasance akwai kwakwarar hujja to babu laifi. Kamar haka shi ma maigida duk ranar da uwargida ta bukace shi, in ba akwai wata sahihiyar hujjja ba kamar rashin lafiya ko tsananin gajiya, to wajibi ne ya ba ta hakkinta kamar yadda ita ma take kokartawa ta ba shi. In kuma ya ki bayarwa to ya zalunce ta kuma hakki na nan a kansa, a Ranar Hisabi sai ya biyata sai dai in ta yafe masa. Haka in shi ne yake kunzuga mata da gangan don cutarwa to nan ma ya zalunce ta kuma zunubin zaluncin na nan sai dai in ita ce ta yafe masa. Lallai hadisai da yawa sun yi kakkausar jan kunne ga mata wajen yin biyayya ga miji; to haka kuma sun nanata umarni a kan bi a hankali ga mata, lallaba su, yi musu kirki, ji da su da yawan kau da kai daga nakasunsu; mafi girma wannan kuma shi ne ayoyin Alkur’ani Mai girma sun maimata cewa maza su huldanci mata a koyaushe da kyautatawa; don haka kin yi aiki da wannan umarni ga maza shi ma yana da nasa sakamakon in har ba su tuba suka gyara ayyukansu ba, da fatan Allah Ya sa mu dace duniya da Lahira, amin.